Connect with us

WASANNI

Najeriya Za Ta Farfado Nan Gaba, Cewar Shehu Abdullahi

Published

on

Najeriya takasa tsallakewa zuwa mataki na gaba bayan data sha kashi a hannun kasashen Crotia da Argentina duk da cewa tasamu nasara a hannun Iceland daci 2-0 a wasa na biyu da suka fafata a gasar.
“Ina da yakinin cewa zamu farfado sosai kuma zamu cigaba da dagewa don ganin tawagar yan wasan bata tarwatse ba har zuwa nan da shekaru hudu masu zuwa” in ji Shehu Abdullahi.
Ya cigaba da cewa “Nayi farin ciki dana wakilci kasa ta a gasar cin kofin duniya duk da cewa bamuyi nasarar fitowa zuwa zagaye na gaba ba amma kuma duk da haka muna yiwa magoya bayanmu godiya bisa goyon bayansu garemu”
Tawagar yan wasan na Najeriya dai zata cigaba da buga wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin nahiyar Africa inda zata buga wasa da kasar Sychelle a ranar 7 ga watan Satumba sannan kuma sai ranar 10 ga watan Oktoba inda zata karbi bakuncin kasar Libya.
Najeriya dai ta fito acikin rukunin daya hada da Argentina da Iceland da kuma kasar Crotia sai dai wasa daya tasamu nasara akai kuma hakan yasa bata samu damar fita daga cikin rukuni ba
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!