Wata Sabuwa: Tawagar Su Kwankwaso Ta Bayyana Matsayarta A APC — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

MANYAN LABARAI

Wata Sabuwa: Tawagar Su Kwankwaso Ta Bayyana Matsayarta A APC

Published

on


  • Ku Ba Ni Lokaci, Zan Daidaita Komai –Oshiomhole

Wani bangare daga cikin jam’iyya mai mulki ta APC wadanda an yi imanin cewa suna samun goyon baya daga wasu jiga-jigan gwamnatin da ke kokarin dakile yunkurin shugaban kasa Muhammadu Buhari na yin ta-zarce a shekara ta 2019, sun ayyana kafa wata sabuwar jam’iyya.

Kungiyar ta bayyana cewa  su ne “sahihan ‘yan APC” kuma  kungiyarsu ita ce ma fi cancanta

Sun  bayyana hakan ne a wani taron manema labaran da aka yi a jiya Laraba cewa, kungiyar ta kunshi ‘yan sabuwar PDP da bangaren APC da ANPP da kuma ACN.

Tsohon sakataren CPC Buba Galadima,ne ya yi wa taron ‘yan jaridar jawabi sannan a tare da shi akwai tsohon minsta kuma shugaban sabuwar PDP, Kawu Baraje.

Galadinma ya ce sun yanke wannan shawarar ce sakamakon rashin cika alkawarin da wannan gwamnati ta yi, musamman ma na rashin daukar matakin da ya kamata ta dauka domin kawo karshen kashe-kashen da ake fama da su a kasar nan.

Haka kuma ya bayyana zaben da jam’iyyar APC da ta ce ta yi na shugabanninta da cewa nadi kawai ta yi, domin ba wadanda suka cancanta su yi zaben ba aka ba su damar ta zaben ba, haka kuma ya zargi gwamnatin Buhari da cewa, kullum ba ta da wani aikin yi sai maganar yaki da cin hanci.

“Wannan gyaran da za a yi wa jam’iyyar APC an fara da kafa kwamitin gudanarwa. Saboda haka mun tara ku a nan ne domin mu bayyana muku irin halin da wasu suka jefa jam’iyyar APC a ciki. Idan za a iya tunawa a zaben shekarar 2015 wasu jam’iyyu sun kulla kawance, suka kafa wata sabuwar jam’iyya wadda aka kirata da APC. An kulla wannan kawancen ne, saboda an tabbatar da cewa, Nijeriya ta tsinci kanta a cikin wani hali, wanda al’ummar kasar ke cikin wani mummunan hali,” in ji Galadima.

‘Yan Nijeriya sun zabi APC saboda alkawuran da ta dauka da kuma tunanin cewa za ta cika wadannan alkawura.Muna bakin cikin halin da muka tsinci kanmu bayan shekara uku da fara wannan mulki babu wani abin kirki da ta kulla. Sai ya zama jam’iyyar APC ta kafa gwamnatin da ba ta iya hassala komai, ya zamana ta gaza wajen gudanar da dukkan al’amuranta. Sai dai kawai mulkin kama-karya da kuma yi wa tsarin mulki karan-tsaye.Haka kuma gwamnatin ta gaza wajen shawo kan matsalar tabarbarewar harkokin tsaro a wannan kasa.”Akwai kuma rahotannin da ke yawo cewa ‘yan sabuwar PDPT na shirin fita daga zuwa PDP.

Daga cikin jiga-jigan sabuwar PDP akwai shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara, da kuma tsohon gwamnan jihar Kano Rabi’u Kwankwaso.

An kira mai magana da yawun Saraki da na Dogara a jiya Laraba domin jin ta bakinsu, amma ba wanda ya amsa kiran. Haka kuma an aikawa da Yusuf Olaniyonu  mataimakin shugaban majalisar dattawa na musammam a kan harkokin yada labarai da Turaki Hassan, na  Mista Dogara, dukkansu babu wanda ya bayar da amsar sakon da aka aika masa.

Bayyanawarta kungiya da za ta yi gyaran fuska a jam’iyyar APC matakin farko ne na samar da wata sabuwar jam’iyyar da za ta yaki gwamnatin Buhari.

Kungiyar ta kunshi tsofaffin gwamnoni da manyan ‘yan majalisa wadanda suka daura damarar yaki da gwamnatin Buhari.

Daga cikin ‘yan sabuwar jam’iyyar PDP din akwai Mista Saraki da tsohon gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako, da sanata, Dino Melaye, wanda ke fuskantar tuhuma kan cin hanci da rashawa.

Wasu da yawa daga cikin manyar jam’iyyar  sun koka kan yadda aka yi watsi da su a loacin da aka gudanar da zaben kasa na jam’iyyar a cikin watan Mayu da Yuni na wannan shekarar.

Tun lokacin da wannan gwamnati ta hau ta fara saka da mugun zare, ganin haka aka fara samun tunanin kafa sabuwar jam’iyyar PDP.

A wata sabuwa kuma sabon shugaban jam’iyyar APC, Adams Aliu Oshiomhole ya yi alkawarin tattaunawa da ‘yan sabuwar jam’iyyar PDP domin kokarin daidaitawa a tsakani.

Oshiomhole ya bayyana cewa, shi ba shi da ra’ayin cewa, duk wanda ke da shirin fita daga jam’iyyar ga hanya nan, saboda haka ya ce zai ci gaba da lalubo bakin zaren warware wannan matsala. Ya bayyana hakan ne lokacin da ya kai wa shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki  da wasu manyan jam’iyyar APC ziyara.

Haka kuma ya ja kunnen shugabannin jam’iyyar na kasa da su guji yin katsalanda a cikin al’amuran jihohi, wanda ke daga cikin abin da ke haifar da rashin fahimta a jam’iyyar.

Saboda haka ya ce shugabanci jam’iyyar na kasa zai ba kowa matsayinsa yadda za a hada kai a taimaka wajen samun ci gaban jam’iyyar a kowane mataki.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!