Connect with us

KASUWANCI

Gum Arabic Research Institute: Da Yadda Take Gudanar Da Ayyukan Ta A Cikin Jihohi 12

Published

on

DAKTA OJIEKPON I FRED, shi ne shugaban cibiyar Gum Arabic Research Institute, wadda reshe ce ta Robber Research Institute, ta Nijeriya, da take gudanar da ayyukan bincike a tsakanin jihohi 12 masu albarkatun karo, wadda take da ofishin ta a Gashuwa ta jihar Yobe. Wanda wakilin mu MUHAMMAD MAITELA, ya zanta dashi dangane da ayyukan cibiyar. Inda ya tabo batutuwa da dama da suka shafi noman karo tare da matsayin sa a kasuwar duniya. A sha karatu lafiya.

Yallabai, a takaice jama’a za su so sanin wannan cibiya ta ku ta ‘Gum Arabic Research Institute’ da ke nan jihar Yobe.
Yauwa, da farko muna matukar godiya, bisa yadda kamfanin jaridar ‘Leadership A Yau’ ya samu zarafin kawo ziyara a wannan cibiya ta ‘Robber Research Institute’; sashen ta mai gudanar da bincike a kan itacen karo, mai mazauni a Gashuwa, dake jihar Yobe.
Cibiyar bincike dangance da itacen karo, bangare ce daga Robber Research Institute, ta Nijeriya, mai hedkwata a Nyanuma, dake birnin Benen a jihar Edo. Wanda ita kuma take a karkashin ma’aikatar ayyukan noma ta kasa, wadda aka dora wa alhakin ayyukan bincike da bunkasar itacen roba, da sauran itacen da suke da dangantaka da ita, wanda itacen karo yana daga ciki; ana noma itacen karo a yankin arewa, yayin da ita kuma roba a yankin kudancin kasar nan.
An kirkiro wannan cibiya ne a shekarar 1961 a matsayin ma’aikata, wanda daga bisani aka sauya ta zuwa cibiyar gudanar da bincike; a karkashin gwamnatin tarayya a 1973. Wanda kuma a shekarar 1994 zuwa 1995 ne gwamnatin tarayya ta yi tunanin sake farfado wa tare da habaka kayan amfanin gona, wadanda za a iya gigayya dasu a kasuwannin duniya. Gwamnati tayi wannan tunanin ne domin rage dogaro da albarkatun mai kadai da ta dogara dashi wajen kudin shiga, da hada-hada a kasuwar duniya.
Bugu da kari kuma, baya ga itacen roba da na karo, wannan shirin ya hada da itacen kwakwar man-ja, gyada, koko da dangogin su; wadanda wannan cibiya ke gudanar da bincike a kan su tare da bunkasa su, yayin da itacen karo shi ne na biyu; bayan itacen roba.
Kuma kamar yadda na bayyana da farko, akwai bambancin muhalli wajen noma itacen roba da na karo, wanda hakan ya jawo gwamnatin tarayya ta baiwa babbar hedkwatar dake Benin kan cewa dole ta samar da wata cibiya- takwarar ta a waje wadda zata gudanar da ayyukan bincike a kan itacen karo, yayin da bincike ya tabbatar kan cewa jihar Yobe ce aka fi samun itacen karo da noma shi a tsakanin jihohi 12; Kebbi, Sokoto, Zamfara, Katsina, Kano, Jigawa, Yobe, Borno, Gombe, Bauchi, Adamawa da Taraba, wadanda ake noma shi a arewacin Nijeriya.
Kuma al’adance, itacen karo yana girma ko noma shi ne a wuraren da sahara ne, kuma yankin da aka fi samun sa da yawan gaske, a Nijeriya su ne jihohin Borno da Yobe. Wannan shi ne ya jawo aka kafa ‘Gum Arabic sub-station, a nan Gashu’a’ da ke jihar Yobe. Sannan tun a shekarar 1995 ayyukan da muka sa a gaba su ne gudanar da bincike tare da bunkasa wannan itace na karo.

Wadanne ayyuka ne wannan cibiya ta fi mayar da hankalin ta a kan su?
Kamar yadda na fada, muhimman ayyukan mu su ne gudanar da bincike, sannan kuma an kafa wannan cibiya ne domin ta fadada binciken alakar itacen da muhalli (Agronomist), da yadda ake aiwatar da girbar karon a gargajiyance; inda muka habaka shi zuwa na kimiyyar zamani, domin ci gaban wannan aikin.
Baya ga wannan kuma, wannan cibiya da ke nan Gashuwa a jihar Yobe ita take aiki kafada da kafada wajen bunkasa noman karo a cikin wadannan jihohi 12, a Nijeriya- tun daga Sokoto zuwa Taraba. Sannan da kulla alaka tsakanin manoman karon da masu sana’ar sa, tare da bayar da bayanai yadda kasuwar karo ke gudana. Saboda burin kowanne manomi shi ne yadda zai sayar da kayan sa, idan sun nuna.
Har wala yau, daya daga cikin aikin binciken mu shi ne taimakon manoma wajen cin gajiyar abin da suka noma. Mu gaya musu inda masaya hajar su suke, tare da basu shawarar adadin da ya kamata su sayar a daidai lokaci kaza, kuma muna da alaka da masu sayan karon a cikin gida da kasashen waje- wanda mu ne a matsayin tsakani.
Wani bangare daga cikin ayyukan mu, shi ne muna baiwa gwamnati tare da masu ruwa da tsaki a sha’anin al’umma shwara dangane da yadda za a bunkasa itacen karo da noman sa, a Nijeriya. Kana kuma muna da hadin gwiwa da manyan cibiyoyin ilimi- jami’o’i da kwalejoji, wajen gudanar da binciken habaka noman karo da sauran ayyuka masu dangantaka da shi. Wanda duk lokacin da hakan ta taso, a shirye muke da mu basu dukkan bayanan da suke bukace dasu, ko kayan bincike da muke dasu a dakunan gwaje-gwajen mu.

Gum Arabic Research Institute, cibiya ce wadda take aiki kafada da kafada da manoma, ko akwai matsalolin da kuke fuskanta daga junan ku?
Haka ne, dangane da al’adar cibiyoyin gudanar da bincike a Nijeriya; akwai wani tsarin bincike da muke kira, kwarmata sakamakon bincike, wanda zai sada tsakanin binciken da wannan cibiyar ta gudanar zuwa ga manoma, a daidai matsayin yadda cibiyar take nufi. Wanda koda-yaushe yunkurin mu shi ne mu fadada bincike tare da kimiyya da fasaha wajen magance wasu matsalolin da manoman karo ke fuskanta, yan kasuwar sa tare da bangaren gwamnati da ke kokarin bunkasa harkar. Yayin da kuma mukan yi amfani da nagartattun hanyoyi wajen isar da wannan sakon zuwa ga inda ake nufi ya je; ta hanyar ‘Research edtension linking system’.
Wanda ta haka muka tanadi ofis na musamman mai kula da alaka a tsakanin cibiyar da manoman, wanda suke kokari wajen sanin bukatun manoman, da yadda suke fahimtar aikace-aikacen mu. Sannan muna haduwa dasu lokaci bayan lokaci domin koya musu wasu sabbin lamurra dangane da aikin nasu, kai ziyara a gonakan su tare da basu shawara. Uwa-uba kuma da shirya musu tarukan karawa juna sani, domin tattauna muhimman batutuwa a kan sana’ar noman karon.
Ta hanyar wannan mu’amala ce muke fahimta tare da gano matsalolin manoman, inda su ma za su kara fahimtar wasu abubuwa tattare da cibiyar tamu. Wanda ta hakan ne muke daukar ingantattun matakan kimiyyar warware matsalolin manoman da noman karon.
A batu na daban kuma, mun yi kokari wajen magance wata matsala wadda manoman karo ke fuskanta; ta daukar shekaru kafin manomi ya fara cin gajiyar itacen karon- inda a baya yake daukar tsawon shekaru 4 zuwa 5 ko 7, kafin a fara dibar sa. Matsalar da ke kawo tarnaki a tsakanin manoma da cibiyoyin bayar da lamuni (bashi). Shi ne yanzu sai muka samar da irin da yake nuna a tsakanin shekaru 3 zuwa 4. Wanda idan manomi ya zo wajen mu zamu bashi wannan irin kuma da zarar ya bi tsare- tsare da shawarwarin da muka bashi a lokacin shuka da renon itacen, to zai fara cin gajiyar karon sa a cikin wadannan shekarun.
Haka zalika kuma, a tarihance, itacen karo ya samo asali ne daga kasashen Afrika; ba zaka same shi a kasashen tarayyar Turai ba, ko Asiya, sannan kuma itacen karo baya yi a kasar Amurika. Sannan nan Afrika ce asalin sa; ba daga wata kasa aka shigo dashi ba, muna da nau’ukan tsiron sa daban-daban, kuma kala-kala. Bugu da kari, tarihi ya tabbatar da cewa Nijeriya tana daya daga cikin inda aka yankewa itacen karo cibiya a tsakanin kasashen Afrika 16. Sannan kuma, jihohin Borno da Yobe, su ne tushen itacen karo a Nijeriya. Wanda indan ka bi tarihi, mutumin Kebbi zai gaya maka cewa, shekaru aru-aru da suka wuce, zai gaya maka ya zo Yobe domin ya sami irin itacen karo, haka mutumin Gombe zai ce maka ya zo da itacen karo ne daga Borno, ya shuka kuma yake ci gaba da habaka har yanzu.
Sannan kuma, mafi yawa kamfunan harhada magunguna da kayan abinci ne ke amfani da karo, matsayin sinadarin da sukan yi amfani dashi. Yayin da kuma wadannan kamfuna, sun da ma’aunin tantance karon zuwa aji uku (grade 1,2,3) a kasuwanin duniya, wanda kowanne aji kimar sa daban.
Bisa ga wannan, a matsayin mu na cibiya mai gudanar da aikin bincike, mun yi kokari wajen samar da ingantattun iraruwa na itacen karo, wadanda suka yi daidai da bukatar wadannan kamfuna a kasuwar duniya, da zarar manomi ya zo zamu bashi irin tare da tsare-tsare da shawarwarin da idan ya bi za su bashi natija.

