Connect with us

TATTAUNAWA

Mace Za Ta Iya Tallafa Wa Al’umma Fiye Da Namiji Idan… – Fatima Abubakar

Published

on

Kiraye-kirayen da mata ke yi na a dan buda musu a ba su sarari wajen jan ragamar madafun iko sun wuce shurin masaki. Duk da cewa ana samun cigaba kadan-kadan wajen nada su a mukamai daban-daban na matakin mulki da sauran sassan gudanarwa amma har yanzu suna ganin akwai bukatar kara sake musu linzami. Bakuwar Shafin Mata Adon Gari ta wannan makon ta warware zare da abawa kan dalilan da take ganin idan har aka sakar wa mata mara kamar yadda ya kamata; za su himmatu wajen inganta rayuwar al’umma fiye da yadda maza suke yi. Ko shin wane dalilai ne wadannan? Ku karanta hirar ku ji su da ma sauran wasu abubuwa da suka shafi musamman mata da matasa da bakuwar ta bayyana game da tallafin da suke yi wa mata masu neman taimako da matasa da yara ta fuskar ilimi. Wakazalika, ta yi wa mata masu zaman dirshan ba su yin sana’ar komai allura domin su fahimci zamanin da suke ciki su kama sana’ar da za ta taimake su ta taimaki iyalansu a maimakon zaman jiran miji ya yi komai da komai.

Masu karatu na so su ji sunan ki da takaitaccen tarihin rayuwar ki….

Sunana Fatima Abubakar Kadashi. Wasu na ce min Ladidi ko Zarah. Amma yawunci Kadashious suke ce min don sunan shagona kenan da kamfani. Ni ‘yar asalin Jihar Kaduna ce. Na yi aiki da Hukumar Zabe ta Jihar Kaduna. Na yi aure kuma ina (Kadashious Collections). Sannan ni ne Manajan Darakta na Kamfanin Yusfat Multimedia Limited. A halin yanzu kuma cikin yardar Allah na shiga siyasa, ina takarar kujerar Majalisar Dokokin Jihar Kaduna a Mazabar Unguwar Sunusi/Badikko. Wannan shi ne a takaice.

 

Mene ne ya ja ra’ayinki kika shiga harkar siyasa a matsayinki ta mace?

 

Akwai abubuwa da yawa. Da farko sai in ce na yi gado wajen Babana. Kuma na yi aiki wajen zabe a Hukumar Zabe ta Kaduna. Na samu ra’ayin siyasa ne lokacin da aka kafa kungiyar tsofaffin dalibai na makarantarmu wanda ina cikin kwamitin gyaran makaranta. Mun je ziyara wajen wani dan majilisar don neman  taimako gyaran toilet (makewayi) na makaranta amma ba mu samu biyan bukata ba. Kuma a mazabarmu akwai mata da matasa da yawa wanda ba su aikin komai. Sai na fara ganin ai nima ina iya fitowa neman wannan kujera, inda na hango da gyaran da yarda Allah da nufinsa in taimaka. Ina da kungiya mai zaman kanta (NGO) kuma ina cikin wasu, muna yin aiki daidai gwargwado.  Bisa basirar da Allah ya yi mun, ina da burin tabbatar da ganin mata da matasa sun ci ribar dimukuradiyya ta hanyar karfafa su da ba su tallafin karatu, insha Allahu.

 

Baya ga taimakon mata da gyaran makarantu, akwai wani abin da kika kara hangowa ne da ya ke bukatar gyara a cikin al’umma wanda sauran ‘yan siyasa ba sub a da kulawa a kai?

 

E to, zan ce mu mata an bar mu a baya, bayan kashi 35 a cikin 100 da aka ba mu ko kashi 10 bisa 100 ba mu yi amfani da shi, kuma in ba muna cikin gwamnati ba ba za mu iya yin komai game da gyaran ko kara kimar mata da matasa ba ko a san damuwarmu.  Ya kamata a ce a yanzu duk inda mace ta fito neman wani abu to ya zamana maza sun ba ta goyon baya don mu ma a gn iya gudunmu, na tabbata mace sai ta tallafa fiye da namiji domin mata muna da tausayi da kulawa.

 

 

Kin ce kina da kungiya mai zaman kanta, me da me kike yi a karkashinta?

 

Muna abubuwa da ya shafi mata da matasa har marayu. Tallafawa wajen kudin makaranta ko sana’a amma ba kudi muke bayarwa ba. Muna siyen kayan sana’a ne mu bayar bayan ka gama koyan sana’ar. Kudin makaranta kuma muna zuwa ne mu biya da kanmu don gudun kar a ki biya ma yaro. Kuma kafin na fara tawa kungiyar sai da na duba na ga ko akwai wata kungiya da ta ke mara wa mata a kan siyasa. Sai na ga akwai amma yawanci a matki ne na jiha, shine na neman izini daga hukumar kula da rajistar mallaka na bude kungiyar da za ta zama jagorar mata a siyasa. Insha Allah nan ba da dadewa ba zan amsa takardar shaidar rajistar da na yi din.  Amma a yanzu ina cikin kungiyoyi masu karfi kamar uku zuwa hudu.

 

Yanzu misali idan wata tana da matsala za ta iya zuwa ta kai miki kukanta kai tsaye, ko akwai wasu hanyoyi da dole sai ta bi kafin ku taimake ta?

Akwai sakatariya da take amsar duk abin da aka kawo. Kuma sai mun bincika. Wasila yanzu jama’a sai a hankali, muna bin komai a hankali ne.

 

Me za ki fi ba wa karfi idan kin samu nasara a zabe?

Insha Allah mata da matasa su ne abun dubawa domin su ne zabe. Tun safe za ki ga mace ta bar gida don ta jefa kuri’a amma kuma su ne ba a damu da matsalolinsu ba.

 

Wani kira za ki yi ga mata masu zaman jiran a basu?

 

Wannan lokacin ya wuce, mace ta tsaya tana zaman jira. Ya kamata ta tashi tsaye wajen neman halal don biyan bukatar kanta da iyalai, ba sai kin jira miji ba. Ina kira ga mata cewa zaman dirshan ba tare da yin sana’a ba; ba naku ba ne. Ku yi kokarin yin sana’a za ku samu nasara.

 

Ko akwai wani tanadi da kika kudurce a kan mata da matasa nan gaba?

 

Allah ya kai mu lokacin, domin komai sai da nufinsa. Insha Allah za su yi alfahari. Kuma ina kara kira ga matasa da mata cewa neman halal wajibi ne wajen mu domin kare mutunci da matsololin yau da kullulm. Mai nema ba ya rasawa.

 

Kin ce a gun sakatariya ake neman izinin ganinki don samun tallafi, ta yaya za a iya samun sakatariyar?

 

A gun sakatare a ke kai takarda amma ganina ai kowa na iya ganina donmin ni ta jama’a ce.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!