Connect with us

RA'AYINMU

Lokacin Dakile Satar Danyan Mai Ya Yi

Published

on

A kwanakin baya kadan ne wasu gungun matasa da suka fito daga yankin nan mai arzikin man fetur na Neja Delta, suka dirka a shalkwatar tsaro ta kasar nan da ke Abuja, inda suke neman da a sauke Kwamandan runduna ta musamman da ke yankin na su, Riya Admiral Apochi Suleiman, daga jagorancin rundunar ta, ‘Operation Delta Safe,’ da ke yankin na Neja Delta. Matasan sun zargi kwamandan ne da karfafa ayyukan satar man na fetur, ta hanyar zargin da suka yi masa na samar wa da barayin man kananan Jiragen ruwan da suke jigilar man da suka sata da su, da ma sauran ababen bukatun barayin man da ke yankin na su.
‘Yan ta’adda sun jima suna amfana daga kudaden da suke samu ta hanyar satar man na fetur, tun ma kafin gwamnatin tarayya ta fara aiwatar da shirin nan na yin afuwa. Inda aka yi ta samun rahotannin satar man har ma da rahotannin da suke nuni da kafa wasu kananan matatun man na boye da ‘yan ta’addan kan yi a yankunan na Neja Delta. ‘Yan Nijeriya sun yi zaton samar da wannan shirin na yin afuwa da kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na tsunduma matasan yankin na Neja Delta cikin wasu sassan ayyukan da suka shafi tattalin arziki, ta hanyar ba su horo da koya masu sana’o’i da sauran aikace-aikace, wadancan munanan ayyukan na su na karya tattalin arzikin za su zo karshe kenan.
Amma sai lamarin ya kasance kuma sam ba hakan ne ba, har gobe dai matsalar satar man tana nan sai ma dada habaka take ta yi. A wani rahoto da rundunar Sojin ruwa ta fitar, ya nuna cewa, kasar nan tana asarar dala bilyan 20 a duk shekara. A shekarar 2013 kadai, barayin na mai sun saci kimanin gangar mai 55,210 a kowace rana, wanda jimillansa a wata guda ya kai kimanin ganga 1,656, 281. Hakanan ma, cibiyar samar da zaman lafiya ta kasar Amurka a rahoton ta na shekarar 2009, ta bayyana cewa, barayin man na kasar nan da ke yankunan na Neja Delta, suna satan tsakanin gangar mai 30,000 zuwa 300,000 a kowace rana.
A cewar rahoton, an yi asarar kimanin dala bilyan 100 ta hanyar satan man a tsakanin shekarun 2003 zuwa 2008. Makudan kudade ne suke fadawa hannun ‘yan ta’addan da kuma wasu iyayen gijinsu, wadanda aka tabbatar da mafiya yawan kudaden suna amfani da sune wajen saye da tara makaman da za su ci gaba da aikata mummunar sana’ar ta su, duk da barazanar da hakan ke yi ga sha’anin tsaron kasar nan.
Lamarin yana kara daurewa LEADERSHIP JUMA’A kai, me ke dalilin da ya sanya yaki da barayin man ya zama matsalar da ta gagara korewa ne, duk da tsunduma Sojojin Nijeriya a cikin yakin? Abin damuwa ne matuka, irin dimbin asarar da kasar nan ke tafkawa sakamakon ayyukan barayin man, wani kamfanin samar da man na ‘yan kasa, yana jagorantar kiran da a kara samar da tsaro da kula ta musamman a kan ayyukan barayin man. Kamfanin ya nuna matukar damuwarsa ne kan yadda ake keta haddin tsaro a sassan yankunan, mashigar Nembe, wata babbar mashiga ce ta fitar da man wacce ta nan ne lamarin na masu satar man ya fi kamari. Kamfanin na NCTL, kadara ce da kamfanin mai na kasa, NNPC, da kuma kamfanin Aiteo wanda ke mallakin kashi 45, gwamnatin tarayya kuma ke mallakan kashi 55.
Akwai manyan kamfanonin da suke zuba danyan man na su tare da fitar da shi ta wannan kamfani na NCTL. Don haka rufe mahimmin waje kamar wannan sabili da munanan ayyukan na barayin mai, yana tattare da babbar asarar da ba ma za a iya kintatawa ba, ga kamfanonin da kuma tattalin arzikin Nijeriya. Ba sai an fada ba, satar man da ake tafkawa ba kakkautawa yana matukar barazana ne ga dorewar tattalin arzikin kasar nan. Sai dai muna nuni da cewa, sashen mashigar Igbomorotu na kudancin yankin Ijaw, da kuma sashen Akasa na kan yankin Brass, sun ci gaba da kasancewa wata babbar matattara na wannan muguwar sana’ar ta barayin na mai, wadanda aka ce tuni sun mamaye yankunan. Sam ba mu ga dalilin da zai sanya a kasa dirar wa barayin man da ke yankunan ba, duk da kasancewar jami’an tsaro a sassan. Wannan abin bakin ciki ne, a namu ra’ayin, Nijeriya ce kadai kasar da duk da dimbin arzikinta na mai, sannan kuma ba wai tana cikin yaki ne da wata kasa ba, amma kuma ayyukan barayin mai sun dabaibaye ta.
Ya fa zama tilas ga gwamnati da ta sake fasalin jami’an tsaronta da ke aiki a wadannan sassan, a kuma fara ne da samar da canji a shugabancin rundunar ta STF, a kuma binciki ko da gaske ne akwai wata shaidar da za ta nuna hadin baki kamar yadda al’umman yankin suke zargi. Sannan kuma, ya kamata shugabannin rundunonin na Soji su duba yiwuwar samar da canji a kan lokaci ga dukkanin tawagar da suke aiki a wadannan sassan domin gujewa yiwuwar samun wata kafa ta hada baki a tsakanin barayiin man da jami’an tsaron. Amma abin da ma ya fi mahimmanci shi ne, muna ganin ya kamata gwamnati ta dauki matakin zakulo iyayengijin barayin man. Bisa la’akari da dimbin asarar da ake tafkawa, akwai bukatar zuba jari mai yawa wajen takaita ayyukan na ‘yan’addan, hakan kuma ba zai yi wani tasiri ba, matukar za a bar iyayengijin na su suna ta watayawa ba tare da sun shiga komar hukuma ba. A gaskiya sune ma ya wajaba a ce an kama tare da hukunta su. Wanda yin hakan zai zama jan kunni ga na baya ya kuma rage aukuwar sace-sacen na mai matukar gaske, kila ma bakidaya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!