Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

An Kama Shugaban Kwalejin Kimiyya Da Fasaha Da Takardar Shaidar Karatun Bogi

Published

on

Hukumar binciken ayyukan cuwa-cuwa da makamantansu ta ICPC, ta ce ta kama wani shugaban kwalejin kimiyya da fasaha bisa tuhumarsa da mallakan takardar shaidar kammala karatun digirin digir-gir, ta bogi.
Kakakin hukumar ce, Uwargida Rasheedat Okoduwa, ta bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Litinin.
Okoduwa, ta bayyana mutumin da suna, Olaolu Olugbenga, shugaban kwalejin kimiyya da fasaha ta Igbajo, Jihar Osun, wanda a baya shi ne, tsohon mataimakin shugaban Jami’ar Oduduwa a Ogun.
Ta ce, binciken farko da hukumar ta gabatar kan koken da aka kai mata, ya nu na Olugbenga, tabbas yana yin aiki ne da takardar shaidar karatun farfesan da ake da shakku a kanta, wanda yake ikirarin ya samu ne daga Jami’ar Ibadan.
A lokacin da yake amsa tambayoyi a ofishin hukumar da ke Ibadan, inda ake tsare da shi, wanda ake tuhuman ya dage ne a kan shi mai gaskiya ne.
Ta ce, in an same shi da laifi, za a tuhume shi ne a doka ta 465 na kundin fenal kod, sashe na 25 na aikata laifuka makamantan hakan.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: