Zan Iya Debo Ruwa A cikin Rariya –Sabo Wanzami — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

TATTAUNAWA

Zan Iya Debo Ruwa A cikin Rariya –Sabo Wanzami

Published

on


Sana’ar wanzanci sana’a ce ta gargajiya da ake gadon ta tun iyaye da kakanni. Ta cikin wannan sana’a ce ake yi wa yara kaciya da yi wa jarirai aski, da yankan cibiya, da cire Beli. Sannan ga mutanen da suke da gadon tsage na baki ko na ciki, ko na wani bangare a jikinsu, duk wannan aikin wanzami ne ya zo ya tsaga duk inda ake bukata a jikin mutum. Malam Sabo na daga kwararrun wanzamai dake zaune a babban birnin tarayya Abuja cikin Unguwar Utako, ya shaida wa wakilin ‘LEADERSHIP A Yau Juma’a’ Rabiu Ali Indabawa cewa, a irin bajintarsu ta wanzamai idan suna wasansu na al’ada zai iya debo ruwa a rariya ba tare da ruwan ya zube ba, duk da cewa masu karin magana suna cewa “Kowa ya sai rariya ya san za ta zubar da ruwa.” Ga yadda hirar ta kasance. 

Bari mu fara da sunanka.

To ni dai sunana Sabo Wanzan, kuma ina zaune ne a nan unguwar Utako dake a nan babban birnin tarayya Abuja.

 

To Malam Sabo ga ka a babban birnin tarayya Abuja, me yake zaune da kai a wannan gari?

To Alhamdulillahi, abinda ya kawo ni wannan gari har nake zaune cikinsa shi ne, wannan sana’a ta wanzanci.

 

To kana wata sana’a bayan bayan wanzanci?

A a ba ni da wata sana’a da wuce wannan sana’a ta wanzanci, ita na sani kuma ita nake yi.

 

Ka kai kamar shekara nawa a wannan gari kana wannan sana’a?

A gaskiya na kai shekara 20 ina zaune a wannan Unguwa ta Utako, kuma ina wannan sana’a.

 

Ita wannan sana’a ta wanzanci da kake yi, shin ka gaje ta tun iyaye da kakanni ko kuwa taka haye ka yi?

To Alhamdulillahi, ita wannan sana’a na gaje ta ne a wurin mahaifina, shi ma kuma ya gaje ta a wurin nasa mahaifin. Don haka ba taka haye na yi ba, gado na yi tun asali. Kuma ita ce sana’ar da na dogara da ita, sakamakon rufin asiri da nake gani da alhairai a cikinta.

 

Sau da yawa za ka ga wasu iyayen sun gaji sana’a, amma sun fi son ‘ya’yansu su kama wata hanyar, kana sha’awar ‘ya’yanka su gaje ka a kanta?

Kwarai ma kuwa, ai sun ma gada tuni, kuma suna nan a kanta, ita su ke yi kuma ba sa kyamarta.

 

Ya za ka kamanta zamanka na gida da na nan Abuja wajen ci gaban sana’arka?

Alhamdulillahi kamar yadda na gaya maka, mun baro iyaye da ‘ya’ya a can gida suna wannan sana’a, a can din ma akwai ci gaba, nan din ma tun da Allah ya sanya neman abincin haka yake, ana samun alheri sosai. Don haka muna samu ci gaba kamar yadda yake a can gida.

 

A ko wace sana’a idan an duba za a ga akwai nasara akwai kuma akasin haka, wato abubuwa na jin dadi da kuma akasin haka, ciki wanne ka amfana da shi.?

To Alhamdulillahi ka san ala kulli halin idan mutum zai yi hakuri da abinda yake samu, kuma ya tsaya iya matsayinsa, sannan ya dogara ga Allah, to lallai zai samu ci gaba. Idan kuma mutum ya gaza hakuri sai ka ga yana hangen wani wuri wanda kuma zai je a karshe zai yi ta shan wahala. Saboda haka mu tamu nan mun rike ta hannu bibiyu, kuma samun alheri da ci gaba a cikinta, sannan mun gadar wa ‘ya’yanmu su ma kuma in sha Allahu ‘ya’yansu za su gaje su.

 

Ita dai wannan sana’a dama ita aka fi sani tun asali, sai ga shi kuma an samu ci gaba ana yi da kayan bature, shin wannan abubuwa na zamani sun rage martabar sana’arku ku kuwa har yanzu ana nan kamar da can?

Alhamdulillahi wadan nan ba su hana mu samu a sana’armu ba, domin a bangaren sana’armu dai wanzami na farko za a nemi ya je ya gyara jariri, kuma yana yi, za a kira shi ya yi kaciya, kuma yana yi, idan da akwai Beli, na mace a kasa yana yi. ka ga kuwa ba zai yiwu yayi dai-dai da masu sana’ar aski na shago da suke yi da wutar lantarki da Kilifa ba. Sannan a nan din ma muna amfani Kilifar wutar ta zamani, kuma akwai wadda ake caja ta ma da wuta wadda ko da babu wuta sai mu yi amfani da ita kawai.

To in ka duba sai ka ga ci gaban ma bai bar mu ba, kuma ba ma samun matsala tsawon awoyi kafin a kawo wuta in sha Allahu, to ka ga ashe mu ma muna tafiya da zamanin kamar sauran. Ashe idan ka duba sai ka ga muna yin abinda ba sa yi.

 

Ka yi maganar cire Beli da Kaciya, kuma wadan nan abubuwa ne masu hadarin gaske, to ke nan ko wane wanzami ne ke iya cire beli da yin kaciya ko kuwa har da ‘yan taka-haye?

Eh a gaskiya yin wadan nan abubuwa babu shakka yana da hadari, domin duk ma kwarewarka a kan aikin sai ka bi an nuna maka yadda yake, sannan a nuna maka cewa wannan abin idan ka yi kaza da kaza za ka yi ya zama kama kaza shi ne dai-dai a wannan aikin, domin idan ka shiga cikin aikin gaba gadi kuma, to akwai lokacin da za a zo wurin da basirarka za ta tsaya tunda ba gada ka yi ba, ka ga da an samu kuskure sai ka ga lamarin ya haifar da matsala, Allah ya kiyaye.

Amma idan dan gado ne to ka ga dole cikin sana’a akwai abinda ya sani na sirrinta, sannan kuma akwai kuma shawara ko taimako da zai rika nema wurin magabata da abokan sana’a don bunkasa ta.

 

To akwai ‘yan tauri akwai kuma ku wanzamai, kuma ko wanne cikinku yana amsa shi mai shiri ne, cikinku kowa zai iya aikin wanzanci ko kuwa lallai sai wanzami?

To Alhamdulillahi shi aikin wanzanci, wato aski da sauransu da kuma wancan bangaren ba daya bane, idan Allah ya baka nasibi ko da ba ka da lakani za ka iya yinta dai-dai gwargwado, amma ba dai-dai da wanda yake yinta kamar wanda ya gada ba, shi daban ne, dole kamar yadda nake gaya maka sai da ka yi biyayya wani kai ma zai bika, domin idan ba ka yi biyayya ba, ta yaya za a yi ka san sirrinta, ko ko me ye a cikinta, sannan kuma yaya aka yi ka iya har ma wani ya zo ka koya masa?

 

A wasu lokutan makera na wani wasa da wuta idan ana wani sha’anin biki ko na shekara, ku ma a naku bangaren ku kan yi?

To Alhamdulillahi, ko da yake mu kananansu ne ‘ya’yansu ne kuma jikokinsu ne, amma kai tunda kake ba ka ganin wasan wanzamai ba, kamar su shan kabewa, ko kuma wasa da za a ce ana nadin Sarki, ko kuma za a tafi nuna wannan sana’armu ce ta gado kowa ya nuna sana’arsa ce ta gado kai baka taba gani ba?

 

A’a ni ban taba gani ba

To ga misali muna da wasanni iri-iri, a yanzu haka zan iya daukar rariya in debo maka ruwa a cikinta ba tare da ruwan ya zube ba. Sannan akwai daga cikin iyayenmu wadanda za su fito da jariri a wurin a yi masa aiki, akwai wadanda za su fito da tsintsiya a tsoma ta a ruwa a hada daya da daya a tayar da ita tsaye mutum ya hau saman kanta ya tsaya ba tare da ta karye ba. Kaza lika akwai wanda zai zo daga cikinmu in ya buga tabarma tana kasa za ta koma sama shi da abokinsa su hau su yi zamansu babu abinda zai same su, Allah ya hore masu wannan daga cikin iyayenmu.

 

Mene ne shan kabewa da ka ambata a baya?

To misali shi dai shan kabewa wasa ne na wanzamai, akan je a samo gashi a hada shi a dama furarsa a hada da ruwan tinya da jini, duk wanda yake amsa sunan wanzami ne sai ya je ya sha, wannan shi ne ake kira shan kabewa.

 

To amma an ce ita Tinya ai guba ce ko?

Gaskiya ne Tinya guba ce, amma ga wanda bai shirye mata ba, ko yanzu in aka nuna maka yadda abin yake in ka ci Tinya babu abinda za ta yi maka. Kuma ba ma wanzami ba, kai ma da ba wanzami ba idan aka hada wanzami zai iya cewa ka sha, kuma idan ka sha babu abinda za ta yi maka.

 

Sau da yawa za ka ga misalin ‘ya tauri, irin karafa masu kaifin da ake mu’amala da su ko ba a gida ba, idan an sa a jikin ‘ya’yansu ba sa yanka su, ku ma haka abin yake a wurinku?

To ai misali ai ka sani shiri ne kowa da irin nasa daban-daban a jikinsa, idan Allah ya taimake ka da shirinka, dai-dai da gumi kai din nan idan na shafa maka aka yanka ka ba za ta kama ka ba. Idan kuma Allah ya sa wani shiri ka zo mana da shi kana bako za ka takale mu, muna iya fitowa da irin abubuwan da aka nuna mana da za mu takali baki da kuma namu, sannan ko yara kanana a cikin gida da za a yi wasa da su, ko kuma wadanda aka zo da su dominsu dama an fito da su ne a nuna masu, ko dai wani kwanansa ya kare a ciki, don za ka ga duk sanda aka yi wasan wanzamai zai wahala a ce an ta shi wani kwanansa bai kare ba.

 

Maganar yi wa jariri aiki da ka yi a baya, kamar yaya aikin yake?

To misali ai ka san jariri ana iya haifarsa ana cire masa Beli, wani ma daga ranar sunan ake yi masa kaciya. To daga irin nan din ma ana iya yi masa aiki a wurin a cire belin a yi masa askin suna, har a yi masa kaciya kuma za a iya yi har a mayar da shi baka ganshi ba.

 

Shekaru kamar 30 zuwa 40 da suka wuce babu kaciyar sa wando, ita wannan kaciya ta sa wando yaya take a wurinku?

To Alhamdulilahi hikima ce da kuma karin daraja da ta samu, ba wani abu bane illa magani na da can da iyayenmu suke yi, wanda idan Allah ya fuwace maka sai ka hada da wannan abin in ka iya da zarar ka hada sai ka yi abinka. Kuma duka wadanda suke yin wancan da wanda suke yin wannan duk daya ne. Za ka iya yin wancan aikin da wadancan suka gada in aka nuna maka yadda aka yi kuma ka yi aikinka ka zauna lafiya.

 

Shin gaske ne, an ce idan aka bata wa wanzami rai wai ya kan sanya wa mutum wani abu a cikinsa?

Dariya! To Alhamdulillahi shi ka san komai na yanzu zamani ya canja, ai yanzu wanzaman ba irin na da bane, domin da da ake irin wannan, hakikanin gaskiya iyayenmu sun yi wannan gwagwarmayar da mutane da kuma sauran wadanda suke abokan arziki irinsu, da abokansu wadanda suke tafiya wasanni. Lallai kamar yadda za ka taka wani a yanzu ka zauna lafiya, idan kamar da din ne ba za ka iya taka shi ka zauna lafiya ba, dole sai wani abu ya faru da kai ko da kadan ne.

 

To wannan ke nan yana nuna rashin hakuri ko kuwa gudun kada a kawo wa mutum wargi?

Misali ai ka sani an ce ana neman bakar tambaya saboda wata rana, kowa akan sana’arsa ya kamata ya rike ajinsa, saboda kada a raina shi. Wani abin idan ba ka da irin wannan din ko kuma baka taba nuna shi ba, wani zai dauke ka ba ka san komai ba, ba ka da komai, aikin banza ma kake yi. Ko da dai za ka dan ratse kadan, tunda hanya ce muke dan kaucewa amma kadan don kada a ce ba mu san komai ba. Amma idan ka gyara ajinka aka wuce wurin sai ka tuba ga Allah tunda ana tuba.

 

To ina ji ana kiran duk wanzami da magaji to kowa ne magaji yaya abin yake?

To ka san gado yadda yake, ni na gada a wurin babana, babana ya gada a wurin kakana, shi kuma ya gada a wurin na sa mahaifin. To haka da haka har zuwa namu jikokin, shi ne za ka ji na cewa kowa magaji.

 

To shi wannan gado na wanzanci, maza ne kadai suke yi ko har da mata?

To Alhamdulillahi, ai duk kan danda wanzaci ya Haifa in ka ga saki wannan gado na sa ko mace ko namiji, to ba dan halak bane, kuma ko mace tana iya gadonsa, kuma hatta mace za ta iya wanzanci. Wallahi wallahi na rantse maka da Allah matata karamar, za ta iya yi maka aski kwal-kwabo har saisaye duk za ta iya. Ai in dai ba na nan ko jariri aka kawo za ta iya yi masa aski.

 

A karshe wane irin kira za ka yi ga ‘yan uwanka wanzamai.

To Alhamdulillahi ni kiran da zan yi a gare su, ina so su sani wannan sana’a ta mu mai albarka ce, kuma akwai rufin asiri a cikinta duk da cewa wasu suna ganinmu a wulakance, kuma wallahi mun wuce wulakanci a wannan sana’a. Duk inda wanzami yake ya wuce wulakanci, don idan aka ce ga wani gida da suka fi kowa sutura, to idan wanzami ya je gidan sai ci abinci, domin ka ga ai a gidan za ka samu ana haihuwa ko kaciya.

Sannan zai yi wahala ka ga wanzami yana roko, ko da za a samu za ka ga ba su da yawa, sannan idan dai ba mutum ne ya zubar da darajarsa ba, to wannan sana’a tana da rufin asiri sosai.

Kuma ina sake kira ga ‘yan uwanmu wanzamai su rike wannan sana’a ta mu da muhimmanci su daukaka ta kamar yadda Allah ya daukake mu. Sannan mu rika yin hakuri da juna domin me, domin duk inda ya ajiye ka ka samu nasibi haka Allah ya so, idan bai so ka ba ba za ka gani ba.

kuma ko da a gidanku ana samun haka, sai ka ga gaka kai ne babba, amma sai ka ga nasibin ba ya kanka yana kan kaninka. Allah ya taimake mu ya ba mu sa’a, Allah ya ba mu zaman lafiya a kasarmu, wannan kamfani na ku Allah ya kare shi ya kuma daukaka ku.

 

To Malam Sabo wanzami mun gode.

Ni ma na gode.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!