Connect with us

WASANNI

Dole Manchester United Ta Biya Sama Da Fam Miliyan 50 Kan Willian, Cewar Chelsea

Published

on

Bayan da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta yi fatali da fam miliyan 50 din da Barcelona ta kai tayi a kan dan wasa Wiliian, kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta bayyanawa Manchester United cewa idan ta na son sayen dan wasa Willian sai ta biya sama da fam miliyan 50.
A ranar Juma’a ne dai kungiyar Barcelona ta kai tayin kudi fam miliyan 50 ga kungiyar Chelsea domin siyan dan wasa Willian sai dai nan take Chelsea ta yi fatali da tayin inda ta ce farashin dan wasan ya fi haka.
Willian, mai shekara 29 a duniya wanda yakoma Chelsea daga kungiyar Anzhi Makhachkal ta kasar Rasha a shekara ta 2013 ya buga wasanni 236 sannan shine gwarzon dan wasan Chelsea a kakar wasan da ta gabata bayan ya zura kwallaye 13 a raga.
Mourinho dai ya na son sake aiki tare da Willian bayan da ya sayo shi a lokacin da ya ke Chelsea kuma ya na son Manchester United ta sake siyo masa shi sai dai har yanzu Barcelona bata hakura ba akan dan wasan kuma ana tunanin zata sake kai sabon tayin kudi.
Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona dai tanason siyan dan wasanne bayan da dan wasanta Iniesta yayi ritaya daga kungiyar yayinda itama Manchester United take son daukar dan wasan domin tunkarar kakar wasa mai zuwa.
Kungiyar Chelsea dai bata da burin siyar da dan wasan sai dai watakila Willian din zaiso barin kungiyar sakamakon har yanzu ba’a san makomar kociyan kungiyar ba, Antonio Conte zai cigaba da zama ko kuma zasu kawo sabon mai koyarwa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!