Matar Tsohon Gwamnan Adamawa Murtala Nyako Ta Rasu — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Matar Tsohon Gwamnan Adamawa Murtala Nyako Ta Rasu

Published

on


A daren laraba ne matar tsohon gwamnan jihar Adamawa Hajiya Zainab Murtala Nyako ta rasu, sakamakon gajiruwar rashin lafiya.
A sanarwar da iyalan marigayiyar suka fitar na cewa Zainab Nyako da ta rasu a babban asibitin gwamnatin tarayya dake Yola FMC, ta rasu tana da shekaru hamsin da biyar, da ya’ya shida.
Sanarwar ta ce marigayiyar Zanab an kaita asibitin ne cikin dare bayan ta yanki jiki ta fadi a bayan gida na tsawon lokaci ba tare da an sani ba, inda ta cika a asibitin FMC.
Haka kuma Hajiya Zainab Nyako, ta rayu da mijinta Murtala Hammayero Nyako, mahaifiyarta da jikoki da ya’ya shida.
Tuni dai akayi zana’idarta a jiya laraba bisa tsarin addinin musulunci, a gidan mijinta tsohon gwamna Murtala Nyako, dake Unguwar Dougirei a Yola fadar jihar Adamawa.
Kafin rasuwarta Hajiya Zainab Nyako, ta kafa kungiyar tallafawa mata da koyar da sana’o’in da take daukan nauyin gudanarwa Women Empowerment Education Iniatibe (WEEIN), haka kuma tayi karantun digri a fanin koyarwa.

Advertisement
Click to comment

labarai