Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

’Yan Sanda Sun Sa Ladar Naira Milyan 1 Ga Wata Mata

Published

on

Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Legas, ta yi tayin biyan ladar Naira milyan guda ga duk wanda ya bayar da bayanan da suka kai ga kama wata mata da ta lullube fuskarta, ta yi zargin cewa, Insifekta Christopher Nabugwu, yana wata rayuwa ce ta almubazzaranci da fantamawa.
Matar ta yi wannan bayanan ne a cikin wani faifan bidiyo da ya watsu a kafafen sadarwar yanar gizo, a ciki ta yi zargin cewa, Insifekta Christopher Nabugwu, ya tara tsabar kudin da ya zarta Naira bilyan 2, da kuma kadarori, ta ma kara da cewa, shi ke mallakan wani makeken gini da ke kan lamba 27 kan titin, Remi Fani-Kayode, GRA, Ikeja, wanda ya haura Naira milyan 250, yana kuma sheke ayarsa ne a wasu tsala-tsalar motoci masu dan karen tsada.
Cikin sanarwar da rundunar ta fitar a ranar Lahadi a Legas, ta bakin kakakinta, CSP Chike Oti, rundunar ta ce, wannan labarin ya janyo hankalin Kwamishinan ‘yan sandar Jihar, wanda har ta kai ga ya kafa wani kwamiti da ya binciki zargin.
CSP Chike Oti, ya ce, “An binciki maganar. A karshe kuma, zargin ya tabbata duk karya ne, an dai so ne a bata ma haziki kuma jarumin rundunar suna kawai, domin kuma a kunyata rundunar.”
Oti ya ce, Kwamishinan ‘yan sandan, Edgal Imohimi, zai yi farin cikin duk wani dan kasa nagari da ya bayar da bayanan da suka kai ga kama wannan matar.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: