Ban Taba Yin Fim Kamar ‘Mutum Da Addininsa’ Ba –Maryam Habila — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

BIDIYO

Ban Taba Yin Fim Kamar ‘Mutum Da Addininsa’ Ba –Maryam Habila

Published

on


Jarumar shirin gagarumin fim din Hausa nan mai suna Mutum Da Addininsa, wato Maryam Habila, ta bayyana cewa, ba ta taba yin fim kamar shi ba, saboda irin sakon da ya kunsa da kuma wahalar da a ka sha wajen daukar sa.
Jaruma Habila ta bayyana haka ne a zantawarta da LEADERSHIP A YAU LAHADI ta na mai cewa, “ba shi ne fim dina na farko ba, amma babu fim din da na taka muhimmiyar rawa kamat wannan fim na Mutum Da Addininsa. An ba ni gurbin da ya dace ni sosai, kuma na taka rawa yadda ya kamata.
“Babban abinda ya fi birge ni da shi ne, an nuna yadda ya kamata dangtantaka ta zama tsakanin mabambantan addinai guda biyu. Ka ga na fito ne a matsayin Kirista wacce na ke tare da ’yar uwar babata, Ina iki da ita a gidan abinci. To, ta na gana min azaba, sai wani mai suna Abdulsalam, wato Ali Nuhu kenan, ya rika zuwa gidan abincin saboda tausaya min da ya ke yi ya na so na ba tare da la’akari da addinina ba, duk da cewa shi Musulmi ne. Wannan ne ya haifar da babban labarin fim din.
“Wannan fim din ba wai a kan soyayya kadai ya ke ba, domin sako ne wanda zai iya amfanar duk wanda ya kalla, musamman yadda zamantawa ta ke a nan Najeriya tsakanin Musulmi da Kirista.”
A yayin da ta ke bayani kan irin kalubalen da a ka fuskanta a yain daukar shirin, Maryam Habila ta yi bayanin cewa, “gaskiya an kashe kudi a fim din nan kuma na sha wahala wajen yadda a ke daukar sa daki-daki a kan sai kowa ya bayar da abinda a ke so, wato mu jaruman fim din. Ga shi kuma an yi tafiye-tafiye garuruwa, don a sami abinda a ke so.”

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!