To ta wacce hanya ce manomi zai ci gajiyar ‘Gum Arabic Research Institute’,?
Makasudin kafa wannan cibiya ta Gum Arabic Research Institute, shi ne domin ta warware matsalolin da manoman karo ke fuskanta, ba tare da karbar ko sisin kwabo a hannun jama’a ba. Sai dai idan za su sayi kayan aikin noman ko iraruwa daga wajen mu, a tsarin farashi mai rahusa. Muna da dubban iraruwan itacen karo da gwamnatin tarayya ta samar, domin manoma, inda aka zabtare kaso 80 cikin farashi.
Sau-tari manoma ko gwamnati da masu ruwa da tsaki a sha’anin al’umma kan zo nan tare da bukatar cewa suna son yin gonar itacen karo, ko yadda za su hada hannu damu wajen bin hanyoyin da za a bunkasa wannan aikin, wanda mukan basu shawara da matakan da ya kamata su dauka domin ganin kwalliya ta biya kudin sabulu tattare da wannan niyya tasu. Tare da bayar da shawara dangane da yanayin kasuwa ko manoman kan su.

A karshe, ko wadanne nasarori wannan cibiya ta samu- a wadannan shekarun da aka kafa ta?
Abu na farko, mun yi kokari wajen tallafa wa masu son zuba jarin su a noman karo, wanda da dama sun samu zarafin mallakar gonakan itacen karo. Wanda a kowacce shekara irin wadannan mutane kan zo nan su sayi iraruwan itacen karon tare da neman taimake su da kwararrun ma’aikatan mu da sazu basu shawarar yadda za su dasa itacen da hanyar renon su.
Wadannan kwararrun ma’aikatan su ne za su jagoranci wannan aiki tare da nuna adadin da ya kamata a dasa a kowacce kadada daya ko yanki na kowanne filin gona, wanda hakan zai sa manomi ya ci ribar abin da ya dasa na karon. Haka kuma, rashin kiyaye ka’ida yana jawo asara ko tasgaro a gonar manomin karon. Sannan kuma muna rarraba musu kayan noma na zamani wadanda za su taimaka musu a aikin.
Wani zubin kuma, Gum Arabic Research Institute tana shirya tarukan bayar da horon sanin makamar aiki, wanda muke hada hancin manana da masu safarar sa da kusoshin gwamnati wuri guda domin sanar da su hanyoyi daban-daban na fasaha da kimiyya wajen bunkasa noman karon tare da karfafa su da sabbin kayan noma na zamani.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!