Connect with us

MAKALAR YAU

Domin El-Zaharaddeen Umar: Kilomita 525 Zuwa Katsina

Published

on

Tun kafin watan azumi El-Zaharaddeen Umar ya sanar da ni batun aurensa, an so a kulla cikin watan Musulunci na Sha’aban, amma Allah bai nufi hakan ta faru ba.
Ko da aka tashi sanya ranar bukin, sai ya zama bayan Sallah da ‘yan makonni, wato wannan Asabar din da ta gabata.
Ina daya daga cikin mutanen da halartar wannan aure ya zamar wa kamar wajibi; wajibi a wurin da aka daura halartar a babin sanin ya kamata da zumunci.
A wani lokaci can shekarun baya haduwarmu ta farko ta kasance da El-Zaharaddeen a Katsina, bisa gayyatar da Malam Danjuma Katsina ya yi min, don yin aiki a kamfaninsa na ‘Matasa Media Links’. A wancan lokaci, kamfanin zai fara wallafa Mujalla wacce aka ba suna ‘Mujallar Matasa’.
El-Zaharaddeen na daga cikin manyan hadimai, kuma babban fulogi a Matasa Media Links. Don haka ko da na isa Katsina, shi ya dauke ni, ya kai ni na ci abinci a wurin sayar da abinci na ‘Shekina Restaurant’ da ke kofar kaura.
Tare da shi muka fara aikin Mujallar Matasa a shekarar 2008 har zuwa lokacin da ta daina fitowa a shekerar 2010. Da yake yana da kwarewa a harkar da ta shafi kwamfuta, na’urar daukar hoto da sauransu. Sai ya kasance duk wani abu da ya shafi hoto a mujallar shi da Umar ke yi.
Ko da Mujallar Matasa ta daina fitowa, ba mu bar zumunci da El-Zaharaddeen. Saboda aikin ya kulla wata alaka ta musamman, wacce ke cike da ‘yan uwantaka a cikinta. An zama ‘yan uwan juna da ake shawarwari da sauransu, don samun mafitan rayuwa.
Na jima ina zolayarsa kan maganar aure. Ko ba komi, na san ba dai kin auruwa yayi ba, balle mu kai tallarsa gidajen rediyo ko talabijin da jarida. A kanshi na yarda da zancen hausawa da ke cewa, aure dan lokaci ne. Wasu ma sun ce, kamar layin markade ne, idan layi ya zo kan ka sai an yi ma.
Na kan gama aikin ofis ranar Laraba da daddare, don haka hutuna na fara wa daga Alhamis; abin da na su shi ne na kama hanyar Katsina tun Alhamis din, amma da yake ina da wata jarabawa, sai na bari sai da na fito sannan na kama hanyar tafiya Kaduna da misalign karfe 5:00 na yamma.
Tun da yammacin wannan ranar Alhamis muke waya da abokan arziki daga Katsina. Wasu ma zolayarsu na yi ta yi akan ba zan halarci daurin auren ba. wasu kuma ce musu na yi ai ba a gayyace ni ba, don haka bana zuwa.
Hanyar da na biyo daga Gwagwalada zuwa Zuba, wato Babbar Hanyar Lokoja, Abuja da Kaduna. Hanya ce dake cike da shingen ‘Yan Sanda. Duk inda ka bi sai sun tsayar da kai sun yi ma maula cikin magiya. Akwai ma wanda suka tsayar da ni, dan sanda kwararre ne wurin maula. Cikin abubuwan da ya fadi min har da cewa wai kishi yake ji, na taimaka mishi da abin da zai sayi ruwa ya sha. Wannan ya san a duba na lalubo Naira 50 na mika mishi. Abin mamaki kawai sai ya ce min, ‘Idan za ka min kyauta, ka yi min daga zuciyarka.’ Ma’ana dai ya raina. Ni kuwa na ce mishi, rainawa ka yi. Sai ya ce, eh. Sai na ce, toh ba ni abu na, ai kuwa Bawan Allah ya miko min, na ajiye Hamsin dina, na mayar da giya lamba daya na kara gaba.
