Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Rashin Cika Alkawari Ya Sa Na Kashe Uban Gidana Soja Da Buduwarsa (1)

Published

on

Wani mai yiwa wani sojan ruwa hida a gidan ya bayyana dalilin da ya sanya shi ya hau dokin zuciya har ya kashe uban gidan sa da Laftar Abubakar Yusuf dan shekara talatin da biyar tare budurwar sa mai suna Lorraine Onye saboda wahalar da yake sha a gidan.
Mai hidimar mai suna Raphael Jaja ya dai kashe budurwar ce wadda take kan karatun zaongo na uku tare da Yusuf ta hanyar chaka masu wuka yakuma saka gawar gawar ta a cikin buhu ya kai daji ya channa mata wuta.
Ajaja wanda ya fito ne daga karamar hukumar Opobo-Nkoro dake cikin jahar Ribas, ya sanar da cewar, ya yanke shawarar aikata ta’asar cesaboda ubangidan nasa yaki ya biya shi albashin sa har na tsawon watanni sha biyar, amma ubangidan nasa ya iya sayawa budurwar tasa wayar tafi da gidan ka da kuin ya kai naira 300,000 da kuma biya mata kudin dakin da take yin haya.
Ya ci gaba da cewa, ubangidan nasa ya yi masa alkawarin zai dinga tara masa albashin ne duk wata, inda zai biya shi gaba daya saboda Jaja yana son ya tara kudin don shirye-shiryen auren sa.
Ajaja ya kara da cewar, saba alkawin da ubangidan nasa ya yi na kin biyan sa albashin ya tinzira shi ya dauki matakin.
Rahotanni sun bayyana cewar, jami’in sojan ya ne ya kashe budurwar tasa ya kuma ware, inda sai daga baya bayan binciken da jami’an ‘yan sanda na farin kaya dake ofishin shugaban ‘yan sanda na kasa da DCP Abba Kyari ke jagoranta ya gudanar da bincike bayan da rahoton da
mahaifin sojan ya kai ga ‘yan sandan, aka gano gaskiyar lamarin.
Jami’an ‘yan sandan sun a lokacin binciken sun gano wayar tafi da gidan ta sojan a gun wani abokin Jaja dake Fatakwal, inda abokin ya ce, ya sayi wayar ce a gun Jaja kuma abokin ya jagoranci jami’an ‘yan sandan suka cafko Jaja a ranar hudu ga watan Yuni na shekarar 2018.
Jami’in ‘yan sanda ya shedawa wakilin mu cewar, Jaja ya amsa laifin sa, inda kuma ya jagoranci ‘yan sandan zuwa dajin da ya da kai sojan da budurwar ya kona su da kuma motar sojan kirar Hyundai Beloster da Jaja ya sayar akan naira miliyan 1.9.
A cewar jami’in ‘yan sandan sun kuma gano wayar tafi da gidan ka ta sojan da jaja ya sayarwa da abokin sa akan naira 30,000.
Jaja dan shekara ashirin da takwas ya bayyana yadda ya hadu da sojan har sojan ya bashi dakin kwana a gidan sa.
A cewar sa, “sana’ata ita ce gyaran wutar lantarki kuma nayi aiki a filin tashi da saukar jiragen sama na kasa da kasa dake birnin tarayyar Abuja, daga baya na dawo Fatwal a shekarar 2016 saboda rashin lafiyar dan uwana.”
Ya kara da cewa, a watan Yuli na shekarar 2016 ne wani ya hada ni da marigayin a lokacin da marigayin yake son a sanya masa na’urar kallo ta DSTB.
Jaja ya ce, a lokacin marigayin yana aiki ne a makarantar firamare ta sojojin sama dake Fatakwal, inda bayan kafa na’urar ta DSTB sai marigayin ya umarce in sanya masa wata wasu wayoyi ganin yaji dadin aikin dana yi masa.
A cewar sa, “na gaya masa cewar nafi son in koma Abuja, amma yaja ra’ayi na inci gaba da zama dashi don in dinga yi masa aiki,inda ya bani makulin dakin daya n a gidan da muke zaune tare.
Ya bayyana cewar, ya yi alkawin biya na albashin naira 15,000 duk wata, inda ya ce zai dinga tara min kudin har lokacin dana sanya zan yi aure a watan Disambar 2017 ya kuma hadu da buduwar tasa ne 2017, kuma duk a lokacin data kwana a gidan, yana umarta ta in kwana dakin ajiye
kaya dake a tsakar gidan.
Jaja ya kara da cewar, marigayin ya taimaka min aiwatar da wata kwangila da kudin ta ya kai naira miliyan 22.8m a cikin watan Satumbar 2017, inda ya yi mini alkawarin zai bani kason naira miliyan 2.5 kuma bada sunan sa ya yi amfani wajen neman kwangilar ta samar da kwamfutoci ga makarantun ba. A cewar Jaja, “a lokacin dana ke
shirye-shiyen aure na, na tambaye shi ya bani naira 400,000, inda ya ce mini baida kudi, amma ya aro naira 320,000 ya bani.
A cikin watan Janairun 2018, na kara komawa gunsa na tambaye shi kudi na, inda ya ce mini baida kudi a saboda haka kada in matsa masa daganan na daina zuwa barikin sojojin.
Ajaja ya bayyana cewar, a watan Maris na 2018, ya kirawo ni kamar sau surin masaki ta hanyar wayar tafi da gidan ka, amma na share kiran nasa, amma daga bayan bayan na auki kiran nasa, ya sheda mini cewar ya samo mini wani aikin, inda dana je ofishin sa, ya ce mini ya baiwa wani akin saboda ya kira ni naki zuwa, sannan ya kuma ta yi mini dariya.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: