Sharhin Fim Din ‘Gidana’ — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

BIDIYO

Sharhin Fim Din ‘Gidana’

Published

on


Suna: Gida Na
Tsara Labari: Sulaiman Bello Easy
Kamfani: Daneji Studio
Shiryawa: Kabiru A. Yako
Umarni: Sulaiman Bello Easy
Jarumai: Shehu Hassan Kano, Nuhu Abdullahi, Hadiza Muhammad, Zainab Sharada, Maryam Abubakar, Ummi Katsina, Sha’aibu lilisco. Da sauran su.
Sharhi: Hamza Gambo Umar

A farkon fim din an fara da yin bayanin matsayin Alhaji, (Shehu Kano) inda wata murya (boice ober) ake bayanin cewa shi hamshakin me kudi ne, aka fadi sunan iyalan sa da kuma alakar dake tsananin sa da Naufal (Nuhu Abdullahi) wanda ya kasance dan dan uwan Shehu Kano ne.
An nuna Hajiya Safna (Hadiza Muhammad) tana zaune tana karin kumallo, sai ‘ya’yan ta mata su uku suka fito daga cikin daki suka bukaci yin karin kumallo tare da ita, daga nan sai sukayi fushi suka tashi suka shiga bangaren da mahaifin su yake zaune suka yi masa korafin basu yi karin kumallo ba, anan take ya sa suka zauna suka fara karyawa da nasa abincin sannan suka ci gaba da hira cikin raha da kaunar juna. A bangare daya kuma ‘ya’yan Alhaji wato shukura da lubabatu sun nemi admission a jami’a har ma Lubabatu da Shukura suna fatan a hada su aji daya saboda irin shakuwar da sukayi, yayin da Shukura (Zainab Sharada) take da burin da ace ya halarta to miji daya zasu aura ita da ‘yar uwar ta lubabatu, ba don komai ba sai don saboda irin shakuwar da sukayi. Wata rana Hajiya Safna suna waya da Naufal (Nuhu Abdullahi) sai ta bawa lubabatu suka gaisa yayin da sauran ‘yan matan ma su Nuriyya suka karbi wayar suna nuna cewa sun yi kewar sa a bisa tsahon lokacin da ya kwashe a kasar waje yana karatu, a wannan lokacin ne ya sanar wa da Alhaji cewa ya kusa dawowa gida domin yana gab da kammala karatun sa. Jin hakan ne yasa Alhaji ya sa Hajiya ta sanar da su Nuriyya maganar dawowar Naufal. Hakan ne ya jefa su Nuriyya farin ciki sai ya zama a sannan basu da wata magana sai ta dawowar Naufal. Akwai lokacin da Alhaji yaje ofishin sa ake gaya masa cewa akwai abokan kasuwancin sa da suka zo yin wani kasuwanci dashi, amma saboda baya nan sai abin bai yiwu ba amma duk da haka akwai kasuwancin da sukayi wanda aka samu riba har ta miliyan biyu, jin hakan ne yasa Alhaji yayi murna da aka samu wannan riba domin ya nuna shi mutum ne wanda ke da wadatar zuciya abu kadan ma yakan sanya shi murna. Ana haka ne admission din su Lubabatu ya fito suka fahimci basu samu course din da suka nema ba wato Medicine, fahimtar haka ne ya jefa su cikin kunci musamman Lubabatu har tafi shukura shiga cikin damuwa, hakan ne yasa mahaifin su ya tabbatar musu da zai bi duk hanyar da zai iya sama musu course din da suke so, jin hakan ne yasa suka kwantar da hankalin su.
Bayan wani lokaci Naufal ya dawo daga kasar waje, dawowar sa ce tasa su Nuriyya sukayi murna suka zauna tare dashi suka bashi labarin abubuwan da suka faru bayan tafiyar sai. A wannan lokacin ne Alhaji ya dauke shi suka fita yawon shakatawa daga bisani kuma sukayi zama na musamman Alhaji yayi masa bayanin yana son ya damka harkokin kasuwan cin sa ga Naufal, inda Naufal yake bashi labarin kwarewar da yayi a fannin iya kasuwanci. Jin hakan ne yasa Alhaji ya kara sakin jiki dashi akan maganar da sukayi.
Kwatsam wata rana shukura ta fito daga cikin daki ta sanar da mahaifiyar ta taga lubabatu a kwance bata motsi, bayan shigar su cikin dakin ne suka duba ta sai sai suka tarar ta mutu, hakan ne ya tashi hankulan mutanen gidan suka shiga damuwa aka sanar da jami’an tsaro halin da ake ciki, bayan zuwan su gidan ne suka yiwa mutanen gidan tambayoyi kowa ya fadi iyakar abinda ya sani, daga nan ne suka tafi don cigaba da gudanar da binciken su. Mutuwar Lubabatu babu jimawa sai Hajiya Safna ta tarar da gawar shukura a bandaki itama an kashe ta, hakan ne ya tashi hankalin ta aka sake kiran jami’an tsaro suka ji halin da ake ciki, anan take Naufal ya tunkude inspector (Shu’aibu Lilisco) bayan ya tunkude sa ne yake yi masa fada akan sun kasa yin aikin da ya dace gashi za’a kashe mishi ‘yan uwa. Nan take inspector ya fusata kuma ya gargadi Naufal akan kada ya sake kuskuren ci masa mutunci domin zai dau mataki akan sa, bayan ya fita ne Alhaji ya nunawa Naufal laifin sa kan abinda ya aikata kuma ya bukaci Naufal akan yaje ya bawa inspector hakuri. Bayan kwanaki kadan ne Hajiya Safna ta bawa mijin ta shawara akan a tuntubi malamai don aji dalilin da yasa ‘ya’yan su suke mutuwa, alhaji ya amince da shawarar ta kuma ya tura Naufal gidan wani malami akan ayi masa duba a fada masa abinda ke faruwa da har ‘ya’yan sa suke mutuwa. Lokacin da Naufal yaje gidan malami bayan malamin yayi duba sai yake fada masa cewa ba aljanu bane ke kashe jama’ar gidan mutum ne wanda ke tare dasu. Jin hakan ne yasa Naufal ya tsorata amma sai ya tashi ya tafi.
Babu jimawa da mutuwar ‘ya’yan Alhaji sai itama hajiya safna aka shiga har cikin daki aka kashe ta, hakan ne ya kara tunzura zukatan ‘yan sanda. Yayin da Alhaji ya tura aka sanar da ‘yar sa Nuriyya labarin mutuwar mahaifiyar ta da yan uwanta. Wata rana Alhaji suna zaune tare da Naufal sai wani dan daba ya shigo cikin gidan suka kama Alhaji suka harbe shi da bindiga nan shima suka kashe shi. A sannan ne kuma Nuriyya ta dawo daga makaranta ta shigo gidan ta tarar da gawar mahaifin ta a kwance a kasa. Bayan ta shiga daki a firgice ne taga Naufal da abokin sa a zaune cikin yanayin rashin imani, hakan ne yasa da Naufal ya kira ta bata je ba ta gudu. Daga sannan ne jami’an tsaro suka shigo gidan suka tarar da abinda ya faru sai inspector ya kira Naufal wanda anan take ya fada masa shi ya aikata duk kisan kan da akayi a gidan Alhaji kuma shi daga inda yake ma jirgi zai hau yabar kasar. Anan take inspector ya nuna masa duk inda zai je ma sai sun kama shi sun yi masa hukunci.

Abubuwan Birgewa:
1- An nuna kyakkawar mu’amula da soyayya wadda ta dace duk wani uba ya zamo yana nunawa ‘ya’yan sa.
2- An samar da wurare masu kyau wadanda suka dace da labarin.

Kurakurai:
1- A farkon fim din an ji (boice ober) muryar namiji wanda yake bayanin matsayin Alhaji da kuma sunayen ‘ya’yan sa. Bai kamata a yiwa mai kallo bayanin matsayin kowa ba, ya dace abar me kallo ya fahimci matsayin kowa daga yanayin tafiyar labarin.
2- Lokacin da Lubabatu bata samu course din da take son karanta ba, anga lokacin da Alhaji ya fada mata zai yi kokarin nema mata irin course din da take so, amma duk da jin haka bata nuna farin cikin ta ba, ya kamata aga lubabatu tayi murna da jin hakan, musamman a yadda aka nuna ta shiga damuwa har tana kuka.
3- Mai kallo yaga Nuriyya a cikin dakin su ta fadawa ‘yan uwanta cewa hand-out take karantawa, duk da a sannan ba’a nuna cewa ta shiga makarantar gaba da sakandire ba, shin hand-out din ta mecece? Idan kuma ta fara karatu ne ta dawo gida hutu ya kamata a fadi hakan ko da baki ne.
4- Ko sau daya mai kallo bai ga Nuriyya ta fita daga gida don zuwa makaranta ba, kuma ba’a nuna ta fara karatu ba, amma sai aka ji mahaifin ta yana tambayar ta ya hutun semester. Shin a gida take yin nata karatun ne?
5- ‘Yar Alhaji wadda ta fara rasuwa me kallo yaji ana ta kiran ta da suna lubabatu, har lokacin data rasu a sanda mahaifiyar ta taje duba gawarta sunan da aka ji ta kira ta dashi kenan, amma lokacin da inspector ya tambayi sunan wadda ta rasu din, sai yayar ta tace sunan ta shukura, shin mancewa tayi da sunan kanwar tata? Ita kuma wadda inspector ya tambaya sai tace sunan ta lubabatu, alhalin itace ake kira da shukura, shin me ya hargitsa sunayen nasu?
6- Farkon lokacin da aka nuna ‘yan sanda sun shiga gidan Alhaji don rubuta bayanan abinda suka faru, takardar da aka nuna jami’in tsaron yana rubutu tafi kama da script wanda ke dauke da labarin fim.
7- Lokacin da daya daga cikin ‘ya’yan Alhaji ta fara mutuwa, shin ya akayi su Alhaji suka gane cewa kashe ta akayi? Domin ba’a nuna alamun an bata guba ko kuma an kashe ta da wani makami ba. Kuma kafin su kira jami’an tsaro ya dace a fara kiran likita don ya tabbatar musu da dalilin mutuwar ta.
8- Bai kamata Alhaji ya tura Naufal wajen malam don neman dalilin mutuwar ‘ya’yan sa ba, ya dace ace shi da kansa yaje wajen malam din ko don saboda muhimman cin abinda ya faru da kuma yadda aka nuna yana matukar son ‘ya’yan sa.
9- Shin wane dalili ne yasa Naufal ya kashe Alhaji da iyalan sa? Ya kamata a samar da dalilin da yasa ya kashe su, koda ta hanyar cewa don ya mallaki dukiyar sa ne ko kuma dai wani dalilin mai karfi. Amma mai kallo bai ji an fadi dalilin Naufal na yin kisan rayuka ba.
Karkarewa:
Shin wane darasi fim din yake koyarwa? Fim din yayi rauni wajen rike me kallo, kuma babu wani sako a cikin sa.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!