A Kaduna na kwana. Da sanyin safiya, ko Karin kumallo ma ban tsaya yi ba, na kama hanyar Katsina. Daga Kaduna zuwa Zariya komi daidai, ina tafiya ni kadai, sai sautin da ke tashi, idan wakar M. Sharif ta shigo ta fita, sai ta wani ta shigo. wasu mawakan ma ban sansu ba, amma kuma muryoyinsu na kwance cikin wayata.
Asalin tafiyar, ya kamata a ce mun yi ta ne da Editan Ayyuka na Musamman na LEADERSHIP A Yau, Malam Abdullahi Usman Tumburkai. Saboda ya san hanyar Katsina matuka. Na so a ce na bi bayanshi ne, don tafiyar ta zo min da sauki. Hakan bai yiwu ba saboda wani uzuri na daban da ya tilasta mishi tafiya tun ranar Juma’a.
Rashin sani da tsautsayi ne suka taru suka ingiza ni na bi ta hanyar Dabai, zuwa Kafur zuwa Malumfashi. Duk yadda ka kai ga annushuwa da farin ciki, sai wannan hanya ta bata ma rai. Tun da nake a duniya ban taba ganin lalatacciyar hanya irin wannan ba. A wulakance take, kai ka ce ba mutane ne ke bin ta ba. A haka na yi ta zurmawa cikin ramuka, ban taba tsammanin cewa zan kai Katsina ba tare da tayoyina sun yi bindiga ba. Na shiga Katsina cike da haushin wannan hanya, ga kuma haushin karon da wani dan tasi ya yi min a daidai Malumfashi.
Abu mafi dadi shi ne, ko da na isa kofar kaura, inda kamfanin Matasa Media Links ke da ofis, na hadu da abokan arziki, kuma ‘ya’yan wannan kamfani; irinsu Adamun Adamawa, Umar A. Umar, Ibrahim El-Tafseer, Zahraddeen Sirajo, Abdullahi Usman TUmburkai, Muhammad Sakafa da sauransu sai na ji wadancan abubuwan ban haushi sun gushe.
Ango kuwa duk da bukinsa ake yi, bai manta da hidimar da ya saba ba. Shi ya kai mu muka ci abinci. har ina zolayarsa da cewa a yanzu shi dan gidan Gwamna Masari ne, komi ma sai ya yi ai.
Bayan mun ci abinci mun koma ofis din Matasa Media Links sai Uban Ango ya karaso, kuma Shugaban kamfanin, Malam Danjuma Katsina, nan dai aka sake gaisawa. Saboda wata haduwa ce da aka dau tsawon zamani ba a yi ta ba.
Da ni da Adamun Adamawa, Abdulaziz Kwanarya, da Abubakar Isah Hassan muka tafi Charanchi domin kwaso kayan amarya da ‘yan uwanta da za su yi jere a gidan ango. ko da aka ta shi komawa cikin garin Katsina, sai ya zama dukkansu sun shiga motar kwaso kaya; Adamun Adamawa da Kwanarya ma saman a-kori kurar suka hau. Ni kuma na kwaso matan da za su je su yi jere. Da kyar da magiya suka taimaka wurin takaita adadin wadanda zan kwasa, saboda mota ta ba za ta juri dibar mutane masu yawa ba.
Ita ma hanyar Charanci zuwa Katsina da ban haushi take, saboda ramuka sai ka zabi wanda ya dace ya fada cikinsa.
A ranar Asabar din muka kama hanya zuwa Charanci inda aka daura aure. Nan ma mun hadu da abokan arziki sosai. A can ne na hadu da wakilinmu na Katsina, Malam Sagir Abubakar, mutumin kirki.
Sai da muka tabbatar an kulle El-Zaharaddeen da amaryarsa Aisha Ibrahim, sannan muka kama hanyar komawa gida. Saboda tsaro da tsoron wannan muguwar hanya da na bi a zuwa, sai na bi bayan Abdullahi Usman, inda ya nuna min hanyoyi masu dama-dama da aminci.
Allah ya tabbatar da alheri a wannan aure, ya kawar da dukkan sharri. Aameen.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!