Connect with us

RA'AYINMU

Ra’ayinmu

Published

on

A ranar Asabar 23 ga Juni, 2018, ne jam’iyya mai mulkin Najeriya, APC, ta gudanar da babban zabenta na kasa, inda wakilai daga mazabu da jihohi su ka taru a babban filin taro ba Eagle Skuare da ke Abuja, don zaben sababbin shugabannin da za su jagoranci jam’iyyar a wani sabon zangon mulkin, inda tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiohmole ya zama sabon shugabanta.
Da fari jam’iyyar ta so ta ki gudanar da wannan zabe gabanin babban zaben kasa na 2019, saboda gudun kada rikicin cikin gida ya dabaibaye ta, alhali ga zabe a gabanta. To, amma wani kulli na karkashin kasa tsakanin jigon jam’iyyar na kasa, Bola Ahmad Tunibu, da shugaban kasa Muhammadu Buhari, da kuma kokarin bin doka da oda ya sa a ka jingine wancan tsari na fasa gudanar da zaben, duk da cewa har sai da a ka gudanar da taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar su ka kara wa shugabannin da ke ci a lokacin karkashin jagoracin Oyegun wa’adin zangon mulkin.
To, amma bayan zargin wancan tsari da yarjejeniya ta faranta wa yankin Kudu maso Yamma (wato yankin Yarabawa), sai Shugaba Buhari ya fito ya kalubalanci tazarcen shugabannin jam’iyyar ya na mai dogara da matsalolin da a ka iya tasowa a gaban kotuna, matukar ba a gudanar da halastaccen zaben shugabanninta ba.
Wasu sun nuna fargabarsu kan dawo da hannun agogon bayan da a ka yi, saboda tsoron barkewar rikicin zabe na cikin gida, musamman idan wasu ba su ji dadin tsarin ba ko kuma su ka yi zargin cewa an zalunce su. To, amma hakan bai hana mafi rinjayen masu ruwa da tsakin jam’iyyar, ciki har da Buhari, Tunibu, gwamnonin APC da sauransu goyon bayan bin tsari ba, wanda a zahirin gsakiya ya fi dacewa da kundin tsarin kasa da dokokin jam’iyyar koda kuwa wani zai iya ganin cewa an yi ne domin a faranta wa jigogin siyasar yankin Kudu maso Yamma da ke cikin jam’iyyar.
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya yi magana a madadin masu ruwa da tsakin jam’iyyar a wancan lokaci, ya nuna cewa, bai kamata tsoron tashin-tashina ya hana a ki bin doka ba, kuma da ma ita siyasa ai ta gaji hayaniya da rigingimu, in ji shi. Don haka APC za ta gudanar da zabe a kowane mataki, kamar yadda doka ta tanada.
Saidai kuma tun daga gudanar da zaben a matakin unguwanni a ka fara samun kace-nace da zarge-zargen juna. Haka nan da a ka kai mataki na mazabu abinda ya biyo baya kenan. Lokacin da a ka kai mataki na kananan hukumomi kuma sai abin ya sake ta’azzara, inda a ka fara samun masu yin tawaye da barazanar ficewa daga cikin jam’iyyar gabadaya. Rikicin ya kai wani mataki maras kyau ne a makon da a ka gudanar da zabukan jihohi, inda a ka rika samun masu fita daga cikin jam’iyyar dungurugum. Wasu su ka rika koma wa tsohuwar jam’iyyarsu ta APC, yayin da wasu kuma su ka rika shiga sabuwar jam’iyyar SDP. Tabbas wannan abu ne maras dadi, musamman kasancewar ya na faruwa ne ga jam’iyyar da talakan kasar ya ke da karfin gwiwa a kanta.
Tuni dai kurar PDP ta riga ta yi kuka, inda mafi yawan talakawan kasar har yanzu su ke fushi da ita. Ita kuwa SDP, saboda a na ganin ta tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ce ba a yi ma ta kyakkyawan zato. Wasu ma gani su ke yi kawai jam’iyya ce ta ’yan huce haushin Buhari. To, amma duk da haka masu hikima su na cewa, wanda ya fada ruwa ko takobi a ka mika ma sa kamawa zai yi. Don haka abu ne mai sauki rikicin ya iya daidaita APC, kamar yadda ita ma PDP rikicin cikin gida ya taimaka matuka gaya wajen daidaita ta.
To, amma za a iya cewa har yanzu ba a makara ba, domin wannan zabe da jam’iyyar ta gudana a mataki na kasa bakidaya har ta samar da sababbin shugabanni, su shugabannin su na aiki tukuru a gabansu na daidaita tsakanin jam’iyyar da wadanda a ka batawa. Su kuma ’ya’yan jam’iyyar ya na kyau a gare su da ita kanta jam’iyyar tasu da su daure su yi hakuri koda kuwa sun yi fushi, domin cigaba da irin wannan rikici a irin wannan mataki ya na da matukar hatsari ga jam’iyyar, domin zaben sababbin shugabanni a mataki na kasa shi ne karshen kowane irin matsayi na jam’iyyar.
Idan har ba a daina ko ba a dakatar da rikici bayan kammala zaben ba, to zai iya yin illa a cikin gidanta. Dole ne rarrashi wadanda a ka batawa koda kuwa har sun kai ga ficewa daga cikin jam’iyyar sun shiga wata daban. Ai neman biko ba laifi ba ne; nagarta ce ma. Don haka ya kamata a tausa!
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!