Za A Hana Sa Maganar Cin Zarafi A Gidajen Rediyon Kano, Inji Ganduje — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Za A Hana Sa Maganar Cin Zarafi A Gidajen Rediyon Kano, Inji Ganduje

Published

on


Gwamnan jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa za su zauna da shugabannin masu gidajen Rediyo da talabishin a jihar dan hana sa duk wani kalami na cin zarafi da yan siyasa suke a jihar.

Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin da mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi na Biyu ya kai ziyarar sallah ta al’ada a gidan Gwamnati da a ka fi sani da hawan nasarawa.

Yayi nuni da cewa zage-zage da cin zarafin da ake na yan siyasa yana hana mutane masu gogayya da mutunci shiga harkokin siyasa a jihar kano.

Gwamna Ganduje ya ce wannan ba karamar kwarace ga jihar Kano ba kwarai da gaske domin sai ka sami mutum da yayi karatu mai zurfi yayi aikin Gwamnati yayi ritaya da za su iya zabe na majalisar jiha kota tarayya sanata da kowane mataki na siyasa su kare martabar jihar kano da kasar nan, amma sai kaga masu wannan cancantar sai su rinka jin tsoron shiga siyasa.

Ya ce, saboda suna jin tsoron a ci musu zarafi, kar a ci mutuncinsu har wasu ma suna cewa wai idan mahaifinka ya bata, ka na so ka gano inda yake to ya shiga siyasa.

Gwamna Ganduje ya ce, wani yana kwance kan gado inya bude rediyo kaji an ce an gano mahaifinka yana gyartai a wani kauye. “Dole ne mu tsaftace wannan yanayi za mu yi taro da shugabannin Rediyo dan ganin  masu baki da kunu, hancinsu da majina, kai da kora, kafa da faso su tabbatar idan yayi magana mara amfani gidajen yada labarai basu saba, ta haka ne kawai za a tsaftace wannan harkar.

Gwamna Ganduje ya ce, don samun fahimtar juna da wasu jam’iyyu Gwamnatin Kano tayi shan ruwan azumi da jam’iyyu kusan 50 wannan ba yana nuna cewa su dawo jam’iyyarka ba ne sai don tabbatar da fahimtar juna a tsakanin yan siyasar za su kuma cigaba da irin wannan zama lokaci-lokaci.

Tun a farko cikin jawabinsa Mai martaba sarkin yayi kira ga Gwamnati ta samar da samun tuntuba tsakanin yan siyasa ta yanda za a kai ga gudanar da harkokin siyasa ba tare da rikici ba, musamman ma dan gudanar da  zabe mai zuwa na 2019 cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Advertisement
Click to comment

labarai