Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

EFCC Ta Gurfanar da Tsohon Shugaban Tattara Kadaden Shiga Na Gombe Kan Wawushe Miliyan 25.6

Published

on

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa wato (EFCC) a Talatar nan ne ta gurfanar da tsohon shugaban hukumar tattara kudaden shiga na jihar Gombe ‘Gombe State Board of Internal Rebenue’ hade da wasu ma’aikata uku na ma’aikatar a gaban kotun tarayya da ke zamanta a jihar Gombe a bisa zarginsu da wawushe miliyan ashirin da biyar da diko shida (N25.6m).

Wadanda aka gurfanar a gaban kuliyar dai sune; Atiku Mu’azu Bayum shugaban hukumar tattara kudaden shiga a jihar Gome; Mohammed Adi babban jami’in da ke kula da dakin adana kayyaki, Ibrahim Abubakar babban Akanta, da kuma Abubakar Usman wanda yake Darakta a bisa laifin wawashe kudaden ta barauniyar hanya.

EFCC ta gurfanar da mutunan ne a karkashin mai shari’a Justice M. G Umar, na kotun tarayya ta daya dake Gombe, kan zarginsu da yin amfani da takardun karya na kasashen ketare domin cire wadannan kudade da suka kai N25, 060, 000.00 mallakin gwamnatin jihar Gombe.

EFCC ta bayyana wa kotun cewar aikata wannan laifin ya saba wa sashi na 1 (1)(a) da 1 (3) da ke ‘Adbance Fee Fraud and other Related Offences Act, 2006’.

Dukkanin wadanda ake zargin sun karya dukkanin zarge-zargen da EFCC take musu a gaban kotun.

Lauyan EFCC O. Israel, ya bukaci wata rana domin ci gaba da bayyana shaidunsu kan karar da suke yi.

Inda kuma lauyan kariya ya nemi shigar da takardar bayar da belin wadanda ake zargin.

Da yake yanke hukuncinsa kan bukatar bayar da belin wadanda ake zargin, Justice M. G Umar, ya amince da bayar da belin wadanda ake zargin kan naira miliyan (2m) ga kowannensu, hade da kawo mutane biyu-biyu muhimmai da za su tsaya wajen amsarsu beli.

Daga cikin muhimman mutane biyun da za su gabatar wajen cike sharadin belin, dole daya daga cikin biyun ya kasance ma’aikacin gwamnati wanda mukaminsa bai yi kasa da Darakta ba.

Kotun ta dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 11 ga watan Oktobar 2018 domin ci gaba da sauraro.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!