Kabilar Maori: Masu Bayar Da Sadakin Aure Da Fatun Karnuka — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

Uncategorized

Kabilar Maori: Masu Bayar Da Sadakin Aure Da Fatun Karnuka

Published

on


A yau mun kewaya mu ka kuma kutsa cikin duniya in da muka ci karo da mutanen kabilar “Maori”.

Filin namu zai sada ku da al’ummar ‘Maori’ da ke kasar  ‘New Zealand’.

Su dai wadannan kabila ta Maori, cikakkun ‘yan kasar New zealand ne. A yarensu su kan ce ‘Tangata whenua’ wato cikakkun ‘yan kasa, mutanen sun samo asali ne daga tsuburin gabashin ‘polynesia in da su ka yo hijira zuwa kasar ta New zealand a kan kwale-kwale shekaru darurruka da su ka gabata.

 

Mutanen Maori,mutane ne ma su tarihi da kuma al’adu ma su taka muhimmmiyar rawa a cikin al’ummar kasar ta New zealand. Wurin bude ido na Maori na daya daga cikin masana’antu ma su bunkasa a cikin kasar New Zealand,mai ba da gudumawa sosai a tsuburin arewa, A Rotorua Za ka iya ziyarar kauyen Maori na musamman ka ci abincin Maori iri-iri, akwai kalar abincin su mai suna (kai), ana dafa (kai) a cikin rami a  daura manyan duwatsu wadda ake kira hangi. Da kuma kallon raye-raye, ziyarar Marae da dai sauran su.

Maori mutane ne ma su dimbin tarihi mai dauke da al’adu da kuma labarai na gargajiya, su na sadar da labarai daga haula zuwa haula ta hanyar tatsuniyoyi da ke ba da labarin kafa tsibirin New zealand  da dai sauransu.

Maraes (wato wurin da mutanen Maori ke haduwa) wuri ne da ke samar da abubuwan da za su ja hankalin al’umma zuwa ga yanayin zamantakewa, addini da kuma al’adar Maori. Marae ya kunshi wharenui (wurin taro) ko a ce dakin taro da kuma wharekai (wurin cin abinci).

Har zuwa yanzu, Mutanen kabilar ta New zealand ‘yan zamani ne su na more kalolin girke-girke na gargajiyar Maori, akwai girkinsu na musamman wanda suke yi wa lakabi da ‘kai’, wannan girki ya sami karbuwa fiye da tunanin mai tunani, su na ji da abincin na su mai su na “kai” sosai da sosai, dangane da abincin na su na kabilar Maori.

Abincin Maori ya kunshi nau’ikan abubuwa daban-daban irin su dangin tsuntsaye da kuma kifi wadda ake kara itatuwa da jijiyoyin jeji. A cikin lambunan su da su ke shuke-shuke na gargajiya, Maori su kan yi shuka na dangin jijiya kamar su dankalin turawa da kuma kumara (dankalin hausa) ko kuma dankali mai zaki, mutanen Maori yawanci su na girki ne a cikin rami ko a ce a karkashin kasa, a cikin tanda da su ke kira hangi (tandar hangi). A wurare ma su zafi kuwa kamar Rotorua, su na amfani da tafasashshen gulbin ninkaya na halitta.

A girkin hangi na al’ada ana dafa nama da ganye ne a cikin ramin da a ka tona a cikin kasa, ana tona ramin sai a saka duwatsu ma su zafi a kasa kafin a daura tandar hangi. Sai a rufe shi da kaya saboda kar tururin ya fita. A bukunkuna ko cin abinci na mussamman, a kan yi wadannan girke-girke na musamman a gidajen cin abinci da wasu otel-otel na cikin kasar.

Mutanen kauyuka da wajen gari kan koyar da  bakin kasar yadda ake yin hangi tandar kasa.

Dankalin Maori (taewa tutaekuri) ya na daya daga cikin abinci ma su muhimmanci a kasar. Sannan akwai biredi (Rewena pararoa) wadda a ke yi da dankali, a na sayar da shi a kasuwannin karshen mako da kuma shagunan biredi na mussamman.

