Duk Duniya Ta Shaida Shugaba  Buhari Mai Gaskiya Ne -Imam Ahmad — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

Duk Duniya Ta Shaida Shugaba  Buhari Mai Gaskiya Ne -Imam Ahmad

Published

on


Imam Ahmad Suleiman shi ne babban Limamin masallacin Juma’a na Magama Gumau karkashin kungiyar Izalatil Bid’ Wa’ikamatis ‘Sunnah [JIBWIS] a karamar hukumar Toro da ke jihar Bauchi.

A wannan tattaunawar da ya yi da wakilimmu da ke Jos, Lawal Umar Tilde, Malamin ya tabo maganar matsalar rashin tsaro da a yanzu ake fuskanta a kasar nan, da kuma cece-kucen da ake yi akan yawan rikicin da ake samu tsakanin Fulani makiyaya da manoma a wadansu jihohi na kasar.

Malamin ya kuma tabo sukan da wadansu mutane ke yi a game da kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na kirkiro da wuraren kiwo ga fulanin da kuma kokarin da gwamnatin ke yi don rage reshin aikin yi ga matasan kasar nan.

Haka kuma Malamin ya bayyana cewa duk Duniya an shaida Shugaban kasa Muhammadu Buhari da cewa shi mutum ne mai gaskiya. A sha karatu lafiya. Allah gafanta Malam, mutanen kasar nan sun yi tururuwa sun zabi shugaba Muhammadu Buhari a 2015, sai kuma ga shi yanzu yana ta samun suka da yawa daga wadansu mutanen kasar cewa ya kawo koma-bayan tattalin arzikin kuma bai iya mulki ba. Me za ka ce a kai?

Bismillahi Rahmani Rahim. Lallai Shugaban kasa Muhammadu Buhari, kowa ya sani mutumin kirki ne kuma mai amana ne, domin ba ma Nijeriya ba kawai duk Duniya ta yarda shi Alhaji Muhammadu Buhari, shugaban Nijeriya ba mai handama ba ne, kuma ba mai baba’lkere akan dukiyar mutane ba ne, hasali ma duk duniya ta yarda yana cikin na daya ko na gaba-gaba daga wadanda suke fada da cin hanci da rashawa.

Sannan kuma yana mai kokarin tabbatar da tsaro a kasar da kuma  azata  akan turba kyakkyawa wanda idan Allah ya yarda nan gaba kadan za a ga amfanin abubuwan da yake shukawa, wanda shi ya sa ma yake kokarin tallafa wa matasa ta bangarori daban-daban.

Misali, shirin nan na E-POWER, a sanina a kashin farko ya dibi matasa 20,000, sannan a kashi na bi yu ya dibi matasa kusan 300,000. To ka ga wannan duk yana nuna maka yana kokarin rike hannun matasa domin ya numa masu hanyoyin da suka dace.

Batun da ka fada cewa shugaban kasa ya yi akan matasa a kwan akin da suka gabata, kuma da fadan da gwamnati mai ci yanzu take yi na hana shan muggan kwayoy, ni a fahimtata, shugaban kasa shi uba ne na kowa da kowa, matasa da Dattawa, duka yana da ‘yancin ya yi wa kowa fada idan ya ga ya  kauce don ya dawo da shi bisa hanyar da za ta amfane shi.

Idan ka duba kasar nan za ka ga mafi yawa matasa ne a gaba-gaba, musamman akan aikata sace-sace da shaye-shayen muggan kwayoyi masu sa maye.

To ka ga a nan a ce maganar da shugaban wasa yake yi wa matasa cewa su gyara halayensu, ai gaskiya ne.  Domin a rayuwarmu ta yau za ka ga duk mutumin da yake fadin gaskiya  mutane da yawa suna tsanarsa.

Bai kamata a masayimmu na ‘yan Nijeriya masu neman ci gaban kasar mu rika fadin magana ba tare da la’akari da alheri ko rashin alherinta ba, musamman bisa abu mai kyau wanda za ta amfanemu, mu ri ka  shigar da siyasa a ciki, mu rika bata abubuwa, yin hakan bai dace ba.

Yanzu ka duba abin da ya faru a jihar Filato a kwana-kwanan nan na rikicin Fulani da makiyaya, kullum kokari ake yi a dora laifi a wajen Fulani, alhali ba a duba barnar da wadansu bangare ke yi ba.

Misali. A nan an yi fiye da wata uku ana kashe Fulani a kowane wayewar garin Allah a jihar ta Filato, amma duk irin koke-kokin da Filanin ke yi ba a ji, amma da zarar an kai hari wa manoma duk duniya sai sun yi ta cewa makiyaya ‘yan ta’adda sun kai hari sun kashe manoma. To ka ga a nan akwai siyasa a ciki.

