Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Rundunar ’Yan Sanda Ta Kama Boka Shugaban Kungiyar Asiri A Ogun

Published

on

Jami’an ‘yan sandar farin kaya daga rundunar ‘yan sanda ta Lagos sun kai samame a unguwar Ayegbami Imosan, Ijebu A Jihar Ogun ranar Talata inda wani mai maganin gargajiya, wanda ake zargin cewar yana da hannu a cikin harin da Badoo suka kai, suka kai ma Fatai Adebayo hari.

Tawagar ta hada da ‘yan sanda kota kwana na SARS, da kuma masu kawo dauki, da kuma Hukumar kulawa da muhalli ta jihar Lagos, da kuma wadanda kulawa da laifi na musamman, a karakashin  shugabancin kwamishinan ‘yan sanda na jihar Lagos Edgal Imohimi.

Mazauna unguwar cikin tsoro suna kallo lokacin da ‘yan sanda suka kai mamaye a gidan tsafin Adebayo, suka rufe shi.

Kamar yadda ‘yan sanda suka yi bayani su ‘yan kungiyar Badoo su kan yi taronsu a wannan gidan tsafin, domin su yi rantsuwa ta asiri kafin su tafi, wani mummunar mamaya a Ikorodu Lagos.

Daga cikin wannan gidan tsafin an lura da akwai kayayyakin tsafi kamars injin nika dutse, carbi,kwalabe, daban-daban sai kuma kasa.

Imohimi ya sahaida wa manema labaraicewar wani dan kungiyar Badoo da aka kama makon da ya wuce, ya ambaci sunan Adebayo, akan cewar shi ne yay i jagorancin ‘yan sanda zuwa can. Y a kara da cewar rundunar ta kama wani jagora kungiyar shi ma an kama shi

Ya  ciagaba da karin bayanicewar makon da ya wuce sun samu nasara wajen yadi da ;yan kungiyar ta’adda, a Ikorodu wadanda mutane suke kiranta bsuna Badoo, shi ma shagaban kungiyar an kama shi, an kama shi ta hanyar ruwa ne saboda yana kokarin gudu ne,duk kuma wadanda ake tuhuma suna tare da mu.

Daya daga cikinsu ya bayyana cewar ya aikata laifin da ake zargin shi da aikatawa, inda har ya kara bayanin cewar idan zasu fita zuwa kashe wani, shugaban kungiyar shi ne ke kai su wurin, inda ake sa ran zasu taimaka masu. S h ma mai sayar da maganin gargajiya da shine ake hada kai.

Ya cigaba ta bayanin cewar ‘’Ina yi ma mutanen  Ikorudu da kuam sauran al’ummar Lagos, ba zasu tsaya hutawa ba, sai sun kawar da abubwan da ake yi wadanda sun sabawa doka an daina yinsu a Lagos. Amma kuma sai Imohimi ya ce ‘yannjaridu su daina tambayars Adebayo saboda kuwa akwai  jawabi wanda za, a yi ma manema Labarai a Lagos ranar Alhamis.

A wani abu kuma wanda ba, a saba da shi ba wanda ake zargin ne , ya yi murmushi, a lokacinda aka ce ma shi ya rike daya daga cikin duwatsun da ake nikawa.

Ya ce shi bait aba kashe wani ba ta hanyar tsafi ya kuamcigaba da cewar’ shi bai jin Turanci amma shi dutsen nikan ana amfani da shi ne, wajen nika tattasai da kuma magunguna.’’

Matarshi da mahaifiyarshi barkewa da kuka suka yi lokacin da ‘yan sanda suka tafi da shi. Mahaifiyar wadda ake kira Toyin Ogunyemi ta ce shi ‘’Adebayo danta ne, shi mai sayar da maganin gargajiya ne, shi ba barawo bane, kada a kashe shi. Shi yana harhada magani ne wajen taimakawa mutane, kamar masu rashin lafiya, masu neman aiyyukan yi da kuma ‘yan kasuwa. Yana amfani ne da dutsen nikan, wajen nikawa mutane, matarshi ma tana taimaka ma shi.’’

Akwai wani abin mamaki da ya faru lokacin da kwamshinan ‘yan sanda Imohimi ya kai ziyara gidan Basaraken Imosan Chief Tajudeen Muili, domin ya sanar da shi an kama Adebayo. Sai Muili mai garin Ija Oloko na Imosan sai ya nuna rashin jin dadinsa dangane da aikata laifin.  Lokacin da ya nemi a bashi damar yay i magana da wanda ake zargi da aikata laifin, kuma saboda me aka kama shi, amma sai kwamishinan ‘yan sandar yaki amincewa da bukatar, amma sai    kawai ya ce, ai ana bincike ne danagane daaikata laifin. Amma dai ya amshi nambar wayar Basaraken ya  ce, zai rika ba shi bayanan ahalin da ake ciki. Tawagar ta sake dawowa gidan Adebayota lalata wurin da ake tsafi.

Ana iya tunawa ita kungiyar asiri ta Badoo ta dade tana gallazawa mutane musamman mazauna Ikorodo da makwabtansu inada suke kashe mutane

Ayyukan su ‘yan kungiyar ya hadu da cikas watannin da suka wuce, amma kuyma yanzu ansamu zaman lafiya a wuraren da suka dade cikin tashin hankali. Amma kuma sai ga shi su ‘yan wadannan kungiya sun koma da kai hare hare kamar yadda suka saba a Ikorodo.

A harin da suka kai sun kashe wani Pastor na Redeemed Christian Church Of God Bictor Kanayo a unguwar Igbogbo cikin Ikorodo. Matar Pasto da dan shi an barsu sumammu, an kuma kai su Babban Asibitin Ikorodu.

Ranar 22 ga Disamaba na shekara data gabata, su ‘yan kungiyarsun kai ma wasu Iyalai hari a garin cigaban al’umma na Itesiwaju ,a Ibeshe Ikorodu, aka kashe mutum da dans hi , surukar shi, aka kuma yi matarsa rauni.

Harin da bai dade ba shi ne ranar 30 ga Disamaba a layin Alajo Abule Osorun, Ibeshe inda ‘yan kungiyarsu aka yi ma kan miji da matar rauni saboda sara, suka yi ma dansu mai wata biyar rauni a ka.

Shi dai maigidan Sikiru wanda aka fi sani da suna Shako ya mutu ne washe gari a Asibitin koyarwa na jami’ar jihar Lagos Ikeja, yayin da kuma matar da dan ana cigaba da lura da su.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: