Yadda Jihadin Fulani Ya Kasance A Kano 1803-4 (5) — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

TARIHI

Yadda Jihadin Fulani Ya Kasance A Kano 1803-4 (5)

Published

on


Kisan Malam Dan Gabuwa

A sa’ar da rundunar da Sarki Alwali ya turo tayi nufin yaki, sai suka sare dukkanin bishiyoyin dake kewayensu, wuri ya zamo fili thabiyr .

Bayan sun gama, sai suka tura wasu tsiraru domin kaiwa masu jihadi farmaki. Da isar au kuwa sai aka soma fafatawa, amma jin kadan da haka sai suka juyo da gudu, inda masu jihadi kuwa suka biyosu abaya suma da gudu, ashe ramin mugunta aka kullawa masu jihadi basu sani ba.

Masu jihadi basu fahimci haka ba sai da suka gansu tsulundum cikin gagarumar runduna an hau su da sara da suka, ai kuwa a wannn rana an kashe da yawa daga masu jihadi.

Amma fa kashe gari, sai masu jihadi suka sake dawowa, suka hau sadaukan nan da kisa. Yaki sabo ya sake ballewa, kowacce runduna ta himmatu bisa samun nasara akan abokiyar bugawarta.

Daga karshe, bayan an shafe wuni ana gwabzawa, masu jihadi suka samu nasarar karya lagon wannan runduna, inda suka tarwatsa su tare da kone mazaunin su dake Jalli da Makachi.

Sarki Alwali yaji matsanancin haushi bisa wannan asarar yaki data auku. Don haka ya yanke shawarar fitowa da kansa domin a gwabza, inyaso duk mai yiwuwa ta yiwu.

A tare da sarki Alwali akwai sadaukai kari bakwai masu sanye da sulken bakin karfe. Haka suka baro Kano izuwa inda masu jihadi suka yada zango anan Tomas, amma da sukai gaba-da-gaba, sai Sarki Alwali ya waske, ya shige garin Dawakin Tofa, inda ya kone garin tare da kashe dukkan mazajensu ciki harda alkalan garin bisa klaifin chaffar da yaji sun kaiwa masu jihadi.

A lokacin kuma, sai masu jihadi suka bar inda suke izuwa wani gari mai suna ‘Bakin Ruwa’, a cikinsu kuwa har da wasu shahararrun sadaukai hausawa da ake kira Dantunku da Maiduniya.

Da Sarki Alwali yaji sun tashi, sai shima ya tashi izuwa kusa dasu, ya sauka a wani gari mai suna ‘Danyaya’, an ce harma masu jihadi na jiyo sautin tambura da gangi da ake kakawa sarki Alwali daga inda suke.

A tarihin yakin jihadin Kano, an ce saida rundunar masu jihadi suka gwabza yaki har sau 93 a tsawon watanni hudu, amma a wannan karon ne kurum sarki Alwali ya fito cikin runduna za’a gwabza dashi a yaki.

Sarki Alwali ne ya jagoranci wannan yaki da kansa wanda suka farwa masu jihadi a ranar wata litinin da yamma, suka kone gidaje da dawakan masu jihadi, anan nema Mal Dangabuwa ya rasa ransa, amma cikin ikon Allah kafin bullowar alfijir sai da masu jihadi sukayi galaba akan rundunar Sarki Alwali, tilas ya juya da baya da gudu.

Bayan wani lokaci sai suka sake dawowa wurin, a tsammaninsu zasu tarar masu jihadi sun bar wurin fadan, amma sai suka tarar dasu cirko-cirko kamar masu jiran wani abu, ga gawarwaki nan a zube fululu..

Wasu daga rundunar sarki Alwali suka kaga murya suna tambayar masu jihadi cewa “ashe har yanzu kuna wannan wuri?” Sai kuwa masu jihadi suka amsa musu da cewa “eh munanan, kuma anan zamu kasan ce”

Sai kawai sarki Alwali ya umarci a juya da baya, yana mai cewa koda anyi fada babu nasara a wannan lokaci.

 

Samun Taimakon Sarki Alwali Daga Daura Da Kuma Cinye Garin Danyaya

Sarkin Daura na lokacin (Sarkin Gwari Abdu) ya kawowa dakarun Alwali dauki. Kashe gari aka sake gwabza faka da rundunar masu jihadi.

A wanna rana masu jihadi sunyi matukar jigata saboda wahalar yaki, ga yunwa dake damunsu. Don haka basu samu nasara a yakin ba.