Maimakon iyaye su  kira ‘ya’yansu su yi masu fada su gaya musu gaskiya, su nuna masu hanyar da ta dace don su bi su amfana, to amma sai aka kawo siyasa a cikin lamarin.

 

To ya kake ganin halayyar matasa, kamar dai yadda Shugaban kasa ya yi magana?

A yau idan ka duba, wadansu matasa da yawa  ba sa son su yi karatu, suna zaune haka kawai ba aikin fari bare baki, kuma wadanda suka yi karatu din, kashi 85 cikin 100 na masu son su sami  aikin gwamnati ne, ba sa tunanin ya za su kafa masana’antun da za su rika dogaro a kansu don ribantar rayuwarsu.

Ina iya tunawa akwai wani faifan bidiyo da na taba kalla na wani  mutumin Kenya  wata hirar da ya yi da dan jarida yana bayyana masa irin nasarar da ya samu a sana’ar da yake yi ta kiwon zomaye  bayan  ya gama karatun digiri dinsa a Jami’ a, kuma ya je ya yi Mastas dinsa ya dawo gida bai nemi aikin gwamnati ba sai  ya bude gonar kiwon zomaye.

A cewarsa ya fara kiwo da zomaye takwas ne, amma a yanzu ya ce yana da zomaye kusan miliyan uku, sannan kum daga cikin zomaye din nan, a bayanansa da ya yi, ya ce daga jikin wadannan zomayen akwai fitsarinsu da kashinsu da gashinsu, kusan kowane bangare na jikinsu yana da amfanin da yake yi wanda dan’adam ke bukatarsa.

A lokacin hirar, ya ce mutane na fitowa daga kasashe daban-daban na duniya ana zuwa a sayensu, wanda ya ce  hakan yana ba shi kudade masu yawa.

Saboda haka idan muka dawo nan gida, matasanmu ba su da irin wannan tunani. Domin idan ka debi matasanmu ka ba su jari su je su fara gudanar da sana’o’in su, da yawa wadansu  daga cikinsu za ka taras sun cinye kudin da aka ba su, domin matasan kasar nan ba masu jure wahala ba ne.

 

A kwanaki baya ‘Yan Majalisa sun yi barazanar tsige Shugaban kasa Muhammadu Buhari matukar bai aiwatar da wadansu kudurorin suka mika masa ba. We za ka ce?

Ba za  su ci nasara ba, don dukkan batutuwansu ba bisa gaskiya suke yinsu ba, sai dai kurum don biyan bukatunsu Amma ba don talakawan da suka zabesu suke yi ba.

 

Game  da matsalar rashin tsaro da fadace -fadace da ake samu nan da can cikin kasar, maye shawararka don magance su?

To lallai abin da ya shafi matsalar tsaro a kasar nan, Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana iyakar kokarinsa idan aka kwatanta da gwamnatin da ta gabata, karkashin shugabancin GoodLuck Janathan.

Kirana a nan shi ne, shugaban kasa ya yi tankade da rairayi a hukumomin tsaro na kasar nan don a sami cire duk baragurbin jami’an tsaro a kuma hukuntasu daidai da lafin da aka samu sun aikata.

Game da rikicin Fulani makiyaya da manoma kuma, shirin nan da gwamnatin tarayya ke yi na sama masu wuraren kiwo a duk inda suke, ya dace. Amma gwamnatin ta tabbata ta kafa hukumar da za ta rika lura bisa aiwatar da shirin don ta tabbatar ana aiwatar da shi tun daga matakin Kananan Hukumom zuwa jihohi har zuwa tarayya.

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ayyana 12 ga watan Yuni na kowace shekara ya zama ranar da za a yi bukin murnar kafuwar gwamnatin dimokurdiya a kasar nan maimakon 29 ga watan Mayu. Ya ka kalli wannan sauyi?

Hakan ya dace. Domin duk mutumin da y a kai jefa kuri’a a lokacin da aka gudanar da wannan zabe na ran 12 ga watan Yuni ya san Marigayi M K O Abiola ne ya lashe wannan zaben,sai dai kawai ba a bashi ba saboda wadansu dalilai da ba a bayyana wa mutanen kasar nan ba.

Amma ayyana Marigayi Abiola na shi ne mutumin da ya lashe zaben, wanda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi, ya kara nuna wa duniya Buhari Shugaba ne adali mai baiwa kowa hakkinsa.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!