Sanannen mai dafa  abinci mai suna Charles royals mazaunin Rotorua ya na amfani da itatuwan gargajiyan Maori wajen hada kayan yaji da dai sauran su. Itatuwan sun hada da: kuku patties wadda a ke yi da ‘greenlip mussels’ na kasar New zealand, koren ganyen puha, da kuma kifi (salmon) hade da manuka (wata itaciya mai suna ti), zuma, bushashshiyar algae da kuma ganyen horopito mai yaji.Ya fara sayar da busassun hadin gargajiyar ga masana girki kamar sa.

A tsibirin stewart, can nesa da yammacin tsibirin yamma har yau. mutanen Maori su na kiwo tare da kama tsuntsayen da su ke kira ‘Rakiura’. Saboda yana yin maikon sa ya sa ya ke da dandano na musamman.Giyar tohu ita ce giyar asali ta farko da a ka fara yi dan sayarwa makwabtan kasar, a na amfani da inibin da aka girbe daga chan wuraren Gisborne (gabas da tsuburin yamma) da kuma wuraren Marlborough (saman tsuburin kudu). Mutanen yaren Maori da su a ke yin giyar tohu kama daga yi har zuwa kasuwancin.

Mamallakan giyar Maori Tiki da kuma bineyards su kan yi shukar inibinsu karkashin jagorancin dokokin Maori na Kaitiakitanga-wato tsaro da kuma tattalin kasa, giyar Tiki kamar alheri ko a ce maganin saa ce ta Maori.

Aure a al’adar Maori ana danganta shi ne da muhimmancin zuri’a da kuma alaka na yare. A wurin wasu mutanen a na zaben abokanen zama a cikin hapu ko iwi. Su kan yi alkawarin auren ‘ya’yansu tun su na kanana, wasu kuma su kan samo abokanen zaman su kafin su nemi yarda daga wurin manyansu.

Aure daga wajen yare ya na sanya mutum ya rasa albarkar kasa, ko kuma  damarsa na tara amfanin gona ko kuma rashin yarda da kuma rabuwar kai da zarar fada ya tash in kuma aka cika aure daga waje ya kan jawo rabuwar zuri’a bayan fadan da za a dauki makami. Misali hapu ko kiwi kan rabu in aka samu aure daga waje, wato ya zama auren siyasa.

Kabilar Rangatira su ne kadai su ka banbanta a ra’ayin aure, auren matasansu a kan hada shi ne kamar irin yadda malam bahaushe ya ce dai-dai ruwa dai-dai tsaki ko in ce kwarya ta bi kwarya,  matasa maza da mata na manyan mukamai ko yaran ma su manyan mukamai a ke zaba a hada su saboda a samu daidaita da kuma   zumunci tsakanin ma su fada su ji a cikin hapu ko iwi. Misalin wannan akwai waikato maniapoto iwi wadda su kan hada auratayya da ma su fada aji daga tsuburin kudu.

Kyaututtukan aure Wiremu maihi te     Rangikaheke (ta arawa) kamar yadda a ka rubuta a shekara ta alif dubu daya da dari takwas da hamsin da shida, lissafin kyaututtukan da za’a bawa iyayen da su ka bayar da auren diyarsu,yankin filaye guda biyu, manyan rigunan da a ka yi da fatar kare guda biyu, abin adon da a ka yi da koren dutse guda biyu, kwale-kwale guda biyu, dogayen riguna na saka ma su matukar kyau guda biyu, raga guda shida, abin kama tsuntsu guda hudu, kashin kifi whale guda uku, takobin maiti da dai sauransu, wannan dukka gidan maza ke badawa saboda mata ba abin wasa ba ne.

Ku tuna abinci daga kasa ya ke, abincin ruwa daga rariyar ruwa, haka zalika kuma namiji daga mace ya ke, ba wani sharadin auren da ya ba da damar gidan mazan da kuma gidan matan su  hadu a yi ta musayar yawu bisa muhimmancin alakar da za’a kulla. Amma a wajen hapu da whanau haka abin ya ke, wani lokacin Taonga (wato baitil mali) ake badawa daga gidan daya daga cikin ma’auratan zuwa gidan daya, idan Rangatirya za su yi auren hatu ko iwi a kan yi shagali na gani na fada, sannan kuma na ke ce raini.

Tarihin Kafuwar Wasannin ‘Olympics’

Jama’a, ko kun san cewa ranar 23 ga watan Yuni na kowace shekara, ita ce ranar musamman da aka kebe domin tunawa da kafuwar wasannin Olympics na zamani?

Dalilin da ya sa aka kebe wannan rana shi ne domin a daidaita ta da shekarar 1894, lokacin da aka kafa wasannin Olympics na zamani, bisa kwaikwayon asalinsa, wato gasar motsa jiki ta Olympics ta tsohuwar Girka, a birnin Paris na kasar Faransa.

Babban kwamitin shirya gasar Olympics na IOC ya kebe wannan rana a shekarar 1948, tare da burin karfafa wa mutanen duniya gwiwa, su kara shiga a dama da su a harkoki masu alaka da wasannin motsa jiki.

Tarihi game da yadda aka kebe ranar Olympics

Lokacin da aka kaddamar da bikin ranar Olympics a karon farko a shekarar 1894, an samu wasu kasashen da suka halarci bikin da ya gudana, wadanda suka hada da Portugal, Girka, Austria, Canada, Switzerland, Birtaniya, Uruguay, Benezuela, da Belgium. Daga bisani a kowace shekara, kwamitocin Olympics na kasashe da yankuna daban daban, su kan gudanar da bukukuwan taya murna tsakanin ranekun 17 zuwa 24 ga watan Yuni. Mun riga mun ambaci yadda wasu kasashe 9 suka fara shirya irin wannan biki. Zuwa yanzu, adadin kasashen da suke gudanar da irin wannan bukukuwa ya kai fiye da 100.

Sa’an nan a wajen wadannan bukukuwan da ake shiryawa domin tunawa da ranar da aka kafa wasannin Olympics, da kwamitin Olympics, ayyukan da a kan gudanar sun hada da wasannin gudu, wadanda ake kiransu “Olympic Day Run” a Turance.

Bikin “Olympic Day Run”

A shekarar 1987, don neman sanya karin kungiyoyi masu aikin sa kai, su halarci bukukuwan tunawa da kafuwar wasannin Olympics, wani sashi mai kula da aikin yayata wasannin motsa jiki, karkashin kwamitin Olympics ya gabatar da bikin, wanda kowa zai iya halarta na Gudu a ranar Olympics; wato “Olympic Day Run” a bakin Turawa. Don halartar wannan biki, ba a bukatar samun kwarewa a fannin wasannin motsa jiki. Masu lafiyar jiki ko nakasassu, tsoffi ko yara, dukkansu za su iya halarta, domin gudun na da buri daya, wato kayatarwa.

A Gudun ranar Olympics na farko da aka gudanar a shekarar 1987, an shirya yin gudun nisan da ya kai kilomita 10, inda aka samu kasashe 45 da suka gudanar da irin wannan biki. Zuwa shekarar 2006, wasu kasashe 161 sun gudanar da bikin Gudun ranar Olympics. Zuwa yanzu bikin da ya kan gudana tsakanin ranekun 17 zuwa 24 ga watan Yuni, ya shafi gudun tsawon kilomita 1.5, da na kilomita 5, da kuma na kilomita 10.

An kasa gudun zuwa iri daban daban ne don biyan bukatun mutane iri-iri, don sanya karin jama’a su halarci wannan biki, tare da samun karin damammakin yayata ruhi na Olympics.

Hukuma mai kula da bukukuwan ranar Olympics

Hukuma mai kula da bukukuwan da ake gudanarwa a ranar Olympics, gami da wasannin Olympics da ake gudanarwa a duk shekaru biyu-biyu, inda ake sauyawa tsakanin wasannin lokacin zafi da na lokacin hunturu, ita ce kwamitin Olympics ta kasa da kasa, wato IOC. An kafa wannan kwamiti a shekarar 1894, wanda ke da hedkwatarsa a birnin Paris na kasar Faransa. Bayan da babban yakin duniya na farko ya barke a shekarar 1914, an dauke hedkwatar kwamitin IOC zuwa birnin Lausanne na kasar Switzerland, ganin yadda kasar take da matsayin ‘yar “ba-ruwana”, wato ba za ta shiga cikin yakin duniya ba kwata kwata.

Zuwa yanzu, idan an isa birnin, za a iya ganin wurin ajiye kayayyakin tarihi masu alaka da wasannin Olympics, da cibiyar nazarin wasannin Olympics, gami da wasu tituna da dakunan motsa jiki, da aka sanya musu take da sunan Pierre de Coubertin, mutumin da ya samar da gudunmowa sosai ga kokarin kafa wasannin Olympics na zamani.

Pierre de Coubertin, “Mahaifin” wasannin Olympics

An haifi Pierre de Coubertin a shekarar 1863 a kasar Faransa. Dukkan iyayensa na da matsayi na sarakai. Kuma babansa wani shahararren mai fasahar zane-zane ne. Saboda muhallin mai kyau da iyayensa suka ba shi, Pierre ya samu isassun damammaki wajen koyon ilimi da fasahohin al’adu. Tun yana karami ya iya zane-zane, da sarrafa kayan kida na Piano, ban da haka kuma, yana sha’awar wasan tseren doki, da tseren kwale-kwale, da wasan takobi, da na dambe, da dai sauransu. Sa’an nan a makaranta, ya nuna sha’awa sosai kan al’adun tsohuwar Girka, inda aka taba gudanar da wasannin Olympics na gargajiya a can baya. Sa’an nan ya tafi kasar Birtaniya domin koyon karin ilimi a fannin aikin koyarwa, inda ya karbi ra’ayin wani shehun malami na kasar Birtaniya mai suna Thomas Arnold, wanda ya mai da hankali matuka kan sanya matasa su shiga cikin wasannin motsa jiki. A ganin Thomas Arnold, wasan motsa jiki na baiwa matasa damar daidaita halayyarsu, da koyon ilimi da kansu. Daga nan Pierre de Coubertin ya fara nazarin tsarin da Birtaniya ta dauka a fannin hada aikin koyar da ilimi, da wasannin motsa jiki a cikin makaranta. Haka kuma ya nuna fatan ganin kasar Faransa ita ma ta dauki wannan tsari, domin kyautata lafiyar jikin dalibai, da sanya su zama mutane masu karfin zuciya, wadanda suke iya jure wahala.

Bayan da ya koma kasar Faransa, ya rubuta littattafai da yawa don yayata tsarin koyar da ilimi mai ci gaba na kasar Birtaniya, da neman raya wasannin motsa jiki a kasar Faransa.

Daga bisani, masu nazarin tarihi na kasashen Turai sun yi ta gano wasu kayayyakin tarihi masu alaka da tsoffin wasannin Olympics a kasar Girka, tsakanin shekarun 1875 zuwa 1881. Wannan batu dai ya janyo hankalin Pierre de Coubertin sosai. Da ma ya yi ayyuka da yawa wajen neman raya wasannin motsa jiki, amma daga nan ya fara yin kira da a farfado da wasannin Olympics, domin a ganinsa ta hanyar yayata ruhun Olympics ne za a iya samun damar raya wasannin motsa jiki a kasashe daban daban. Daga bisani, a shekarar 1892, shi Coubertin ya yi wani jawabi, inda a karon farko ya gabatar da ra’ayinsa na “farfado da wasannin Olympics”. Bisa kiran da ya yi, an bude wani taron wasannin motsa jiki na kasa da kasa a birnin Paris a shekarar 1894, inda aka yanke shawarar kaddamar da wasannin Olympics na zamani na farko a kasar Girka, wanda za a dinga gudanar da shi duk shekaru hudu-hudu. Sa’an nan a ranar 23 ga watan Yuni na shekarar 1894, aka kafa kwamitin Olympics na kasa da kasa, inda Pierre de Coubertin ya zama babban sakataren kwamitin. Irin gudunmowar da Pierre de Coubertin ya samar, a kokarin kafa wasannin Olympics na zamani, ya sa ake kiransa da lakabin “mahaifin wasannin Olympics na zamani”. Akwai wasu maganganun da ya yi wadanda suka yadu a tsakanin jama’a sosai. Ga misali, “Halarta ya fi samun nasara muhimmanci”, da “wasan motsa jiki ya yi daidai da zaman lafiya”, da dai sauransu.

Ruhin Olympics

“Ruhin Olympics” take ne na wani jawabin da Pierre de Coubertin ya yi a shekarar 1919, a bikin taya murnar cika shekaru 25 da farfado da wasannin Olympics. Inda Coubertin ya bayyana bambancin dake tsakanin ruhin Olympics da na sauran wasanni. A ganinsa, wasanni suna kayatar da mutane, amma wasannin Olympics sun sa an samu kayatarwa, gami da alfahari. Cikin jawabinsa, Coubertin ya bayyana dalilin da ya sa ya yi kokarin neman farfado da wasannin Olympics, wanda shi ne burinsa na daidaita tsarin koyar da ilimi a cikin makarantu. A cewarsa, ba ya jin dadin tsoffin hanyoyin da ake bi wajen koyar da ilimi ga matasa, inda ake yi musu matsin lamba sosai, da rashin daidaito bisa fasahohin da ake horar musu. Ya ce ya taba nazarin wasannin Olympics na gargajiya. A ganinsa, jama’ar Girka ta baya sun gudanar da gasar wasannin motsa jiki ne, ba domin kyautata lafiyar jikin mutum, da kayatar da masu kallo kawai ba. Abin da ya fi muhimmanci da suke lura da shi, shi ne aikin tarbiya. A cewar Coubertin, makasudin gudanar da wasannin Olympics na gargajiya, shi ne neman daidaita halayyar matasa ta hanyar wasannin motsa jiki. Wannan makasudi ya dace da ra’ayin Coubertin game da wasan motsa jiki.

Game da dabarun da za a iya bi domin mayar da ruhin Olympics ya zama gaskiya, Coubertin ya ce abin da ya fi muhimmanci shi ne sanya kowa ya iya shiga a dama da shi. Ko wane mutum wanda ba shi da matsayi, shi ma ya kamata a ba shi damar jin dadin motsa jiki. A ganinsa, duk da cewa wasannin Olympics sun shafi gasa da takara, amma ainihin makasudin wasannin shi ne sanya ‘yan Adam samun damar kyautata lafiyar jiki, da halayyarsu, maimakon samun lambar yabo kawai.

Sai dai mene ne ma’anar tushe ta ruhin Olympics? A cewar Coubertin, ma’anar ruhin ita ce: a koyi darasi daga tarihin bil Adama, sa’an nan a yi kokarin samar da makoma mai kyau a nan gaba. Bisa wannan ruhi, in ji Coubertin, za a iya taimakawa samun zaman lafiya, da daidaito, da kuma baiwa matasa karin damammakin samun ilimi.

(Bello Wang, ma’aikacin sashen Hausa na CRI)

Me Ya Sa Ake Alakanta Mata Da Gulma?

Mece ce gulma?

Gulma ita ce a fadi aibun wani alhali ba ya wajen, idan an gan ta ko an hango wani na ta sai a yi shiru ko a yi sauri a kwalmada hirar yadda ba za ta gane da da ita ake yi ba.

 

Me ya ya ke haddasa gulma?

Bai wuce hassada ba da rashin ilmi uwa uba da rashin abin yi, domin idan zaman banza ya yi yawa ya kan jawo mutum ya yi ta maganganu mararsa kan gado.

 

Su waye su ka fi aikata gulma?

Tabbas an yiwa mata shaida akan sun fi kowa gulma da tsegumi watakila sabo da su ba sa fita aiki ne kuma watakila ba su da sana’ar da za ta dauke mu su hankali daga sakawa sauran mata ido.

 

Mene alfanun yin gulma?