Amma bayan yaki ya k’are da dare, sai malumma shugabanni ga masu jihadi suka taru domin tattauna mafita garesu.

A wannan lokaci, dukkansu sun gamsu da cewar kamata yayi su bar wannan wuri izuwa ga Malam Bakatsine wanda ya aiko musu da sakon albishir na cewa ya kame iko da garin Gaya.

To sai kuma aka shiga shawarar tayaya za’a tafi can din?

Wasu suka ce a tafi da dare, Malam Abdurrahman yace ai idan aka tafi da dare za’ace guduwa sukayi. Sai Malam Jibrila yace a bari da safe su sake yakar wannan runduna, in yaso sai Allah yayi hukunci a tsakanin k’arya da gaskiya.

Shikenan kuwa sai kowa ya gamsu da hakan.

Da gari ya waye sai aka sake shiga yaki. Aka buga yaki mai tsanani, har sai da masu jihadi suka soma cin galaba akan rundunar Sarki Alwali.

Koda Sarkin yaga haka, sai yayi saurin janye rundunarsa ya shige cikin garin Danyaya yasa aka kame kofar gari.

Masu jihadi suka bisu a baya har bayan gari. Daga nan sai suka zauna suna jira.

Ba tare da wata jimawa ba sai mutan garin Danyaya da dakarun Alwali suka soma fitowa waje, da alamar za’a sake yin fada kenan.

Da suka fito sai suka jeru suna fuskantar rundunar masu jihadi, wasu cikinsu suka kaga murya suna cewa kun kawo kanku ga mahalaka.

Nan take kuwa matan dake cikin masu jihadi suka barke da kabbara, suka amsa musu da cewa “Kwarin guiwarku abune mai kyau”. Daga nan fa sai fada ya barke.

A ka shafe dare dukkansa ana fafatawa, daga bisani dai masu jihadi sukayi galaba, inda suka kashe mazaje da yawa daga rundunar sarki Alwali, suka kone ganuwa da rushe wani yanki, suka shige garin tare dayi masa kawanya, gashi kuma Sarki Alwali yana cikinsa.

Daga baya dai sai Malumma Shugabannin masu jihadi sukayi shawara, sukace a kyale sarki Alwali ya fita daga garin ba tare da wani abu ya same shiba tunda yaga ikon Allah da idonsa.

Sai kuwa aka bude masa kofar gari, ya fice da wata tawaga ‘yar kadan tunda sauran duk sun tsere, wasu kuma an karkashe su.

A tare dashi a wannan lokaci akwai ‘ya’yansa biyu, chiroma wanda daga baya ya tuba har sarki bafullani na farko a Kano watau sulaimanu ya nakashi mai unguwar kutumbawa, sai kuma kanuwansa Madawaki. Ragowar kuma bayin sarki ne irinsu Sarkin yara, sarkin shanu da wasunsu.

 

Sakon Sulhu Daga Alwali Da Gudunsa Zuwa Zariya

A farkon sha’aban sai masu jihadi suka tafi ɓagwai, sannan sukayi Damargu.

A ɓagwai sun tarar mutan garin sun karya alkawari, sun sauka daga kan abinda suka ɗorasu akai, don haka sai suka farma garin, suka koresu. Daga nan suka tafi Tofa, sai suka wuce Gogori, suka isa Farin Ruwa, sai suka karasa Tambari, sannan suka tsallaka yankin katsina inda suka sauka a Kurkujan.

A can ne suka haɗu da Malam Ummaru Dallaje (wanda ya zamo sarkin katsina a shekarar 1816) da Malam Ishaka (wanda ya zamo sarkin Daura a shekarar 1805). Suka shafe watanni huɗu suna gwabza yaki da sadaukan daular katsina, amma daga bisani yunwa da gajiya yayi musu yawa, sai suka yanke shawarar komowa Kano.

Suka shigo Kano ta Taɓanni dake tsohuwar gundumar Gwarzo, sannan suka wuce farin ruwa, suka shiga Gogori, suka biya ta ɓagwai sannan suka nufi bichi.

Daga Bichi sai sukayi Damargu, sannan suka karasa Tomas suka sauka. Daganan kuma sai suka tura wata runduna bisa jagorancin Malam Jibrila izuwa garin Fagay, suka yaki garin tare da kone shi, sannan suka kamo bayi.

Sai dai ya kamata. Sani, a wannan lokaci, sarki Alwali a takure yake matuka, domin birnin Kano ne kaɗai a hannunsa, babu kuma inda yake iya zuwa.

