Connect with us

BIDIYO

Sharhin Fim Din ‘Daren Jiya’

Published

on

Suna: Daren Jiya

Tsara Labari: Ibrahim Birniwa da Buhari Isa Dandume.

Kamfani: Jamnazz Production

Jarumai: Sani Musa Danja, Jamila Nagudu, Baballe Hayatu, Aysha Abubakar, Shamsu Dan Iya, Salima Ahmad. Da sauran su.

Shiryawa: Nazir Dan Hajiya

Bada Umarni: Sadik N. Mafiya.

Sharhi: Hamza Gambo Umar

 

A farkon fim din an nuna Usman (Sani Danja) a cikin gidan sa tare da karuwar sa Safeena wadda yake yiwa sallama akan zai je wani waje ya dawo, amma sai ta nuna rashin amincewar ta saboda tana tsoron kada matarshi ta dawo gidan ta same ta. Usman ya nuna mata cewa matar shi taje asibiti zaman jinyar mahaifiyar ta wadda bata da lafiya kuma zata dau tsahon lokaci kafin ta dawo, bayan ya rarrashe ta ne ya tafi yaje asibiti ya duba jikin mahaifiyar matarshi Nusaiba (Jamila Nagudu) bayan fitowar sa daga asibiti ne ya hadu da wata budurwar shi Salma a tsaye akan titi ya dauke ta a mota suka tafi. Bayan Salma ta shiga motar ne sai ta fuskanci cewa gidan sa zasuje ba hotel ba, hakan yasa ta nuna rashin amincewar ta amma bayan ya gaya mata matar shi bata gidan kuma akwai wata budurwar tashi a gidan sai ta amince.

A bangare daya kuma Nusaiba (Jamila Nagudu) wadda ke jinyar mahaifiyar ta sai ta fadawa mahaifiyar ta zataje gida ta debo kayan sawar ta saboda nata sunyi datti, mahaifiyar ta bata amince da tafiyar ta ba har zuwa lokacin da Zayyad (Garzali Miko) kanin Nusaiba ya shigo asibitin, sai Nusaiba ta aikasa gidan da motar sa don ya debo mata kaya. Bayan Usman da budurwar shi Salma sunje gidan sa sai mai gidan gidan nasa wato Lado (Shamsu Dan Iya) ya soma mamakin yadda usman ya jefa kan sa a halin neman mata. Bayan Usman ya shiga cikin falo sai Safeena karuwar da ya bari a gida ta soma jan Salma da rigima akan sai ta kori Salma amma sai Usman yaki amincewa da hakan har Safeena tayi zuciya ta bukaci ya bata kudin ta zata tafi gida amma sai ya rarrashe ta ya nuna bazai kwana a dakin da ya ajiye Salma ba. Zayyad kanin Nusaiba yazo gidan Usman amma sai Lado megadi ya hana shi shiga saboda umarnin da Usman ya basa na cewar ko mahaifiyar sa ce tazo kada ya bari ta shiga. Zayyad ya fusata ya kira yayar sa Nusaiba sai itama ta fusata tace ya dawo Ita zatazo da kanta. Hakan kuwa akayi ta karbi motar Zayyad bayan ya koma ta nufo gidan Usman don dibar wasu kayan sawar.

Lokacin da Usman ya shiga cikin dakin da Salma take sai ya ganta a kwance cikin jini an kashe ta hakan ya tashi hankalin sa har itama Safeena tagane halin da ake ciki, a daidai sannan ne matar sa Nusaiba ta shigo cikin gidan taga Usman tare da Safeena wadda ta kasance kawarta. Bayan Nusaiba ta gama cin alwashin cewa ta gama zama dashi sai ta shiga cikin daki don kwashe kayanta anan ne taci karo da gawar Salma. Hakan ya firgitata ta fito falo, a wannan lokacin ne kuma jami’an tsaro suka shigo cikin falon tare da mai gadi wanda yayi musu rakiya, suka shigo akan sun fito neman wani barawo da suke zargin ya shigo cikin gidan, sun soma yunkurin fara bincike ne sai aka kira wayar daya daga cikin yan sandan (Baballe Hayatu) aka sanar masa da cewar an kama barawon acan wani wajen. Hakan yasa suka tafi, yayin da itama Safeena ta bukaci Usman ya bata kudin ta amma ya hana ta hakan yasa tayi fushi rabar gidan. Bayan Safeena tabar gidan ne sai Nusaiba ta taimakawa Usman suka dauki gawar Salma aka sa a mota ya tafi don ya yar.

