Lauya Ta Wanke ’Yar Sanda Da Mari A Abuja — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Lauya Ta Wanke ’Yar Sanda Da Mari A Abuja

Published

on


A jiya ne wata lauya mai suna, Abibatu Lawani, ya gurfana a gaban kotun yanki mai daraja ta daya dake Kubwa a bisa laifin kai wa wata ‘yar sanda hari ta hanyar wanke ta da mari. Wanda ake zargin na fusakantar tuhumar laifin kai wa ma’aikacin gwamnati hari a bakin aiki da kuma kin amsa tambayoyin daga ma’aikacin gwamnatin dake a bakin aiki.

Mai gabatar da karar, John Okpa ya bayyana wa kotu cewa, wanda ake zargin ya tare kofar shiga inda ake tsare masu laifi ne dake ofishin ‘yan sanda a kubwa a ranar 2 ga watan Yuli yana waya ba tare da saurara wa ba.

Ya ci gaba da cewa, a lokacin da aka bukaci wanda ake zargin da ta bar wuri sai kawai ta kai wa ‘yar sanda mai mukamin sajan Precious Ugwu, wandda take a bakin aiki a dai dai lokacin.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!