Yadda ’Yan Gudun Hijirar Borno Su Kai Sallah Cikin Matsi — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

MANYAN LABARAI

Yadda ’Yan Gudun Hijirar Borno Su Kai Sallah Cikin Matsi

Published

on


’Yan gudun hijirar sansanin Fariya da ke birnin Maiduguri a jihar Borno sun bayyana cewa sun gudanar da bikin karamar sallah a cikin rashin sukuni, inda kunci tare da rashin walwala su ka maye gurbin shagalin bikin.

’Yan gudun hijirar sun yi wannan korafin ne a sa’ilin da su ke zanta wa da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ranar Jumu’a.

Daya daga cikin mazauna sansanin; Malam Jiddah Ambari, ya ce sun gudanar da bikin sallah a cikin takura da damuwa, sabanin yadda kowanne iyalai su ka ji. Ya ce, sun kai kimanin sama da mutum 5,000, wadanda ke rayuwa a sansanin, amma bikin karamar sallar bana ba su yi shi cikin sukuni ba, ya na mai cewa babu abinci ballantana tufafin sawa.

Bugu da kari, ya sake bayyana cewa matsugunin ya na fuskantar karancin abinci, rashin tsafta da karancin kula ta fannin kiwon lafiya tare da rashin cikakken tsaro.

“Hakan ya tilasta ma na dole sai mun fita waje neman abinci da kanmu, yayin da wasu da dama a cikinmu dole su ke yin azumin dare, saboda babu abincin da za su ci. A can baya, watanni tara da su ka wuce, kungiyoyin agaji irin su Sabe The Children da makamantansu ne ke raba ma na abinci.

“Su kan tallafa ma na da kudi tare da kayan abinci a kowanne wata, amma a halin yanzu an dakatar da aikin jinkan. Wanda a halin da a ke ciki yanzu, mafi yawa daga cikinmu su na rayuwa ne a halin ni-’ya-su, inda wadanda ba su da galihu dole su ka tsunduma sana’ar barace-barace a kan titi, domin samun abinda za su rayu.

“Mun fito ne daga karamar hukumar Marte kuma tun bayan da mu ka zo wannan matsuguni yau sama da shekaru uku, babu wani mutum daga hukumar NEMA ta kasa ko hukumar SEMA a jihar Borno da ya taba kawo ma na dauki ko tallafi,” in ji shi.

Malam Ambari ya yi kira ga gwamnati da ta kawo musu daukin gaggawa a matsugunin nasu.  “Kuma ya kamata su daina kiran mu da matsugunin da ba a bisa ka’ida ba, saboda mu ’yan Najeriya ne wadanda mayakan Boko Haram su ka raba mu daga yankunan mu,” ya ce.

Har wa yau shi ma Mustapha Abdallah ya shaidar da cewa, akwai adadi mai yawa na kananan yara da mata da ke fama da cutuka daban-daban a sansanin ba tare da samun cikakkar kula ta magani ba.

“Mu na fama da manyan kalubale kuma dadaddu da mu ke rayuwa da su. Kuma kamar yadda kake gani a nan, mu na da kimanin kananan yara sama da 2,000 wadanda ba su zuwa makaranta. Wanda ta dalilin halin matsi mafi yawan iyayen ba su iya tura yayan su zuwa makaranta.

“Saboda wannan ne mu na gama gwamnati da Allah ta ceto rayuwar mu daga tagayyara, don Allah ku bayyana musu hakikanin halin da mu ke ciki.”

A yayin da ya ke mayar da martanin zarge-zargen ’yan gudun hijirar, kodinetan yanki a hukumar NEMA ta kasa, Malam Bashir Garga, ya musanta zancen tare da bayyana cewa an kafa sansanin ba bisa ka’ida ba.

Garga ya ce, gwamnati ta samar da gidajen kwana wadanda ’yan gudun hijirar ke zaune a ciki, kuma ga yan gudun hijirar da su ka fito daga kowacce karamar hukumar da wannan matsala ta Boko Haram ta shafa, amma wasu daga cikinsu sun yi taurin kan komawa inda a ka tanada mu su din.

Advertisement
Click to comment

labarai