Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

An Damke Wanda Ake Zargi Da Kashe Shugaban APC A Imo

Published

on

Jami’an rundunar ‘yan sanda na tawagar yaki a fashi da makami , ta kama wadanda ake zargi da kashe wani babban gizo na jam’iyyar APC ta jihar Imo, Amos Akano.

Shi dai Akano an sace shi inda aka yi garkuwa da shi, kafin ayi zaben shugabanninn jam’iyya na kasa,amma kuma bayan ‘yan kwanaki sai aka samu gawar shi, bayan an kashe shi.

An dai samu labarin cewar ita rundunar ‘yansanda ta musamman FSARS  a karkashin shugabancin Godfrey Bictor, sun samar kutsawa cikin ‘yan ta’addar ne, lokacin da suke jiran su samu nasu kason, daga ‘yanuwan marigayin.

Kamar yadda kwamishinan ‘yansanda na jihar Dasuki Galadanchi, su dai wadanda ake zargi da aikata laifin an kamasu ne a Ihiala, cikin jihar Anambra.

Kwamishinan ya bada sunayensu kamar haka, Ikenne Nwosu,aka  Ezego Chibuke Martins, Emeka Eke,Chijoke Akurara, da kuma Adubuokwu Chibueze, ya ce, su ‘yan ta’addar suna harkokinsu tsakanin jihohin Imo da kuma Anambra.

Galadanci ya kara da cewar kama su wadanda ake zargi da aikata laifin, wani babban ci gaba ne wajen yaki da ake yi da masu aikata laifuka a jihar.

Kwamishinan ya ci gaba da cewar ‘’ Ina mai sanar daku cewar an kama mutane biyar, wadanda ake zargin sun yi garkuwa da kuma kashe wani mutum da ake kira Amos Akano.

‘’Ita dai wannan kungiya ta mnasu aikata laifi tana amfani ne da Mgbidi a Oru ta gabas, wajen da suke boyewa, sun kusa amsar nasu kason kudin, daga wurin ‘yanuwan shi wanda aka kashe, wanda yanzu marigayi ne, aka yi masu zobe aka kama su a Ihiala cikin jihar Anambra.

‘’Suma sauran ‘yan kungiyar musamman ma shugaban nasu, an kama shi ne ta hanyar dabara ta kwarewa, dangane da aikinsu na jami’an tsaro.’’

Shi dai kwamishinan ‘yansandan ya sha alwashin yaki da masu aikata laifuka, musamman ma garkuwa da jama’a a jihar, ya canza yadda jami’an tsaron suke tafiyar da aikinsu, ba ma kamar wdanda aka san aikinsu yana da muhimmanci sosai.

 

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!