Gwamna Tambuwal Ya Rushe Kwamishinoninsa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Gwamna Tambuwal Ya Rushe Kwamishinoninsa

Published

on


Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya rushe Majalisar Zartaswar Gwamnatinsa a cikin matakin gaggawa.

Rushewar na da manufar gyaran bawul tare da sake tsara kakkarfar Majalisar Zartaswa domin gudanar da aiki yadda ya kamata ga al’ummar Jihar Sakkwato.

Wannan bayanin yana kunshe ne a cikin bayanin da Kakakin Tambuwal, Malam Abubakar Shekara ya fitar da Yammacin jiya Laraba.

Bayan ya godewa Kwamishinonin kan sadaukar da kai, biyayya da kwazo ga Gwamnatinsa, Gwamnan ya bayyana godiyarsa ga al’umma kan hadin kai da goyon bayan da suka baiwa ‘Yan Majalisar Zartaswar masu barin gado kan nasarorin da aka samu.

Kamar yadda bayanin ya nuna, Kwamishinonin za su hannunta lamurran gudanarwar ma’aikatansu ga Manyan Sakatarori. Haka ma Tambuwal ya mika sakonsa na fatar alheri gare su a dukkanin lamurran da suka sa a gaba a rayuwa.

Tun dai bayan nada Kwamishinonin bayan zaben 2015, wannan shine lokaci na farko da Tambuwal ya rushe Kwamishinonin lamarin da jama’a da dama ke ganin ba ya rasa nasaba da gabatowar Babban Zaben 2015.

Advertisement
Click to comment

labarai