Connect with us

RA'AYINMU

Batun Fasa Gidajen Yari Da Barazana Ga Tsaron Kasa

Published

on

D
aga watan Yuni na shekarar 2016 zuwa watan na Yuni na wannan shekarar ta 2018, an sami rahotannin fasa gidajen yarin kasarnan har sau shida, wanda hakan ya yi sanadiyyar arcewan wasu masu manyan laifuka har 268, gurbatattun mutane ne da kasantuwansu cikin al’umma hadari ne mai girma, domin kuwa mafiya ma yawansu duk suna zaman jiran kisa ne kasantuwan irin manyan laifukan da suka tafka zamanin da suke zaune a cikin al’umman. Na baya-bayan nan shi ne na gidan yarin Minna, Jihar Neja, inda fursunoni akalla 200 aka ce duk sun gudu. A wasu lokutan jami’an gidajen yarin sukan ce wai sun sami nasarar kama wasu daga cikinsu, wanda fadin hakan sam ba ya sanya wa hankulan al’umma su sami natsuwa, don kuwa kowa ya san hadarin da kasantuwar irin wadannan gurbatattun cikin al’umma yake da shi.
Ko ka ce, Kurkuku ko ka kira su gidajen Yari, duk ma’anarsu guda ne a harshen Hausa, ma’anarsu shi ne, wuraren da a kan killace mutanan da kasantuwarsu a cikin al’umma yake da hadari. Wurare ne kuma na bayar da horo ga wadanda suka aikata laifin da ya wajaba a ja masu kunni na musamman ko kuma an ajiye su ne a wurin kan laifin da suka aikata kafin a yanke masu hukunci. Ana kuma iya kiransu, wuraren gyaran halaye, watau an ajiye masu halin da bai dace da zamansu cikin al’umma ne ba a wajen domin su gyara halayyan nasu su dawo cikin al’umman a matsayin mutane nagartattu marasa hadari. Baya ga yadda ake yi wa gidajen yarin gini na musamman irin wanda ake kwatanci da, ‘Katangan karfe,’ a kan kuma sanya Jami’an tsaro na musamman wadanda aka ba su horo na musamman kan yadda za su kula da wurin da kuma masu laifin da ke cikinsa. Amma wai duk da hakan ne, irin wadannan baragurbin masu matukar hadari a cikin al’umma sukan sami hanyar sulalewa ko su busa su balle su sake kunno kai a cikin al’umma. Wanda a kodayaushe hakan ke matukar tayar da hankulan al’umma.
Masana, da suka hada da jami’an tsaro, ma’aikatan sashen shari’a, manazarta tunanin kwakwalwa da sauran ma’aikatan da ayyukansu ya shafi kyautata rayuwar al’umma, sukan sha mamakin yadda hakan ke aukuwa, wanda yawan aukuwan hakan yakan baiwa kowa tsoro, musamman ma dai a yanayi irin namu a nan Nijeriya. Manazartan sau da yawa sukan dora laifin aukuwar hakan ne kan dalilai masu yawa, kamar na yadda a kan cusa fursunonin da yawan nasu ya wuce ka’ida a gidajen yarin, wanda kuma hakan ke haddasa jinkirta zartar da hukunci, ga kuma karancin su kansu jami’an tsaron gidajen yarin, rashin samar da kayan aiki irin na zamani wajen tafiyar da gidajen yarin, rashin samar da horon da ya kamata ga su kansu kalilan din jami’an tsaron gidajen yarin da suke nan, uwa-uba rashin isassun kudaden da za a yi abin da ya wajaba a gidajen yarin da akalla zai iya nu na su a matsayin wuraren da suka dace da zaman dan adam.
