Kujerar Mataimakin Gwamna A Siyasa Da Tsarin Mulkin Najeriya — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

NAZARI

Kujerar Mataimakin Gwamna A Siyasa Da Tsarin Mulkin Najeriya

Published

on


Wani bincike da na gudanar a kan wannan matsayi na kujerar mataimakin gwamna shi ne matsayi ne wanda sai mai hakurin gaske da kai zuciya nesa ke iya rike ta. Sai kuma wanda ke da wata irin fahimta da dangantaka mai karfin gaske tsakanin mai rike da ita da kuma gwamnan da su ke mulki a tare.

Kujera da matsayi ne wanda tsarin mulkin kasa ya kasa ba ta ko mai ita wani hobbassa sai dai kawai cewa idan gwamna ba ya nan ka rike. Shi ma wannan ba dole ba ne; idan gwamnan ya ga dama ya na iya baiwa wani ba kai ba. Sai kuma duk wani aiki da gwamna ya ba ka.

A tsarin mulki a matsayin ba ka da hus na wani abu da za ka iya aikatawa. Sai abin da gwamnanka ya ba ka. Ba ka da ikon bada umurnin fitar da kudi ko da kuwa ficika ce, indai ba daga cikin aljihunsa zai fitar ba.

Wannan matsaya ya sanya masu rike da wannan matsaya sai ka samu su na fama da jama’ar da su ke karkashinsu a siyasance. Su na tsammanin cewa saboda matsayin da su ke rike da shi na suna daga gwamna sai su. Don haka su na tsammanin duk yadda gwamna ya fantama dole ne su fantama a hakan.

A wani lokaci idan mai wannan matsayi ya ce zai rika kula jama’ar na siyasa sai ka ga ’yan tsurku sun fara kai suka ga gwamna cewa lallai mataimakin nasa ya na yi ma sa wata makarkashiya ko ya na shirya ma sa zagon kasa. Ba ka ankara ba sai ka ga an fara yakin sunkuru da gaba. Idan ba a kai zuciya nesa ba, sai ka ga mataimakin gwamnan ya zama abin tausayi.

Irin wannan sarkakiya wacce mataimakin gwamna kan shiga ta sa a baya a ka yi ta samun masu kira da a soke kujerar. Wanda ya fara wannan kiran a baya shi ne Alhaji Tukur Jikamshi lokacin ya na mataimakin gwamna zamanin Marigayi Umaru Musa Yar’Adua a jihar Katsina. Da a ka shiga tsakaninsu sai da Alhaji Tukur ya zama abin tausayi. Irin wannan sarkakiya da matsala ta sanya a ke samun rigingimu tsakanin gwamnoni da mataimakansu a jihohi daban-daban, kamar misali kwanan nan a Kano tsakanin Ganduje da Farfesa Hafiz, wanda a ka ruwaito mataimakin na yin wasu zantuttuka ga mutanensa har ya na cewa ba za a sake tsayawa takara tare da shi ba.

Ga abinda ya faru kwanan nan a jihar Bauchi, inda mataimakin ya ajiye ya ce ya gode da damar da a ka ba shi da yadda ya taba faruwa lokacin Bafarawa, Gwamna Wammako ya na mataimakinsa a jahar Sokoto.

A karkashin kasa jihohi da yawa na fadan sari-ka-noke tsakanin gwamnansu da mataimakansu kuma da yawa su na cin dunduniyar juna. Wannan ya sanya gwamnoni da yawa ba su son su ga cewa mataimakansu sun gaje su. Wasu na cewa misalai da a ka samu na mataimaka na gadar gwamnoni, in sun hau su kan yi kokarin rama cutarwar da a ka yi masu lokacin su na biyayya. A Sokoto da Wammako ya zama gwamna sai da ya hana Bafarawa sakat a siyasance. Haka da Mamuda ya zama gwamna sai da ya hana Yarima sakat a jihar Zamfara. Ga abin da ke faruwa yanzu a jihar Kano tsakanin Kwankwaso da Ganduje.