Sarki Alwali ya aiko wasu malumma mazauna Kano da takardar neman sulhu ga rundunar masu jihadi. Malumman sune :Malam Kabara, Malam Gabto, Dan gwauranduma Sumailu, Malam Jabbo Alfulati, da Malam Goja.

A cikin takardar, ya bayyana cewar a shirye yake ya riski masu jihadi kuma yayi jihadi tare dasu koda kuwa zaiyi tafiya da kafa ne. yace kuma zai bi dukkan umarninsu.

Amma sai masu jihadi suka yi watsi da bukatarsa, suka ce ai tun da fari suka umarceshi yayi haka, amma maimakon yaji maganarsu sai ya shiga haɗa rundunar mayaka wadda zata halaka su, sai yanzu da Allah ya kunyatar dashi zaice yana son ya shigo cikinsu.

A karshe suka shaida masa cewar zasu kawo farmakin kwace Kano ranar sha biyu ga watan Rabiul Awwal.

Ranar wata lahadi da dare sarki Alwali ya sulale izuwa Rano bayan yaji sakon masu jihadi, inda ya ɗan kwana biyu sannan ya haura Zaria.

Ranar wata litinin kuwa da dare masu jihadi suka shiga Kano fare da kame iko da ita.

A bisa wata ruwayar an ce kwanaki arba’in da ficewar sarki Alwali daga Kano sukuma suka shiga, amma wasu sunce kwanakin arbain da ɗaya ne ba arbain ba.

Tun daga nan ne kuma suka kasan ce a cikin Kano tare da mallake sassanta duka.

Wannan kuma shine tarihin yadda aka kwace Kano da yaki a jihadin fulani.

Abu nagaba bai wuce yadda Malam Bakatsine ya halaka Sarki Alwali ba a garin burum-burum, da kuma yadda mulkin sarakunan fulani ya kasan ce, haɗe da kalubalen yakin da suka fuskanta kuma.

 

Soma Sarautar Fulani A Kano Da Sarki Sulaimanu

Malam Sulaimanu shine sarkin Kano na farko a jerin fulani. Tun bayan da Sarki Alwali ya fice daga Kano, fulani suka shige mata, sai ya zamo sun karɓe iko da ita baki ɗaya.

Kadi Muhammadu Zangi bai faɗi yadda aka zaɓi Malam Sulaimanu a matsayin Sarki ba duba da akwai manyan malumma da suka jagoranci gwabza yakin jihadi a Kano, misalin su Malam Abdurrahman, da Malam Jamo, da Malam Jibrila da Malam Bakatsine, da Malam Danzabuwa da Malam Usmanu Bahaushe da wasunsu.

Abinda ya ruwaito a Littafinsa Taykidil Akbar shine: Masani Muhammadu Bello ya haɗu da tawagar malumman Kano da suka jagoranci yakin jihadi a Birnin Gada. Sai ya basu takarda mai umartar su da cewar su zaɓi sarkinsu da kansu. Daga nan kuma sai suka zaɓi Malam Sulaimanu, kuma babu wanda yayi jayayya bisa haka domin dukkansu sun shaida yadda Allah Ta’ala ya kaskantar da ɗaukakakkun masu mulki, ya kuma ɗaukakasu da sarautarsu.

To amma dai, wata ruwayar baka tazo akan cewa Malam sulaimanu ya kasan ce shine ke yiwa masu jihadi limancin Sallah, don haka bisa umarnin shehu Usmanu da yace “limamin ku a sallah shine shugabanku” sai aka naɗa shi ya zamo sarki, yayin da sauran malumma suka zamo ‘yan kwamitin zartaswa wanda sarki bashi da ikon yanke wani abu sai da sahalewar su.

Saboda haka, an bayyana cewar anyi zaman lafiya a zamanin mulkin sarkin Kano sulaimanu.

A zamanin, sarautar Kano ta zamo ta daban, domin akwai mukamai da abubuwa da yawa na al’ada da fulanin suka ajiye tun bayan hawansu madafun ikon Kano. Inda yaki ya fara shine shekara ta 1807 inda akace Sarki Alwali ya dawo daga zariya, ya shiga garin burum-burum, yana kulla yadda zasu kawowa Kano hari domin ɗaukar fansa.

Ai kuwa sai Sarki Sulaimanu ya tura Malam Bakatsine izuwa garin da runduna gagaruma. Ai kuwa suka je suka farwa garin da yaki. Akayi fafatawa gagaruma, amma dai cikin ikon Allah suka samu nasarar kone garin da halaka sarki Alwali.

 

Advertisement
Click to comment

labarai