Babban abin damuwar ma shi ne, a duk lokacin da aka ce an fasa gidan yari, tilas sai ka sami gigita da razana ga sauran al’umma kan halin da za a shiga kan batun tsaro, domin hakan ya nu na manyan masu laifi sun karu kenan a cikin al’umma. Don magance hakan, akwai shawarwarin da ake bayarwa na yadda za a inganta gidajen Kurkukun da muke da su, ta yadda duk wani yunkuri na a fasa ko a busa su, ba zai yiwu ba. Mafi mahimmanci cikin irin wadannan shawarwarin ita ce lura da cewa, kusan duk gidajen Kurkukun da muke da su sun tsufa, domin kuwa kusan tun zamanin turawan mulkin mallaka ne aka gina su, a hakan kuma suke har kawo yanzun ba wani canji, wanda hakan yana daga cikin yawan cinkoson da ake samu a cikinsu, da kuma karantar kayan more rayuwar da ke cikinsu.
Abin takaicin ma shi ne, irin fahimtar da jami’an da ke kula da gidajen yarin suke da shi, bai bambanta ba sosai da na su kansu tsararrun da ke cikin gidajen yarin, saboda wasu daga cikinsu tun farawansu da aikin har barinsu, ba wani sabon horon da suka samu face dai na yau da kullum da suke tsinta a cikin gudanar da aikin nasu. Amma a ta fannin kyautatawa kuwa, jami’an gidajen yarin sun fi morewa fiye da su kansu tsararrun. Hakanan kasantuwan gidajen yarin a cikin gari tsakiyar jama’a, shi ma yakan taimaka wajen yadda ake yawan fasa gidajen yarin a tsere.
Za mu iya tuna irin godon da gwamnatin Jihar Legas ta yi ta yi ga gwamnatin tarayya kan ta dauke gidan Kurkukun Ikoyi daga wajen da yake a halin yanzun zuwa wani wajen na daban. Misalin yanayin gidajen yarin da ke Ikoyi, Enugu, Owerri da sauran tsaffin garuruwa, sam kayayyakin da ke cikin su ba su dace da bukatar zamanin da muke ciki ba a halain yanzun. Sannan kuma duk da kankantan su, ba kuma ta yadda gwamnati za ta yi tunanin iya cewa wai a fadada su. Ko ma da hakan, ai ba dubara ce ba a fara fasa gidajen yarin da sunan za a fadada su, alhalin ‘yan fursunan suna zaune a cikinsa.
A namu shawarar, abin bukata a nan shi ne, a yi kokarin gina wasu sabbin gidajen yarin wadanda kuma suke dauke da dukkanin kayan bukata a cikinsu irin na daidai da zamanin da muke ciki yanzun. Daga cikin matsalolin da gidajen yarin namu ke fuskanta akwai batun cinkoso, wanda hakan kan tilasta a rika hada manyan masu laifi da kananan masu laifin, kila ma wadanda ake tuhuma ne kawai, suna jiran a yanke masu hukunci ne, wanda a karshe a ma iya samun su ba tare da aikata laifin komai ba. Shi ma tafiyar hawainiyar da ake yi wajen yanke hukunci a kotunanmu, yana daga cikin matsalolin da suke kara dagula lamarin. A lokuta da yawa, sai ka ji wai ance babu ma motar da za ta kai fursuna kotu, ko kuma ka ji an ce, an canza ma mai gabatar da karan wajen aiki.
A wasu lokutan kuma, kotunan ne ko alkalan za ka ji an ce suna cikin hutu, ko a ce mai gabatar da karan ne yake can yana hada wasu bayanai, domin a sami zartar da hukunci mai sauki. Mun ji duk akwai hakan. Amma dai duk hakan ba zai taimaka wa shari’ar ba, ba kuma taimako ne ga su kansu fursunonin ba, wadanda ake barin su cikin wata wahala ta ba gaira ba sabar, wanda ke kai ga su shafe lokaci mai tsawo fiye ma da kila lokacin da in an yanke masu hukunci za su shafe a tsare. Hakan kuma ba taimako ne ga gidajen yarin ba, da kuma jin dadin su kansu ‘yan fursunan. A ra’ayin wan-nan Jaridar, fasa gidajen yarin da ake abin bakin ciki ne da takaici, halin kuma da su kansu gidajen yarin ke ciki da na jami’ansu a halin yanzun duk shi ma abin takaici ne. Wannan kuma shi ke kara bayyana irin barazanar tsaro da ke kara jefa razani a zukatan ‘yan kasa nagari.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!