Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Kotu Ta Bayar Da Belin Wadanda Ake Tuhuma Tare Da Nnamdi Kanu

Published

on

Babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja, ranar Litinin din nan ne ta bayar da belin wadanda ake tuhuma tare da Nnamdi Kanu, shugaban ‘yan tawayen Biyafara, da ya yi layar zana ya bace.
Mai shari’a, Binta Nyako, tun a ranar 20 ga watan Fabrairu ne ta yi umurni da a rabe a tsakanin tuhumar da ake yi wa Nnamdi Kanun da sauran wadanda ake tuhumar a tare da shi, kan yadda rashin Nnamdi Kanu a kotun ke neman tsayar da ci gaban shari’ar.
Wadanda ake tuhuman a tare da shi yanzun suna fuskantar tuhumomi ne guda uku na, Cin amanar kasa, su ne, Bright Chimezie; mai shirya ayyukan kungiyar ta IPOB, da wani mamban kungiyar mai suna, Chidiebere Onwudiwe; Benjamin Madubugwu; da Dabid Nwawuisi.
Da take yanke hukunci kan sabon shigar da neman belin su da aka yi lokacin da aka sake gurfanar da su a ranar 20 ga watan Maris 2018, Mai shari’a Nyako, cewa ta yi babu laifi a bukatar neman belin da aka yi, da kuma la’akari da shekarun da suka kwashe a tsare.
Ta ce, wadanda ake tuhumar sun kwashe kimanin shekaru uku a tsare, alhalin ko da an same su da laifin da ake tuhumar su da shi hukuncin su ba ya wuce na daurin shekaru biyar zuwa bakwai.
Sai mai shari’ar ta gindaya masu sharudda kwatankwacin sharuddan da ta gindaya wa Kanu a lokacin da take bayar da belinsa a watan Afrilu na shekarar da ta gabata, na cewa ba za su yi hira da manema labarai ba, ba kuma za su halarci wani taro ko gangami ba.
Bayan wannan kuma, sai ta neme su da su kawo mutane biyu da za su tsaya masu kowannensu wadanda za su ajiye tsabar Naira milyan 10 a asusun kotun.
Ta kuma umurce su da su rika kai kansu ga Kwamishinan ‘yan sanda na Jihohin da suke bayan kowane sati biyu a Jihohin da suke.
Sai ta umurci, Chimezie da ya rika kai rahoton kansa ga Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Ribas; Onwudiwe da Nwasuisi ga Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Enugu, shi kuma, Madubugwu ga Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Anambra.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: