Ba Ni Da Haufin Cewa PDP Za Ta Karbi Kasar Nan Idan A Ka Yi Zaben 2019 -Aisha Maijama’a — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

TATTAUNAWA

Ba Ni Da Haufin Cewa PDP Za Ta Karbi Kasar Nan Idan A Ka Yi Zaben 2019 -Aisha Maijama’a

Published

on


Wannan hira ce da IBRAHIM MUHAMMAD ya yi da daya daga cikin shugabannin Mata a jam’iyyar PDP, HAJIYA AISHA MAIJAMA’a. Ta bayyana mana irin gazawa da take ganin jam’iyya mai mulkin kasar nan ta yi sama da shekaru Uku a kama mulkinta ga yanda hirar ta kasance:

Da farko za mu so ki gabatar da suna da matsayinki a jam’iyyar PDP?
Suna na Aishatu Yakub Maijama’a a Kano na rike shugabar mata ta PDP a 2014 zuwa 15 sannan ina daga cikin dattawan jam’iyyar.
APC da ta karbi mulki daga wajenku ta cika shekaru uku da doriya a kujerar mulki ya ya ki ke ganin rawar da ta taka wajen ci gaban kasar nan?
Wato ala kulli halin idan mutum yace zai baka riga sai ka kalli ta wuyansa tukuna. A lokacinda PDP take mulki mun gamuda iftila’i na rashin tsaro da tashin fitintinu a jihohi musamman wasu daga na kudu da Arewa maso gabas da kuma na yan Naija Dalta da yawa mun sami abinda suka zama mana kalubale wanda dashi wannan APC ta yi amfani tace idan ta karbi mulki wannan abubuwa zai kau, to muma a lokacin a PDP mun san ba dalilimmu abin yake faruwa ba. Allah ne ya saukar dashi domin komai da lokacinsa, to sai muke musu addu’a Allah yasa hakan takasance idan sun karbi mulki. Allah yasa su kawo mana tsaro da suka yi alkawari sannan su kawo mana kwanciyar hankali da zaman lafiya ai ance zaman lafiya yafi zama dan sarki harshi sarkinma kansa.
Sai muke gani cewa mutanennan farfagandace irin tasu sun yi amfanine da wani yanayi da Allah ya saukar a wannan lokacin wanda suka yaudari talaka akan cewa zasu kawo masa zaman lafiya da kwanciyar hankali da bunkasar arziki, to daga baya sai abubuwa suka zama gwanda jiya da yau. Idan ka lura a lokacimmu ba a zuwa a dauki mutum a tafi dashi a ce iyalanka sai sun biya kudin fansa sannan za a karboshi.
A lokacin PDP za ka ga Fulani da ake ce musu fulani din ba wadanda suka yi shigar burtu suka zama fulani suke irin abinda sukeyi ba, suna zaman lafiya da kowace irin al’umma a Nijeriya a Afirka ma gaba daya domin su dama makiyaya ne, suna keta kowane lardi da kasa suna shiga da dabbo bin su, amma a yanzu sai ta zamanto cewa fulani da manoma da kabilu ba a zaman lafiya.
A lokacimmu babu wannan. Ka ga irin wannan kalubalene wanda gara baya da yanzu, wanda a baya da an bi matakin da PDP ta zo da shi, ai an kusa samun galabar Boko Haram din su ka zo suka yaudari talaka cewa zasu kauda duk wata fitintinu, talaka ya dauki kuri’arsa ya dangwala musu to yau ina muka wayu gari? Yanzu a kauyemmu Tudun wadan Dankadai inda na fito ba ka da ikon yanzu ka keta dajin Falgore ko ka shiga dajin Nata’ala caf za a daukeka ko kayi wajen dajin kudaru tsaf za a daukeka a wurin saidai danginka duk abinda kuka mallaka an tattara anba mutanen sannan su dawo dakai wannan masiface da bamu taba saninta a Arewa ba, da mukanji a wannan a wasu kasashe ko kuma muyi yan Neja-Dalta saboda turawa da shigowa hakar mai, mu dai a Arewa a wayo na ban taba ji an saci mutumba ace sai an bada kudi. Kwanan nan aka dauki wani bature ma’aikacin Dantata da Sawoe yaje duba gada da rana tsaka muna zaune muka rika jin harbe-harbe a Sharada. Ni dai gaskiya ban ga wani canji ba, imma canji ne sai dai na innalillahi.
A yakin neman zaben da APC ta yi na kanbama rashin tsaro ne ya kauda PDP daga mulki sai gashi kuna ganin ta gaza yanzu ku a matsayinku me ku ke na ganin kun sami karbuwa a wajen al’umma don dawo wa ku dora ga ci gaban kasar nan?
To ai yanzu duk wanda yake a Nijeriya indai magidancine ko matashi, ai basai ma PDP ta yi kanfen ba, zata dawo mulki saboda abinda zaka lura dashi wannan Gwamnati tana azabtarda mutanene da yunwa da talauci da kuma rashin tsaron kaga ai abu uku kenan sannan su kuma da suke hasashen cewa sun zone dansu kauda wadannan abubuwa su a zaune suke lafiya suna cikin wadata da walwala ta zahiri.
Duk wanda yake majalisa ko Gwamnati indai yana cikin mulkinnan idan ka kalleshi zaka ganshi cikin walwala ba abinda ya dameshi na kuncin rayuwa bai damu da makotansa ko yaya kasar take ciki ba, amma kullum budar bakinsu cewa zasu kawo gyara to gyaran a kansu kurum ya tsaya dama yunwace ta korosu sukazo suka shiga mulkinan dansu azurta kansu su mamaye dukiyar da PDP ta tara sannan kuma su sake dorawa akan laifinda PDP bata yiba su ce su suka yi to sai Allah ya jarrabesu gaba daya abin ya warware musu sun rasama yanda zasu samo bakin zaren.
Yau talaka ma basai an gaya masa ba, nayi maka imani duk mutuminda zai tafi dangwala kuri’a da yunwa zashi, wane mutumne yaje da yunwa ya kwana bai ciba ya bar ya’yansa da yunwa, bashida tunanin inda zashi, to wannanne zai sake zuwa ya dangwalawa wannan Gwamnatin kuri’arsa. Allah ma ya taimakemu su fito suyi zaben domin za ka ga cewa wannan barazanar da suka dauka yanzu su kama wannan su kulle su kama wancan su kulle sai su hana zaben ma.
Allah ya taimakemu mutane su fito suyi zaben saboda mutum Allah yayi masa basira menene daidai mene ne ba daidai ba, to zaka gani mutane da yawa sun dawo daga rakiyar wannan Gwamnati kowa yasan Gwamnatice ta yaudara ta karya ta zalunci zalunci akan talaka, talakan da ya dauki kudinsa ya sayi kati ya sawa Buhari ya dangwala masa kuri’a yanzu shi ake azabtarwa da kudinsa ya zabo wannan masifar ta yaya zai sake zabarta.
Ko da yaushe masu Gwamnati idan ana maganar gyara suna cewa yanda yanda ku PDP kuka bar kasarne a damalmale bayan shekaru 16 da kukayi mulki tasa ba a canji da sauri kina sane da hakan?
Bari in tambayeka idan gidanka ya rushe shekara 15 kayi tafiya bayan ka dawo sai aka taru aka rika baka tallafi yanzu sai ka tsaya sai bayan shekara 15 zaka gyara gidan . Duk wanda ya kawo maka tallafi ka suturta tallafinnan inace inka dawo bayan wata daya za a taras wannan gidan ka gyarashi . Wane tallafine a duniyarnan ba a ba wannan Gwamnati ba, wane irin bashine ba a yafe mata ba.
Wane irin kudin “paris club”bata tara ba, wane irin kudine Amurka da Ingila bata bayarba idan kana bibiya wane irin makudan kudade ne ba a samu na mai ba, wane irin rara ne Buhari bai tara ba, ya akayi har yanzu gyaran bai yiwu ba sai dada tabarbarewa ma abin yake, ai wannan ma zance ne kawai saboda idan dai talaka shine a zuciyarsu da ransu ai duk wannan abu da aka bayar zasu iya dauka su gyara in yaso sai aje. An yarda cewa suje su a ganninsu mu munyi barnar, su suka san munyi barna, mu bamusan munyi barna ba, amma suda suke ikirarin sunga barnar su nuna cewa sun gyara, amma sai koma baya aka samu. Kashiga kasuwa a Kano da kasuwani muka sani kaga mutum yana zaune a kasuwa zaice maka gwamma gwamnatin PDP da wannan Gwamnatin saboda an kakabawa mutane talauci talaka bashida ikon yanda zai sai wani abu, bazai iya saye ba, an kakaba musu haraji duk abinda ya samu Gwamnatice take karbewa. Duk abinda ka sani Gwamnati ta dora masa haraji to ta yaya talaka zai sake dawowa ya zabe su.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!