Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Safarar Karuwai: Birtaniya Ta Yankewa ‘Yar Nijeriya Zaman Gidan

Published

on

Shugabar hukumar yaki da safarar mutane ta kasa NAPTIP uwargida Julie Okah-Donli, ta bayyana hukuncin da aka yankewa wata ‘yar Nijeriya mai suna Josephine Iyamu mazauniyar kasar Birtaniya akan safarar mutane cewar abu ne mai kyau.
Uwargida Julie Okah-Donli ta yaba da hukuncin ne a sanarwar da ta fitar a garin Abuja tace hukuncin da kotun da Kotun Birmingham Crown dake Birtaniya ta yanke wata dama ce da zata baiwa hukumar ta kwarin gwaiwa don cafko saurran yan Njieriya da suka yi safarar yan Nijeriya zuwa kasahsne waje don hukunta su kamar yadda dokar Nijeriya ta tanada.
Acewar ta, tare da hadin gwaiwar sauran masu ruwa da tsaki dake kasashen duniya, hukumar zata kara kaimmi wajen ganin an zakulosauran yan Nijeriya da suka yi safarar mutane zuwa kasashen waje.
Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito cewar, NAPTIP da takwarar ta NCA sune suka cafke Josephine IIyamu a karkashin shirin su na hadaka na yaki da safafar mutane na iyaka da iyaka JBTF.
Uwargida Julie Okah-Donli taci gaba da cewa, wannan shine karo na farko da aka fara yanke hukunci ga ‘yar Nijeriya da ta yi safafar mata biyar don yin karuwanci.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!