Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Mataimakin Shugaban Gidan Yari Ya Fada Komar ’Yan Sanda Kan Zargin Fashi Da Makami A Inugu

Published

on

Rindinar yan sanda ta jahar Enugu ta cafke mataimakin shugaban gidan yari Mista Collins Ugwu a bisa zargin samun hannun sa a cijin yin fashi da makami.

Ugwu, dan asalin yankin Ezza dake cijin jahar in Ebonyi, nazauni ne a garin Abuja, inda yake yin aikin sa a shakwatar ta gudan yari an kuma cafke shine a Enugu a ranar 26 ga watan yuni tare da kani mai suna Ifeanyi Ozor, da ya fito daga jahar Enugu wanda kuma yake da zama a Abuja sai kuma wani mai suna Smart Osetu da ya fito daga yankin Oguta cikin jahar Imo kuma mazaunin Abuja.

Kwamishinan yan sanda na jahar Mohammed Danmallam ne ya sanar da hakan a lokacin da ya yi bajin kolin wadanda ake zargin,inda ya ce an cafko Ugwu ne tare da wadanda ake zargin bayan samun bayanan da rindinar ta samu bayanan sirri akan su.

Acewar sa gungun nasu suna tsayawa ne wuraren bankuna idan mutane sun dauko kudi sai su bisu su kwace ko kuma su bisu har gindin motocin su fasa kofar mutocin a cikin wayo su sace masu kudi har ila yau, suna daga cikin gungun masu sayen kayan sata.

Ya kara da cewar an cafke su ne a kan titin Ogui dake Enugu a ranar 26 ga watan Yuni 2018, an kuma kwato mota kirarar Golf mai cauke da lambar Abuja RBC 220 KF, da kuma fasasshen fulogi da suke amfani dashi don aikata ta asar su.

Duk kokarin yan jarida nasu ji ta bakin Ugwu amma yaki yin wani bayani, musamman ganin cewar shi babban jami in gwamnati ne da aka dora masa alhakkin kare rayukan alumma.

A karshe kwkmishinan ya ce Ugwu da abokan sa suna bayar da hadin kai akan binciken su da ake yi kuma in an kammala, za a maka su a gaban kotu.

 

 

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: