Connect with us

RA'AYINMU

Alkalai Da Batun ‘Yancin Sashen Shari’a

Published

on

A kwanan nan ne Alkalin babbar kotun kasarnan, Mai shari’a Walter Onnoghen, ya nuna matukar rashin jin dadinsa kan yadda ‘yan siyasa ke tsalma bakinsu kan abin da ya shafi nada alkalai a kotunan kasan nan. Ya nuna jimaminsa kan yadda tsarin nada alkalan ke tafiya yanzun haka a cikin kasarnan, ta yadda hatta gwamnan Jiha, matukar babu sunan alkalin da yake so cikin alkalan da hukumar tantance alkalan ta zayyana wadanda take nufin mika su ga cibiyar hukumar ta kasa domin a nada su a matsayin alkalai, to matukar babu sunan dan takarar na gwamna, sai ka taras gwamnan ba zai taba bari sunayen nan su isa ga shalkwatar hukumar ba. Mai shari’a Walter Onnoghen, ya ce, hakan ya nuna yadda manya masu fada aji a kasarnan suka mamaye sashen na shari’a, wanda kuma hakan yake tozartar da sashen na shari’a gami da dankwafar da ayyukan sashen.
Wannan fusatan da babban alkalin na kasa ya nuna, tunatarwa ne ga irin rawar da kotun kolin ke takawa a sashen na shari’a, duk kuwa da kasantuwarsa daya daga cikin turakun gwamnati uku wanda sashe na 153 na tsarin mulki 1999 ya ba su. Kamar yadda sakin layi na 21 na daya daga cikin ukun tanaje-tanajen tsarin mulkin na 1999, sashen na shari’a yana da daman baiwa gwamnonin shawarar wanda ya kamata a nada cikin mutanan da hukumar shari’a ta jiha ta gabatar masa a matsayin babban mai shari’a na Jiha, manyan alkalan kotunan Jiha, Grand Khadi na kotunan daukaka kara na Shari’a na Jihohi, da kuma shugabanni da alkalan kotunan daukaka kara na al’ada na Jihohi.
Abu mai mahimmanci ma, hukumar sashen shari’a din na kasa, wancan sassa na tsarin mulki da aka ambata a sama, ya ba shi daman amsa da kashe kudade. amma abin bakin ciki, hukumar ta sashen shari’ar na kasa tana iya gudanar da wannan aikin nata ne kadai a mataki na tarayya, amma an kwace mata wannan hakkin nata a mataki na Jihohi. Mahimmancin na sashen shari’a wajen tabbatar da bin dokokin kasa da kuma tabbatar da ana bin Dimokuradiyya sau da kafa, shi ne mafi mahimmanci a tsakankanin turakun mulki uku. Amma sai a kullum sashen yana dogaro ne da sauran sassan turakun biyu kafin ya sami daman yin aikinsa.
Misali, sashen na shari’a, ba shi da tabbataccen iko akan ko wane ne ya kamata ya zama jami’i a sashen na shari’a, da cirewa ko canza jami’an sashen na shari’a da kuma karfin aljihun sashen. Sashe na 17 (2) (e) na tsarin mulki ya bukaci samar da cikakken ‘yancin da ba shi da wani kaidi da kuma matsayin cin gashin kai na kotuna. Matukar ana son sashen na shari’a ya rika gudanar da ayyukansa yadda ya kamata, kamar yadda wannan sashen na tsarin mulki da aka ambata a sama ya tanadar masa, ya zama tilas ya kasance yana da ‘yancin aljihunsa daidai gwargwado da kuma cikakken ‘yancin cin gashin kai ba tare da wani kaidi ba.
Wadannan sune matsalolin da aka tilasta wa sashen na shari’a rungumarsu, a lokacin da yake fafutukar kare ‘yancinsa. A namu fahimtar, tsarin sashen na shari’a a wannan kasan bai samar da irin wannan ‘yancin kan da ake da bukatar a samar wa sashen ba, ta yanda zai sami daman gudanar da ayyukansa ka’in-da-na’in. duk wannan sun samo asali daga kwacewar ikon da aka yi wa sashen kan batutuwan da suka shafi, nada alkalai, sauke alkalan, samar da kudade ga sashen na shari’a da sauran yanayin aikin ma’aikatan sashen, wadanda duk an maishe su a hannun gwamnati mai wuka da nama.
Duk da cewa, sassa na 84 (2) (4) (7) da 121 (3), na tsarin mulkin sun baiwa sashen na shari’a ikon tafiyar da lamurran kudadensa, wanda ya ce za su rika fitowa ne daga aljihunan ayyukan yau da kullum na gwamnatocin tarayya da kuma gwamnatocin jihohi, amma babu kuma inda tsarin mulkin ya ayyana ainihin kason da ya kamata a rika baiwa sashen na shari’a. Sashi na 121 (3) na tsarin mulkin na shekarar 1999 karara ya bayyana cewa, “Duk wasu kudade da gwamnatocin Jihohi za su kebe wa sashen shari’a a Jihohinsu, kai tsaye su danka kudaden ne ga shugabannin kotunan da abin ya shafa.
Amma kawo yanzun, ba wani gwamna a Nijeriya da ya yi aiki da wannan dokar ta tsarin mulkin. A namu ra’ayin, yin hakan tsalma baki ne na ba gaira ba sabar kan harkokin tsarin shari’a na kasarnan, inda gwamnatocin kan rike da ragamar ‘yancin sashen na shari’a da ma majalisar, wadanda suke yin dokokin fitar da kudaden, wanda hakan ya baiwa sassan biyu na madafun iko yanka wa kansu abin da suka ga dama, sa’ilin da shi kuma sashen na shari’a yana gefe ya yi tagumi yana sauraron abin da sauran sassan biyu da ke tare da shi a hukuncin tsarin mulki suka ga daman yanko masa.
Hakan ya tilasta wa sashen na shari’a gurfana da yin durkuso yana neman duk wani abin da yake da bukata daga sauran sassan biyu, lamarin da yake mai matukar hadari. Ra’ayin wannan jarida ne, matukar ba a bayar da cikakken ‘yan cin gashin kai marar kaidi ga sashen na shari’a ba, wanda ya kunshi cikakken ikon hukumtawa da kuma saka wa duk wani jami’i na sashen shari’a ga sashen na shari’a ba, matsalan tsalma baki da siyasantar da sashen na shari’a, nada alkalai ba za a taba kawar da shi ba. Shakka babu, rashin hakan ya nuna ana fuskantar wata babbar barazana ne ga sashen shari’a da ma ita dimokuradiyyar kanta.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!