Connect with us

ADABI

Mallam Bahaushe Ga Naka (5)

Published

on

Hakazalika, saboda tabarba rewar tarbiyyar yaran, a waje, wani ba ya da ikon kiran dan sa ya aika. Idan mutum ya ba dan sa kudi ya aike shi sai ya gudu ya kashe kudin. Idan mutum ya biyo sawu, ko ka na ganin wai ka shaida ma Baballe mahaifin sa don ya yi masa fada don ya gyara halin sa, to sai shi da Atika da sauran yaran su rufe kofar gida su taru su yi ma mutum dukan tsiya. Idan kuma mace a makwabta ta yi masu ba daidai ba sai Atika da sauran yaran su taru su afka mata cikin gidanta su yi mata duka sai sun bar ta kwance. Idan kuma dan ta ya dauko magana ko ya jawo fada a waje, da ya shigo gida, kai da ya yi ma laifi, muddin kafar ka ta tako zauren gidan to nan ma sai su rufe gida su yi maka duka kaima. Ta kowacce hanya dai babu tarbiyya mai kyau. Ka ga sun ma ci amanar kyauta ko kiwon da Allah Ya basu. Tunda an ki a ba yara tarbiyyar da ta dace.

Saboda tsiya sai da ta koma Baballe, abincin da Atika ke sayarwa, sai ya saya. ‘Yarsa ta cikinsa za ta dauki tuwon ta kai yara, shi kuma za ya aiko kanenta da kudi ya saya masa. Dokar Atika kenan, tunda bay a bada kudin cefane saidai a dafa ya ci. Ta kuma ce masa ya tashi ya koma Ibbo neman kudi ya ki. Har kudin mota ta bashi don ya tafi ya basu wuri ya ki.

Wani lokaci kuma sai shi da Atika, kowa ya rike tsabga ko wani abin duka su zauna su yi ta zagin juna, idan su na yin rigima. Ya na ‘ubanki na ce’, itama ta na cewa ‘ubanka na ce’. Ka ga in ba talaka ba ba mai zama shi da mai dakinsa ba mai ganin darajar wani. Ya ce mata shegiya diyar mashayin giya, ita kuma ta ce masa ‘e, ai ubanta ya ma burge da ya sha giya, giyar kuma ta alkama ta alfarma, shi nasa uban ai burkuma ya sha, giyar da ba wata giyar kirki ba, giyar dussar dawa wadda maguzawa ke hadawa. Har ma Halisa ko Turai, wata daga cikin su kan shiga gidan su raba su fada.

Rannan Halisa da Turai su na zaune su na hira a gidan Atika sun a yi wa juna ba’a kamar yanda su ka saba sai ga dan aike daga gidan babbar ‘yarta da ake kira Saude. Cewa ta zo maza-maza. ‘Lafiya?’. Ya ce ‘ina fa lafiya?’. Su duka su ka figi hijabai sai gidan. Su na isa su ka tarar da Saude ta haihu, ga ta kwance cikin jinni, a gefe guda ga jariri na ta kuka. Ga Saude cikin yunwa ga jariri cikin yunwa. Turai ya mazaya idanunta biyu kowacce kusurwar dakin ta ga ko tsumman katifa da za a yada ya tabbatar maka dakin kwanciya ne babu. Dakin ba komi sai wasu tarin tsumman suturu a can lungu, kamar dai tungar mahaukaciya. ‘To yaya za ayi?’. Atika ta tambayi ‘yar. Saude ta ce a fara kawo mata abin ci tukun. Amma su duka biyun ba mai ko anini. Halisa ta ce: ‘kada a bata lokaci tunda har yanzu jinni na dibar ta’. Turai ta ruga waje ta tsayar da mai taksi, su ka kwashe ta sai asibiti. Aka yi mata allurar tsayar da jini. Halisa ta sayo mata abin ci. Sannan Halisa ta sake yin tsaye sai da ta ga an yi mata karin jini ta biya kudin. Turai kuma ta ruga kasuwa ta sayo wa jariri kayan sawa. An ma har su kwana su ka wuni a asibitin nan mijin Saude bai zo ba. Ka ji dan iska, talaka, maras tunani, maras arziki.

Babi Na Hudu : Baballe a Bisa Sikeli

A babban zauren taro na Jami’ar, manyan furofesoshi jajjayen fata sun taru. Manyan dalibai masu nazarin karatun digirori na biyu da na uku sun yi sahu sun zauna. Farfesa Cassen Carry ya mike ya gabatar da takardar Malama Turai Abba mai taken halayyar Mutanen Afrikiyya da yanda tarbiyyar su ta shafi zamantakewar su. Aka ba Turai izini ta mike ta gabatar da halin talakan Arewa, bahaushe, inda ta bada misalin halayen Baballe da Atika da ‘ya’yansu da ke zaune a Kantuk kaf.

Turawa su ka fara ihu su na tafi. Har daga cikin su wasu da su ka taba zama kasar Langeri su ka rika buga kafa su na cewa ‘shege Baballe, dan iska, talakan banza talakan wofi’. Nan su ka ji ashe ma Baballe, idan sallah karama ko babba sun zo ko lokacin shara ko kuma idan abubuwa su ka tsure masa in ba ya da ko sisi sai ya shafa ma fuskarsa bula da farar kasa ya daura walkin kura ya rike kahon mariri ya bi kofar gidajen masu hali na Ilarsu ya na hura shi, ya na rawa. Su kuma su yi ta bashi kudi da sutura. Turawa su ka yi ta dariya su na cewa ‘tsiyar ko illar talauci kenan’.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!