Ba Da Tallafin Aikin Hajji Abu Ne Da Ya Dace – Shaikh Jingir — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Ba Da Tallafin Aikin Hajji Abu Ne Da Ya Dace – Shaikh Jingir

Published

on


Kasancewar lokacin ayyukan hajji na wannan shekara ta 2018, sai kara kusantowa yake yi, an bukaci gwamnatin tarayya da ta yi ragi a kan yawan kudin da aka sa wa kowane maniyyaci da zai biya kafin ya sami zuwa sauke faralin a kasa mai tsarki.

Shugaban Majalisar Malamai na kungiyar Izalatil Bid’ah Wa’Ikamatus Sunnah, Shaikh Muhammadu Sani Yahaya Jingir, ne ya yi wannan kira a lokacin da yake jawabi wa dimbin Musulmin da suka hallara a wajen rufe tafsirin watan Azumin wannan shekara a Masallacin Jumma’a, na ‘Yan taya, da ke Jos, a ranar Alhamis din makon da ya gabata.

Shugaban majalisar malaman, ya nemi hukumar Alhazai ta kasa da hukumomin Alhazai na Jihohi, da su rika sanya masu ilimin Addinin Musulunci su rika gudanar da harkokin ayyukan tafiya aikin hajji don a sami saukin tantance maniyyata da ke da sukunin zuwa Saudiyya don yin aikin hajji.

Shaikh Jingir, ya yi amfani da wannan dama don yaba wa nasarorin da gwamnati mai ci yanzu karkashin jagorancin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ta samu a cikin shekaru uku da ta yi da kama aiki, ya ce, nasarorin da gwamnatin ta samu bisa yakin da take yi da kungiyoyin ‘yan ta’adda kamar Boko Haram, da yaki da cin hanci da rashawa, abin a yaba ne ainun.

Ya hori al’ummar Musulmi da su zama masu aiki da darussan da aka karantar masu a lokacin watan Azumi a koyaushe kuma su kara hada kai da junansu, su kuma tabbata sun mallaki katin dan kasa da na yin zabe don tinkarar zabubbuka masu zuwa na 2019.

 

Advertisement
Click to comment

labarai