Kofin Duniya: Messi Yana Cikin Wani Hali — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Kofin Duniya: Messi Yana Cikin Wani Hali

Published

on


Daya daga cikin fitattun ‘yan wasan kwallon kafa na duniya na fuskantar kalubalen ficewa daga gasar cin kofin duniya da ake yi a Rasha.

Lionel Messi na Argentina, wanda ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya sau biyar, ya jagoranci kasarsa a wasa na biyu na rukunin D da  suka kara da kasar Croatia.

Sun shiga wasanne da matsin lamba ganin cewa sun tashi canjaras ne kawai a wasansu na farko da Iceland hakan ya sa Argentina samun maki daya, yayin da Croatia ta doke Nijeriya da ci 2-0, abin da ya ba ta maki uku, kuma ta kasance jagora a rukunin.

Messi, wanda ya lashe gasar cin kofin Zarakun Turai sau hudu da Barcelona, da kofunan La Liga da sauran kofuna da dama a matakin kulob, bai taba cin wani muhimmin kofi da tawagar kasarsa ba.

Kuma wasu na ganin wannan ce gasar kofin duniya ta karshe da gwarzon dan kwallon zai taka a rayuwarsa saboda sai nan da shekara hudu sannan za a sake buga wata sabuwar gasar.

Musamman ganin cewa ya taba sanar da yin ritaya daga bugawa Argentina kwallo a baya, kafin daga bisani ya sauya shawara bayan an bashi shawara daya dawo domin kasar tana bukatarsa.

Messi zai so ya nuna kansa kuma ya fitar da kasarsa kunya, musamman ganin yadda ya zubar da fanareti a wasansu da Iceland sannan kuma ya yi rashin nasara a kan Crotia.

Bugu da kari ganin yadda babban abokin hamayyarsa Cristiano Ronaldo ya ke haskakawa a gasar, inda kawo yanzu ya ci kwallo hudu a wasa biyu.

Wasu dai na ganin Messi zai yi kukan-kura a wasan Nijeriya domin ceto Argentina daga barazanar da ta ke fuskanta na ficewa daga gasar.

Sai dai a gefe guda wasu na ganin cewa zai yi wuya, kuma ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare, musamman ganin yadda ita ma Nijeriya ba kanwar lasa ba ce kuma.

 

Advertisement
Click to comment

labarai