Amfanin gulma bai wuce ki fada ki ji dadi a ranki ba kuma ki farantawa makiyan wanda ku ka yiwa gulmar rai, domin ita gulma ba alkhairi n mutumin ake fada ba mummunan aiki ko kaddarar da ta sami wacce ake gulmar ake yayatawa. Yara su na da son jin labarai za ki ga kamar ba sa gane abubuwan da uwa take fada saboda wasa ya dauke mu su hankali amma sarai su na ganewa. Wasu yaran ma su kan labe su na sauraron abinda ake fada. Su kan je su ba wa abokansu yara labari ko kuma su je su feasawa wacce aka yi gulmar a kanta ba tare da sun yi wayon sanin uwarsu su ka tonawa asiri ba.

 

Mene aibun yin gulma?

Aibunta ya fi komai yawa saboda gaba daya ma  gulma aibu gare ta bata da alkhairi ko guda daya, a duniyarmu da ma a lahira saboda haramun ne sannan Allah ba Ya yafe wa wani laifin wani har sai kin je kin nemi gafara a wajen wacce ki ka zalumta kuma ki fadi abin da ki ka ce a kanta wanda abu ne mai matukar wuya ki iya yin hakan.

 

Shin wannan dabi’ar ta gulma ta na raguwa ne ko karuwa take yi a cikin al’umma?

Gulma kara karuwa take yi musamman yadda yanar gizo-gizo (social media) ta yi tasiri a zamanin nan namu. Idan ada gulmarki bata wuce ki fesawa ‘yan gidanku ba  idan ta yi yawa ki shiga makwabta amma a yanzu cikin mintina kadan za ki iya kiran mutane goma a waya ki fesa musu labarai. Mutanen da su ke wata unguwa nesa da ke ko kuma wani gari koma wata kasar mai nisa  Idan ba ki da kudin kira ko kuma ki na kusa da wacce gulmar ta shafa ba sai kin yi magana ta ji ki ba, ga hannyoyin rubuata sako ki tura a tare a baki amsa a take ba tare da kowa ya ji ba, daga ku sai ubangijinku.

 

Ina mafita?

Mafita daya ita ce mata mu fita mu nemi ilmi musamman na addini, bayan mun samo ilmin sai kuma mu yi amfani da shi mu kori shaidan wanda ya ke yi mana wasi-wasi a cikin zukatanmu. Mu ki yarda mu yi ko da ya na kawata mana a ranmu. Domin muddin ki ka saba da gulma ta zama jikinki idan ba ki yi ba za ki taba jin dadi ba. Sannu a hankali za ta zama sana’arki alhali ke ba albashi zaa ba ki ba sai ma dai idan aka gano ki sunanki ya baci, mutuncin ki ya zube kuma kowa zai iya tasowa ya zo har gidanki ya fada mi ki bakar magana a gaban yaranki wadanda su ma za su daina ganin mutuncinki.

Gulma ta na rusa tarbiyyar da ki ka dade ki na bawa yaranki, dabi’un uwa kacokan yara su ke kwaikwaya, za a kai lokacin da ba ki da bakin da za ki yi musu fada akan su daina gulma. Muddun ki na yin sana’a ko aiki za a sami rangwamen zaman banza, hankalinki zai tafi kan abin da ki ka saka a gaba. Ko da ya ke wasu gulmammakin ma a wajen aiki ko a wajen sana’a a ke hado su.

Gulma ta na da dadin fada a baki, ga ta da gardin sauraro amma ta na da matukar daci idan mu ka jiyo an yi gulma akanmu mu ma. Tunda ba kya so a yi da ke to ke ma ki daina yi da wata, sabo da yadda ki ka ji ba dadi haka ita ma wacce ki ka sakawa ido ta ke ji. Mu so juna saboda Allah, mu taimaki juna , mu kira ta mu fada mata gaskiya komai dacinta idan ma wani abu ta ke yi marar kyau, sai mu ba ta shawara. A cire kyashi da hassada ga mutanen da su ka fi mu ci gaba a rayuwa.

Advertisement
Click to comment

labarai