Kamfanin Bodafone Ya Sayi Kaddarorin Liberty Global A Kan Euros Biliyan18.4 — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KIMIYYA

Kamfanin Bodafone Ya Sayi Kaddarorin Liberty Global A Kan Euros Biliyan18.4

Published

on


Kanfanin Birtaniyan nan mai suna Bodafone ya amince da sayan kaddarorin katafaren kanfanin basar Amuurkan nan mai suna Liberty Global, kaddarori da harkokin tan a basashen turai a kan kudi Euro Biliyan 8.4 ($21.9 billion), wannan cinikin da aka yi ranar Laraba zai mayar da kanfanin ta zama mafi girma a nahiyar turai.
Cinkin day a yi daidai da Fam Biliyan 16.1, zai bayar da dama Bodafone ta mallake kaddarorin Liberty dake basashen Czech Republic da Germany da Hungary da kuma basar Romania, kamar dai yadda bayanin da aka fitar a garin Lanmda ya nuna.
An gudanar da cinkin ne da nufin gaggauta bunbasa harkokin kanfanin na Bodafone a kasuwar sadarwa na zamani.
Hakan ya nuna kenan Bodafone zai zama cikin jagororin kanfanonin sadarwa a nahiyar turai, domin kuwa zai taba gidaje da harkokin kasuwanci fiye da Miliyan 110.
“Wannan harka zai samar da cikaken harkar sadarwa na nahiyar turai da zai fuskanci gwagwamayar tsakanin kanfanonin sadarwa na duniya” inji shugaban kanfanin Bodafone, Mista Bittorio Colao.
“Muna fatan gaggauta samar da kanfanin sadarwa mai barfi, muna kuma dogara da bwarewar kanfanin Bodafone wajen samar da irin kanfanin da muke fata, domin tayi goggayya da sauran kanfanoni masu harka irin na sadarwa”.
Wannna cinikin ya nuna kena kanfanin Bodafone zai samarwa da mafi yawan mutanen dake nahiyar Turai wayan sadarwa na tafi da gidanka.
Sanarwar ya kuma bara da cewa, mallakar kanfanin Unitymedia a basar Germany zai samar da fagen gwagwamarmaya da azai fuskanci kanfani irin su Deutsche Telekom.
“Haduwar kanfain Bodafone dana Unitymedia zai samar dunbulalliya kanfanin da zai gamsar dad a jama’a a kasuwa harkar sadarwa a basar Jamus, hakan kuma zai samarwa da masu amfani kafafen sadarwar zabi.
A na saran kammala wannan cikin bayan amincewar hukumomin kula da harkokin sadarwa na Turai daga nan zuwa tsakiyar shekarar da muke ciki na 2019.

Advertisement
Click to comment

labarai