Connect with us

ADABI

Salo Dokin Jigo: Tsokaci A Kan Wakar Kalubale Ta Akilu Aliyu (4)

Published

on

A makon da ya gabata mun tsaya  a baitin da ke nuna fa’idar ilimi. Yanzu za mu ci gaba kan yadda Dakta Salisu Garba Kargi ya yi fashin bakin kalmomin aikatau dan aji hudun da Fasihin mawakin ya yi amfani da su a wannan baiti.

Dagule: Abraham ( 1973:168) da Bergery (1993:190) da Jami’ar Bayero( 2006:86) sun gwada cewa, wannan kalma ce wadda take nufin bata ko lalata abu. Watau abu ya gama lalacewa gaba daya. Sarrafa wannan aikatau na gwada cewa, Akilu Aliyu, yana nufin ko da abu ya lalace gaba dayansa, ya gaggari sarrafuwa, ilimi na iya gyara shi kuma  a ci gaba da amfani da shi.

Kwakkwabe: Bergery (1993:664) da Jami’ar Bayero (2006:259) dama gari ko kasa da ruwa ko caba magana mara dadi. Bergery (1993) ya kara da cewa, idan aka ninka shi to yana nufin gaba dayan abin ya ya shafa bai rage komai ba. Misali: Lamarin ya kwakkwabe, watau gaba dayan lamarin ya lalace. ko kuma a ce: tuwo ya kwakkwabe, watau tuwo da miya sun hade har ya zama abin kyama. Ko kuma a ce: Ida nunsa sun kwakkwabe, watau idanunsa duk sun yabe da kwantsa. Shi kuma Zarruk (1996:29) ya ce ninki wani nau’i ne na karfafawa a cikin aikatau. Shi kuwa sarrafawa a cikin aikatau yana gwada tsanani ko karfi ko yawan aukuwar abu. Duk yadda bacin abu ya kai ga maimaituwa to ilimi zai iya gyra shi har a amfana da shi.

Dabalbale: Abraham(1973:159) da bergery (1993:176) da Jami’ar Bayero (2006) sun bayyana wannan kalma da ma’anar bibbirkita ko rikirkita aiki. Watau duk yadda abu ya kai ga rikicewa ko juyewa (birkita) ilimi zai iya gyara shi, ya warwashe kuma ya koma daidai.

Jagwalgwale: Bergery (1993: 486) ya ce shi ne yawan taba abu, babu gaira babu dalili wanda har zai kai abin ga lalacewa. Misali, ku daina jagwalgwala dan magen nan kada ya yi gabanya(ciwon tsinbirewa). Jami’ar Bayero(2006:211) kuwa, suka ce shi ne babbata abu da lalata shi. Watau a nan Akili Aliyu yana nufin cewa, duk yadda hannu ya shiga ya bata abu ilimi zai gyara shi. Hatta kuwa ciwon gabanya(Dwarfism). Redmond (2008) ya bayyana cewa, lilkitoci sun gano dalilansa da kuma hanyoyin magance shi.

Bergery (1993:) da Jaggar (2001:247). Sun bayyan cewa, irin wadannan rukuni na aikatau, suna bayyana matsanancin gurbatar halin wani abu ne ta yadda batun mai she shi asalinsa ko kyautata shi domin cin gajiyarsa abu ne da hankali, ba ya tunaninsa.

Wannan bayanai duk sun gwada cewa, lallai wannan Fasihi yana da fahimtar cewa, ilimi na iya gano abin da hankali ke ganin rashin yuwarsa. Alal hakika kimiyyar juya-bai ( re-cycling), watau fasahar sarrafa gurbatatun abubu zuwa sababbin abubuwa daban domin amfanin dan’adam, ta tabbatar da wannan fahimta ta Akilu Aliyu. A karkashin wannan fasaha Huang (2009) da John (2009) sun bayyana cewa, lallai a halin yanzu za a iya rarabe ruwa da duk wani abu da zai iya gurbata shi, tun daga ambaliyar mai ko dagwalon masana’antu ko sinadaran kamfanoni ko turbaya, da dai sauran abin da ke iya gurbata ruwa. Haka kuma Hartman (20090 ya kara da cewar,  ba wai ruwa ba kawai, hatta guntattakin karfe da alama ana juya su zuwa gwangwanaye da wayoyin wuta, haka kuma ana juya gurbatattun robobi wajen yin darduma da ledojin rigunan jaket ta tire ko faranti da matsefin gashi, ds. Sannan kuma da yadda ake juyar da rududdugaggun takardu da gilai zuwa sababbin takardu da gilasai da tayil na gyaran dakuna. A karshe kuma na juyar da  dagwalon man injina da fenti da tayoyi da kuma silinda.