Kujerar mataimakin gwamna wani matsayi ne na iya ruwa fitar da kai, idan kuma ba ka yi taka-tsantsan ba, to za ka shiga rububi, don gwamnanka zai kulle ka kuma ba abinda za ka iya yi a tsarin mulki

Sai dai a gan ka da yawan jami’an tsaro da jiniya idan ka na so, wadanda su ma tsarin mulki ne ya ba ka su. Amma a ciki ba komai sai fankam-fayau, domin hakkinka na ofishin iya wanda doka ta ba ka, idan ba ka ba su iya rike ma ka danginka balle siyasarka, kamar yadda binciken da na yi ya tabbatar ma ni.

Wani mataimakin gwamna da ya samu matsala da gwamnansa ya shaida ma ni cewa, da gwamnansa ya rike ma sa komai saboda munafukai sun shiga tsakaninsu, “sai da cefane irin wanda ya kamata a yi a gidana ya nemi ya gagare ni,’’ in ji shi.

Kamar yadda na ce, matsayin iya ruwa ne fitar da kai, idan ka amsa dole ka san matsayin da tsarin mulki wanda ba komai ba ne da ya wuce bin abin da gwamnanka ke so. Daga nan ya zaka zauna da mukarraban gwamna lafiya kamar yadda wani tsohon mataimakin gwamna ya shaida mani .’’ zaka yi ta gani da ji daga wajensu[jami an gwamna]kuma ba ruwansu da kai don haka sai ka kai zuciya nesa’’

Sai kuma ya zaka tafiyar da siyasarka ? wanda yafi wahalar sha ani da kuma tsaka mai wuya.in ka rika biya su da tara su. Da taimaka masu .a ce ma gwamna kana da manufar da ta sanya kake hakan in akai nasarar hada ku fada.na lahira sai fika jin dadi,in kuma ka kyale mutanenka a ce ka watsar dasu anan wani yanayi ne na gaba kura baya siyaki.

Rashin wani takaimemen matsayin da tsarin mulki ya baiwa kujerar ya sanya idan kuna dasawa da gwamnanka sai baka wata ministiri yaceka rika kula da ita, sannan ya rika baka wasu hukumomi yace kai ne shugabansu , ya kuma rika sanya ka kana jagorantar wasu kwamitoci. Duk wannan in wata matsala ta tashi gwamnan na iya kwace su cikin kyaftawa da basmallah. Kuma ba yadda zaka iya. Baka kuma da ta cewa

Wani tsohon mataimakin gwamna da nayi Magana dashi, ma anar kujerar sai yace ‘’ kujera ce ta biyayya ,wakilci, dan aike da kuma jiran me za a saka ,da aikata abinda aka ce ma kayi ,ya kara da cewa kujera ce ta hakuri da amfani da hikima ka zauna da kowa lafiya’’

Bincike na ya tabbatar mani wasu mataimakan gwamna za suyi ta hakuri,amma da an bar gwamnatin babu ruwansu da gwamnansu .don suna tuna cutarwa da gwamnan yayi masu. Nayi Magana da mataimakan gwamna biyu,wanda suke cikin wannaan koken . daya ya shaida mani cewa ‘ Duk halin da na shiga gwamna na ne ya saka ni sai fara kawo hujjojinsa.’’ Dayan kuma ya shaida mani cewa. ‘’ yanzu zaman kai na nake nayi biyayya a lokacin da muna gwamnati kamar yadda tsarin mulki ya bani to yanzu ba gwamnatin ! sai kuma in ci gaba da biyayya?ga wa”

In ka ga dan siyasa a kujerar mataimakin gwamna abu uku yake nema wajen ka. Shawara, tausayawa, sai addu a.

Danjuma Katsina mawallafi/dan jarida, a na samunsa a 08035904408, email: katsinaoffice@yahoo.com. Twitter @danjumakatsina bayan an rubuta @Danjuma Katsina…. Ya na wallafa wata jarida da ke bisa yanar gizo mai suna Taskar Labarai

Advertisement
Click to comment

labarai