Yaki Da Handamar Kudi: Jigajigan ‘Yan Siyasar Da Gwamnatin Buhari Ta Garkame A Kurku — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

Yaki Da Handamar Kudi: Jigajigan ‘Yan Siyasar Da Gwamnatin Buhari Ta Garkame A Kurku

Published

on


A Shekarar 2015, gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi manyan alkawura uku na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa da maido da martabar tattalin arzikin kasa da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

Bayan shekaru uku, an garkame jigogin ‘yan siyasa a gidan kaso, inda hakan ya nuna a zahiri, alkawarin da gwamnatin ta dauka na yaki da cin hanci da rashawa ya fara zama dahir, inda aka yanke wa wasu ‘yan siyasar hukuncin zaman gidan kaso har da tsofaffin gwamnoni da tsofaffin ministoci da manyan jigogin ‘yan siyasa. Wasu daga cikin wadanda aka dauren sun samu alfamar zama tare da iyalansu a wasu lokuta, wasu kuma haka aka bar su suna wuri-wuri da ido.

Misalin wadanda suka zauna da iyalinsu a gidan yarin shi ne tsohon Gwamnan Jigawa, Alhaji Sule Lamido wanda aka garkame a gidan yari na Kurmawa da ke Kano tare da ‘ya’yansa na cikinsa su biyu. Galibin wadanda aka taba garkame a gidan yarin in baya ga wasu ‘yan majalisun dokoki na kasa, an gurfanar da su a gaban kuliya ne saboda tafka almundaha a karkashin gwamnatin da ta gabata. Biyu daga cikin wadanda aka dauren dama can suna fuskantar shari’a a gaban kotu tun kafin hawa karagar wannan gwamnatin. Baya ga wadanda aka tasa keyarsu zuwa gidan yarin, har ila yau akwai wasu da ke gudun hijira bisa radin kansu domin yin ‘yar zulliya ga hukumomin da ke yaki da cin hanci da rashawa da zambar kudi.

Wadanda suke ‘yar zulliyar sun hada da tsohon shugaban PDP, Alhaji Adamu Mu’azu, da tshohuwar minister mai, Diezani Alison-Madueke da kuma tsohuwar shugabar Hukumar Kulda Filayen Abuja, Hajiya Jamila Tangaza.

A nan ga jeren sunayen manyan ‘yan siyasa wadanda aka tasa keyarsu zuwa gidan Yari a karkashin gwamnatin Shugaba Buhari kamar yadda muka samo muku daga Jaridar Daily Trust.

Tsohon Gwamnan Kaduna Ramalan Yero:

Kwanan baya aka tura shi gidan Yari na Jihar Kaduna, inda ya zauna a gidan Yarin daga ranar 31 na watan Mayu zuwa 6 ga watan Yunin 2018, tare da tsohon shugaban PDP na jihar Abubakar Gaya-Haruna da tsohon Sakataren Gwamnatin jaha Hamza Ishak da tsohon karamin ministan wuta Nuhu Somo Wya. Hukumar EFCC ce ta gurfanar dasu a gaban Kotu a bisa zargin badakalar kudi.

 

Tsohon Gwamnan Filato Jonah Jang:

Shima an tura shi gidan Yari dake garin Jos, inda ya yi kwana takwas. Jang wanda zababben Sanata ne mai ci, mai wakiltar mazabar Filato ta Arewa. A yanzu haka, Jang yana fuskantar tuhuma sha biyu ta badakalar naira

biliyan 6.3 tare da wani tsohon kashiya  dake aiki a ofishin tsohon Sakataren gwmnatin jihar Yusuf Pam, Jang ya kuma ansa laifin sa. Albarkacin shigar Jang gidan yarin na Jos aka maido da hasken lantarki a gidan wanda a baya an dan jima daurarrun gidan suna zama a cikin duhu dimdin!

 

Tsohon Gwamnan Jihar Adamawa Bala James Ngilari:

Shine na farko da wannan gwamnatin ta fara yankewa hukuncin zaman gidan Yari a cikin watan Maris ddin  2017. An yanke masa hukunci ne saboda gazawar samar da dokar jaha da kuma aikata munafunci, ya kuma amsa laifin sa aka kuma kulle shi shekara biyar a gidan Yari.

 

Tsohon Gwamnan Taraba Rabaran Jolly Nyame:

An yanke masa hukuncin zaman gidan Yari na shekaru sha hudu saboda badakalar kudi. Alkalin babbar Kotu dake Gudu cikin Abuja mai shari’a Adebukola Banjoko ne ya yanke masa hukunci saboda zambar kudi har naira biliyan 1.64 bayan da hukumar EFCC ta shigar da kara.

 

Sanata Peter Nwaoboshi:

Shi ma an tura shi gidan Yari na Kirikiri inda ya shafe awowi arba’in da takwas. Peter Nwaoboshi wanda a yanzu yake wakiltar mazabar sa ta Delta ta Arewa a karkashin inuwar jamiyyar sa ta PDP, ana zargin sa ne da badakalar  sama da naira miliyan 805 kuma EFCC ce ta gurfanar dashi a gaban kutun mai shari’a Alkali  Mohammed Idris a bisa tuhuma guda biyu da kuma safarar haramtattun kudi, amma daga baya an bayar da belin sa.

 

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamido:

A cikin watan Yulin 2015 Gwamnatin Shugaba Buhari ta tura Lamido shida ‘yayan sa biyu Aminu da Mustapha tura su ajiya a gidan Yari na Kurmawa a bisa zargin safarar kudi har naira biliyan 1.351, har ila yau Lamido yana daya daga cikin masu neman kujerar Shugaba Buhari a 2019.

 

Tsohon Kakakin PDP Na Kasa Oliseh Metuh:

Hukumar EFCC ce ta gurfanar dashi a gaban Kutu a bisa zargin karbar naira miliyan 400 daga gun tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara akan fannin tsaro Sambo Dasuki, kudin da aka yi amannar suna daga cikin kudin sayen makamai dala 2.1 a lokacin tsohuwar ggwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan,inda har yau ake tsare dashi a gidan Yari na Kuje dake Abuja.

 

Tshon Ministan Abuja Bala Mohammed:

Bala da dansa an hulle su a gidan Yari na Kuje dake Abuja shida dansa Shamsudeen, a bisa zargin badakalar kudi. Hukumar EFCC ta gurfanar da Bala akan tuhuma shida data hada da badakalar naira miliyan 864 da bayar da bayanan karya akan kaddarar sa, inda kuma dansa aka gurfanar dashi akan tuhuma sha biyar da suka hada da safarar kudi ta haramtacciyar hanya.

 

Tsohon Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara Kan Harkar Tsaro, Kanal Sambo Dasuki Mai Ritaya:

A yanzu haka ya shafe has watanni talatin da daya a gidan Yari a bisa zargin badakalar dala biliyan 2.1 na sayen makamai.Mafi yawancin manyan da ake tuhuma akan cin hanci da rashawa, sun auka ne a cikin gadar zaren da Dasuki ya jefa su ta hanyar basu kudin na makamai. Wasu daga ciki da suka zurma sun hada da tsohon gwamnan Sokoto Attahiru  Bafarawa da tsohon gwamnan jahar Kano  Ibrahim Shekarau da shugaban gidan talabijin na AIT Raymond Dokpesi da tsohon shugaban PDP na kasa Bello Haliru da dan sa da Musiliu Obanikoro da kuma dansa.

 

Tsohon Gwamnan Neja Babangida Aliyu:

Hukumar ta rike shi a bisa zargin cin hanci da rashawa da safarar haramtattun kudi da suka kai naira biliyan biyu.

 

Tsohon Ministan Sufuri Fani-Kayode:

Shi ma yana a cikin wannan jerin, inda aka kulle shi a gidan Yari na Ikoyi.

 

Tsohuwar Ministar Kudi Nenadi Esther Usman:

Itama tana daga cikin wannan sahun  wadda a cikin watan Yuni na shekarar 2016 aka tura ta gidan Yari na Ikoyi, inda Femi Fani-Kayode aka kai shi gidan kirikiri na Legas duk a rana daya, bayan an gurfanar dasu a gaban Kotun dake jahar Legas a bisa zargin badakalar naira biliyan 4.9. Fani da Nenadi dukkan su EFCC ce ta gurfanar dasu ne a gaban Kotun mai shari’a Alkali Sule Hassan a bisa tuhuma sha bakwai.

 

Tsohon Gwamnan Filato Joshua Chibi Dariye:

A yanzu haka zababben sanata ne daga jahar Filato an kuma yanke masa hukuncin zaman gidan Yari na shekaru sha hudu. Dariye wanda yake wakilrtar mazabar sa ta Filato ta tsakiya a karkashin tutar jamiyyar sa ta APC, an yanke masa hukuncin ne a ranar 12 na watan Yuni a bisa cin amana da kuma badakalar kudi har naira biliyan 1.16. Alkalin babbar Kotun dake Abuja mai shari’a Adebukola Banjoko ne ya yanke masa hukuncin kuma shine dan jamiyyar APC mai mulki da aka yankewa hukunci akan tuhuma takwas.

Advertisement
Click to comment

labarai