Bugu da kari, ba wai abin da hankali ke ganin rashin yiwarsa ne kawai a yau ilimi ya gani ba, hatta ma abin da hankali ya gaza hararo shi, ilimi ya gano shi. Misali, samar da halittu masu rai kuma masu kama da juna ta hanyar fasahar dashen kwayoyin halitta( Cloneng), tamkar yadda Wilmut(2009) ya tabbatar da cewa, an samar da tagwayen ‘yan dalo (masu kama da juna ainun) a Jami’ar Kinki, ta jafan, a shekarar 1998. Da kuma yadda aka samar da wata ‘yan kyanwa mai kama da uwarta, a shekarar 2001, a Jami’ar Tedas, ta Amurka.

Daga wannan dan gajeren bayani za iya fahimtar irin gudummawar da wadannan rukuni na aikatau suka bayar, wajen kyautawa da zurffaf manufar sakon da kuma kara masa gwabe a zukatan jama’a.

Ribar Ilimi Ga Ma’abocinsa

Wannan fashi Akilu Aliyu ya jawo hankalin jama’a game da irin alhairan da ma’abota ilimi ke samu a dalilin ilimin nasu ga kadan daga cikin misalan wuraren da ya ambaci haka domin karin tabbas:

A yau koshi waye da she?

Mutan ilimi suka hamdale

Su waye masu fada a ji?

Da sun magana ta daddale.

A yau koshi wa ke da shi?

Mutan ilimi suka kammale (kbl:24-26).

Ga ma’anonin  kalmomin aikatau wadanda aka kaurara domin kara fito da manufar wannan Fasihi a fili karara domin samar da ingantacciyar fahimta ga jama’a:

Hamdale: Wannan Kalmar aikatau dan aji hudu na Kalmar hamdala wadda ke nufin godiya ga Allah( Bergry 1993:443) da Jami’ar Bayero (2006: 192). Ida aka danganta da manufar wannan Fasihi kuwa kalmara na nufin cikakkiyar godiya, wadda ba ta dauke da wani nakasu. Watau godiya da lafazi da zuciya da gabobi. Domin haka godiyar da aka yi ta bayyanar goshi da haram ko kuma an gamsu da tara haram. Na kasasshiya ce, Allah kuma babu ruwansa da irinta, haka kuma godiyar da ake furtawa amma gabobi ba sa aiwatarwa ita ma nakasasshiya ce. Do dukkan wadannan nau’in godiya mutan ilimi ne kawai suka san da su har suke kiyaye su, domin haka ma’abota ilimi su ne kawai suke iya tantance halas da haram a wajen nemansu da cinsu.

Sannan kuma su ne ke godewa Allah a mganganunsu kuma dogewa cikin biyayyar Allah da gabbansu, hakan kuma ita ce ta mayar da su cikakun mawadata. Duk wanda yake sabanin haka, to talaka ne kuma fakiri komai samunsa, domin kuwa godiyarsa ba ta da muhalli a wurin Allah tamkar dai yadda Aljaza’iri (199—) da Mahmud(1998:CDNO.1) ya tabbatar da haka.

Daddale: Daddale wanna Kalmar aikatau mai asali daga daddala, kamar yadda Kamusun Bergery (1993:181) da Jami’ar Bayero (2006:84) suka bayyana ita ce daddabe fura da tabarya ko lailaye dabe. To idan aka danganta ta da wannan muhalli sai ta zamo cewa, kamar yadda idan fura ta kai wanna mataki sai a sha kawai, haka idan mai ilimi ya yanke wani hukunci ya furta wata magana babu mai iya jayayya ko musantawa, saboda gaskiya da adalcin da ke ciknta da kuma tsabar amincewar da aka yi masa a cikin ala’umma. Haka kuma idan aka juya maganar lailayewa watau yadda ruwa ba ya iya samun kafar shiga har ya bata lailayayyen gini, hakan nan idan mai ilimi ya yi magana ba a iy a samun makurdadar batanci a cikinta saboda matsayin mai ilimi a cikin al’umma.

Kammale: Kammale ita kuma  Kalmar kammale kamar yadda Bergery(1993:546) da Jami’ar Bayero 229 suka bayyana tana nufin gama ko hada ko kuma karasa aiki. Idan aka danganta ma’anar da manufar wannan fasihi kuwa yana nufin cikakken girma’ Watau nau’in girman da ake cin gajiyarsa a nan duniya, sanna kuma ya gode har lahira. Domin kuwa duk wanda ya samu girma ta dalilin sarauta, iyakarsa duniya, haka kuma girma da dalilin dukiya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!