Connect with us

TATTAUNAWA

Canza Ranar Dimukradiyya Bankaura Ce, In Ji Ango Abdullahi

Published

on

A cikin makon da ya gabatane shugaban Kungiyar Dattawan Arewa kuma tsohon dan takarar gwamnan jihar Kaduna a jam’iyyar S.D.P a zamanin su M.K.O Abiola kuma tsohon shugaban jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Farfesa Ango Abdullahi, ya yi wannan furuci a yayin da suke zantawa da wakilinmu da ke shiyyar Zariya, inda ya ce, “Ni a waje na canza wannan rana ba shi da wani amfani saboda mun san an yi hakan ne domin a wawushewa yarbawa kuri’unsu illa iyaka.
“Don in muka duba baya shima tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi haka a lokacin da yake nemawa kansa farin jini, sai ya kirkiri 29 May don dai ya samu karbuwa ga jama’ar da ya ke ganin barazana ne a gareshi a siyasance amma ba don kishin siyasar kasar nan ba.
“Don haka ina son duniya ta ji ta shaida a wajen dawo da ranar Damakaradiyya 12 June da karrama iyalan Abiola ban ga ya isa abun a zo a gani ba face kawai ana son rarukan kuri’un da ke hannun Yarbawa ne kawai kamar yadda wasu shugabanni suka yi a baya.
“Don haka a wajena in ma akwai wanda ya kamata a karrama bai wuce marigayi Musa ‘Yar Aduwa ba, domin shi ya kafa jam’iyyar S.D.P kuma shi ya tsayar da dantakaran da ya yi nasara har wasu suka sami bakin yin magana a siyasance kuma shine ya tsaya kyam wajen tabbatar da damakaradiyya a kasarmu Nijeriya.
“Kuma duk wani dan siyasa a yanzu yana cin gajiyar abin da marigayi Musa ‘Yar Adua ya dasa ne tare da wasu mutane kalilan a lokacin baya, idan jama’a basu sani ba su je su binciki tarihin jam’iyyu kamar su S.D.P da P.S.M da P.S.P da N.R.C za a fahimci rawar da wadancan mutanen suka taka wajan dawo da martabar damakaradiyya a Nijeriya wanda ke nuna cewa su ya kamata mu karrama ba kamar yadda lamari ya ke a yanzu ba.
“Dabi’ar da marigayin ya nuna ta sa bai kamata a manta da shi ba koda bashi a raye, don haka ne na yi watsi da dawo da ranar damakaradiyya June 12, Domin ni na san an yi hakan ne don a sami kuri’une wajen Yarbawa, to a yi mu gani.”
Karshe Farfesan ya yi fatan alkairi ga jama’ar kasa baki daya tare da rokon Allah ya kawo wa kasarmu zaman lafiya da kwanciyar hankali da tabbatar siyasa ta gari da zamu gane abin da zai kawo ci gaba a kasa baki daya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!