Usman na tafe a mota sai motar ta lalace hakan yasa ya kira Nusaiba ta dauko motar Zayyad ta kawo masa ya saka gawar a ciki, amma bayan yayi nisa sai ya hadu da yan sanda suka rutsashi ya bude bayan motar, amma koda ya bude sai akaga babu komai a ciki, hakan ya jefa Usman cikin mamaki ya dawo gida ya fadawa matar shi Nusaiba halin da ake ciki.  A wannan lokacin ne kuma Safeena ta dawo gidan tare da ‘yan sanda wadanda ta gaya musu cewa anyi kisan kai a gidan. Bayan jami’an tsaro sun bincike gidan ne basu ga komai ba sai digon jini wanda Usman yayi musu karyar cewa matar sa Nusaiba ce take al’ada har ya zuba a kasa. ‘yan sanda sun yarda da hakan kuma sun fita daga gidan tare da Nusaiba. Bayan faruwar hakan ne kuma Lado ya shigo cikin gidan ya fada musu duk yasan abinda ke faruwa kuma yasan budurwar data shiga gidan har ta kashe Salma, sannan kuma shi yabi bayan Usman ya cire gawar dake motar sa a sanda ya tsayar da motar zai yi fitsari, bayan ya cire gawar ne yaje ya yar a daji a sakamakon shima Usman ya taba taimakon sa a baya kuma yayi amfani da wannan damar ne don ya taimaka masa shima.

 

Abubuwan Birgewa:

1- Anyi amfani da basira a labarin ta hanyar saka abubuwan da suka rike me kallo.

2- An nuna illolin da cin amana ke haifar wa.

 

Kurakurai:

1- Lokacin da Nusaiba ta baro asibiti tazo gidan Usman don dibar kayan sawar ta, an ga tayi parking din mota a bakin get, amma lokacin da ‘yan sanda suka zo zasu shiga gidan me kallo baiga motar a inda ta ajiye ba, shin ina motar take?

2- Camera tayi rawa a lokacin da aka fara nuno gawar Salma a cikin dakin Nusaiba.

3- Lokacin da jami’an tsaro suka fara shiga gidan Usman, an nuna Usman da Safeena har da Nusaiba duk a zaune kamar masu jiran umarni, a irin tashin hankalin da Usman suka shiga shida Nusaiba bai kamata duk a gansu a zaune ba, domin ya dace aga Nusaiba tana tuhumar Usman akan batun gawar data samu a cikin dakin ta, ba wai a gansu jugum a zaune ba.

4- An nuna Lado ya rufe get din gidan Usman a sanda Nusaiba ta dawo daga asibiti, amma sai akaga kofar a bude a lokacin da jami’an tsaro suka shigo cikin unguwar. Ya dace a samar da dalilin da yasa aka sake bude kofar.

5- Lokacin da Safeena ta shigo gidan Usman ta tarar da Safeena, ya dace ace ta kore ta saboda fahimtar abinda suke aikatawa da mijinta, haka itama Safeena ko ba’a koreta ba ya dace ta kori kanta daga gidan tunda tasan bata da gaskiya, amma sai mai kallo yaga har ta samu ‘yancin zama tare da su Nusaiba a falo, a zahiri sam hakan ba abu ne da zai yiwu ba.

6- Falon da aka nuno Usman ya fara shigowa tare da Salma, falon yasha bamban da wanda aka nuna jami’an tsaro sun shiga don yin bincike, shin falon gidan guda biyu ne?  Gidan bai yi kama da mai falo biyu ba kuma falo na biyun bai yi kama da cewar a cikin gidan bane, bai dace a nuna wannan falon ba don hakan zai iya rikitar da tunanin me kallo.

7- Shin wacece budurwar da ta shigo gidan Usman ta kashe Salma? Ya dace a bayyanawa me kallo matsayin ta da kuma dalilin ta na shigowa gidan har ta kashe Salma.

8- Ba’a nuna wa mai kallo cewar Usman yayi nadamar abinda ya aikata ba, sannan kuma matar shi ba’a ga tadau mataki don yiwa tufkar hanci ba.

 

Karkarewa:

Fim din ya nishadantar, amma labarin bai tafi kai tsaye har karshe ba kuma zaren  labarin bai dire ba.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!