Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

’Yan Fashi Sun Yi Wa ‘Yar Bautan Kasa Fyade A Bayelsa

Published

on

Wata da aka boye sunanta wacce kuma ta kasance mambace mai yi wa kasa hidima wato (NYSC), rahotonnin sun tabbatar da cewar wasu gungun ‘yan fashi da makami sun yi mata fyade da karfin tsiya a Yenagoa, da ke jihar Bayelsa.
Lamarin ta auku ne a lokacin da ‘yan bindigan suka kai farmaki domin yin fashi da makami a unguwar Yenizue Gene, da ke cikin garin na Yenagoa, inda suka riske ‘yar bautan kasar hade da yi mata fyade da kafin tsiya a ranar Lahadin da ta gabata.
Uku daga cikin ‘yan fashin sun shaida cewar sun mamaye unguwar ne wajajen karfe uku na safiyar ranar ta Lahadi, inda suka bude ruwan alburasai amma sun harbi babu ne domin sun yi ta harbin ne sama don razanar da kowa, suka shaida cewar ‘yan banga sun yi kokarin kai musu farmaki amma kuma sun kasance dauke da sanduna ne kawai da kuma adduna, lamarin da ya sanya ‘yan fashin basu ji shayin ‘yan bangan ba.
Rahotonin su zo kan cewar ‘yan fashin sun fara sace wa mambar NYSC wayoyinta, kudadenta, da wasu muhimman ababenta daga bisa suka yi mata fyade da kafin tsiya.
Wasu makwaftarta sun shaida lamarin a matsayin abun takaici, inda suka bayyana cewar sun kai mata dauki domin ceto rayuwarta.
“Bayan da suka kammala aikata, ta’asarsu, mun hanzarta kaita asibiti domin kula da lafiyarta,” In ji majiyarmu.
Mai Magana da yawun ‘yan sandan jihar, DSP Asinim Butswat, ya shaida cewar uku daga cikin wadanda suka aikata ta’asar sun fada tarkonsu.
Ya ce, suna samun rahoton aukuwar lamarin yi wa ‘yar NYSC fyaden ne kuma suka tashi domin kai dauki.
Butswat wacce aka yi wa fyaden ta samar musu da cikakken bayanai da zai kai ga gano wadanda suka tafka ta’asar, ya kuma ce, tuni ‘yan sanda suka himmatu domin taso keyar wadanda suka aikata wannan danyen aikin.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: