Connect with us

KASUWANCI

Cikin Wata Biyu NNPC Ta Kara Kudin Kalanzir Sau Uku

Published

on

Hukumar kula da albarkatun mai ta kasa ta kara kudin farashin kananzir har sau nuku, tsakanin watan Mayu da kuma wannan watan, an dai kara kudin farshin man ne zuwa Naira 40 ko wacce lita, kamar dai yadda wani binciken da ka yi ya gabatar.

An gano cewar duk da yake akwai karin farashin ita Hukumar ta hanyar karamin kamfanin dake karkashinta, wato kamfanin dake rarraba shi man,ya daina rarrabawa su ‘yan kasuwar.

Yawancin ‘yan kasuwar na shi kananzir din, abinda aka fi da sanmin Dual Purpose Kerosine, wato kananzir wanda ake ayyuka daban daban da shi, sun bayyana cewar , sun dade da biyan abinda,. Har yanzun ba a kawo masu  shi ba, tun watan Nuwamba  na 2017 suka biya, duk da yake sun kara biyan wasu kudade zuwa PPMC, saboda karin farashin da aka yi.

Binciken da aka yi a Abuja ya nuna, su ‘yan kasuwa masu zaman kansu sun biya Naira milyan 4 da dubu 785 a kan ko wacce lita dubu33,000, ta DPK cikin Nuwamba 2017, wannan kuma shin yasa abin ya kai ga Naira 145 ko wacce lita. Amma kuma har yanzun ba akawo shi man ba.

Wasu daga cikinsu sun biya karin kudaden da suka kai Naira dubu 1675,000 ko wannen su, a cikin watan Maris na 2018, saboda su samu kayan, abinda kuma ya sa shi farashin kanan zir ya kai Naira 150 ko wacce lita, amma kuma duk da hakan basu kawo kananzir din ba.

Ranar 3 ga watan Mayu na wannan shekarar shi kamfanin PPMC ya fitar da wata takarda mai lamba, PPMC/CSD/UPM/0034, tana bada sanarwar wani sabon karin kudin kanazir, shi yasa kuma a wancan lokacin farashin lita ya kai Naira 179.83 na tsohon Defot na Lagos / Ijora, amma kuma farashin tsohiuwar matatar fetur ya tsaya akan Naira 168. 94.

An kuma kara samun sabon karin kudin kananzir na Naira 984,390 da kuma Naira 335,610 wanda aka yi ranar 9 ga watan Mayu da kuma 6 ga watan Yuni na wannan shekara, wadanda ‘yankasuwar da abin ya shafa suka yi, akan shi kanazir din da ka  biya tun watan Nuwamba 2017. Wannan shi ya kawo kudin kananzir ya zama Naira 190 ko wacce lita, wanda kuma aka yi a karo uku wanda aka kara farashin mai cikin watanni biyu

An ji labarin cewar ranar Talata a Abuja akan abinda ya shafi su ‘yan kasuwa masu zaman kansu, cewar yanzu dai basu samu an kawo masu kananzir ba, daga  PPMC ba, duk kuwa da yake an kara masu farashin man, sun kuma biya.

Sun bayyana cewar lokacin da suke sa ran daukar shi kananzir , sai kuma su samu wani sabon labari, daga PPMC, tana bayyana wani karin farashin kananzir, a kuma sanar dasu cewar, su sake biyan wasu kudaden, kafin su samu damar dauka.

Daya daga cikin ‘yan kasuwar da abin ya shafa wanda kuma baison a fadi sunan shi, saboda tsoron kada a dauki wani mataki dangane da shi, ya bayyana cewar ‘’ A watanni biyu da suka wuce Hukumar kula da albarkatun mai ta kasa (NNPC) ta yi karin kudin kananzir har sau uku, inda aka duba sosai ana iya gane ashe ma har sau biyar ne aka kara kudaden, abinda ya kai ga kusa da Naira milyan 1 da rabi.

Farashin lita 33,000 na DPK a karshen watan Nuwamba Naira milyan 4. da dubu785, wanda ya sa ke nan ko wacce lita ta kananzir ta kai Naira 145, saboda haka idan aka hada gaba daya, abin ya kai Nairan milyan daya da rabi, wannan shi yasa farashin kananzir ya tashi zuwa Naira 190 ko wacce lita.

Wani abin ban haushi shi ne sun ki su samar da kananzir din mai yawa, watanni bakwai da suka wuce,  duk lokacin da mutum yake ganin ya kusa samun damar dauka, kuma ka biya kudi , kamar yadda aka yi yarjejeniya, sai su baka labarin cewar su, ba zasu iya ba, saboda farashin ya sake karuwa.

‘’Wani babban bakin ciki shi ne har yanzu basu yarda sun samar da kananzir watanni bakwai da suka wuce’’.

‘’Don haka a watanni biyu da suka wuce NNPC ta hanyar kamfanin PPMC sun kara fashin DPK, sau uku zuwa hudu, muna ganin ai zamba cikin aminci ce abinda kuma bai dace ba’’.

Shi ma wani dankasuwa mai zaman kanshi ya ce, bai kamata saboda farashin danyen ya karu, ayi amfani da wannan damar, a kuma hana diloli daukar kayan da suka biya.

Ya yi kira da cewar tun da dai an biya kudaden, ya dace a bada kayan tun farko, ya kara cewar ita Hukumar, tana da damar ta sanar da su ‘yan kasuwar, dangane da karin farashin , amma kuma sai su bari sai an yi maganar wata sabuwar harkar.

Ya kara jaddada cewar ‘’ Mun san cewar farashinn danyen mai ya karu, amma kuma wannan ai bai kamata ba,ayi amfani da ita wannan damar, asa shi al’amarin akan,kayan da aka riga aka biya kudaden su. Kamata ya yi a samu bada wadanda aka biya kudadensu, daga nan kuma sai a sanar da diloli cewar, akwai karin kudin da za a yi, idan maganar sake sayen ta taso a gaba.

‘’A daina amfani da siyasar farashin danyen mai, da wani abinda za a yi amfani da shi, a cuci ‘yankasuwa masu zaman kansu, saboda suna ganin ita kungiyar yan kasuwar man fetur da kananzir,kamar kausashinsu ya yi kasa, wannan sam ma babu adalci, bai kamata kuma ace, sai a wannan gwamnati mai yaki da fatara da cin hanci za a yi haka ba’’.

Lokacin da aka tuntube shi babban jami’i na sashen hulda da jama’a na Hukumar kula da albarkatun mai ta kasa, (NNPC) Ndu Ughamadu, ya bayyana cewar al’amarin kananzir yanzu ya zama, wanda ya fara biya , shi za a ba, saboda kuwa shi kananzir wanda ake shigo da shi daga kasashen waje, yana da tsada, shi yasa aka hana wakilin ita Hukumar amsar kudade daga ‘yan kasuwa.

Ya ci gaba da cewar ‘’Muna sanarwa kasuwar da DPK yawanci daga Matatun man fetur, saboda wanda ake sayowa daga waje yana da tsada. Don haka muke amfani da wanda ya fara biya, shi ne za a ba, da farko, muka kuma fadawa wakilanmu da suke kulawa da sayar da man, kana su amshi wasu kudade  a matsayin biya, har sai wadanda suke da tickets shaidar sun biya kudin an kammala dasu’’.

‘’Kamar yadda kuka sani su ‘yan kasuwa masu hada hadar kananzir, suna son su biya akan DPK da kuma AGO(diesel) su kayayyakin da suka fi so ke nan, amma kuma idan aka ce matatu sun samu matsala, sai kuma su fara wata magana daban.’’

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!