Dansanda Ya Yi Ajalin ‘Yar Bautar Kasa Ana Gobe Za A YaYe Ta — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Dansanda Ya Yi Ajalin ‘Yar Bautar Kasa Ana Gobe Za A YaYe Ta

Published

on


Ana zargin wani dansanda da kashe wata mai yiwa kasa hidima mai suna  Linda Angela Igwetu wadda kuma take cikin sahun takwarorin ta da aka  yaye jijya alhamis à Abuja.

Kisan  natar ya janyo cece kuce à kafafen sada zumunta,musamman yadda iyayen ta suka bayyana sai an bi wa yar tasu hakkin ta.

‘Yar yiwa Katar hidima a garin Abuja ne ake zargin dan sandan ya hallaka ta, Linda Angela Igwetu, tana daya daga cikin takwarorin ta da aka tsara za a tâte à ranar 5ga watan Yulin 2018 a  Abuja.

Lamarin mutuwar Linda dai an an yada ne ta Twitter mai adiredhi @Chiskyyy  a ranar 4 ga watan Yulin 2018.

Mariganyiyar ta yi aikin ta na yiwa kasa hidima ne a wani jamfani mai suna Global Company dake yankin Mabushi kuma an ce yarinyar ta ne yawo ne da kawayen ta duk a cikin murnar shagalin kammala hidimar tira kasa hidima.

Da yake bayyana yadda lamarin ya auku daya daga cikin abokan yarinyar yar shrara 23 da uku mista Segun Awosanya yace ta tashi daga gun aiki a makare a ranar talata da misalin karfe 11 na dare taje ta samu takwarorin ta a inda suke gudanar da de shagul gulan su na murnar kammala yiwa kasa hidima kafin yaye su washe garin alhamis a Abuja.

Ya ce, sun bar gida da misalin karfe uku na daren ranar laraba,inda dan sanda mai suna Benjamin Peter ya harbe ta a shigen da ake dakatar da ababen hawa daura da Ceddi Plaza.

Acewar sa  harsashin ya same ta a kwuibinta inda juni ya yi ta zuba aka garzaya da ita asibin Garki a cikin wata budaddiyar mota Jini nata zuba, kuma mahukuntan asibitin suka ki karbar ta a bisa hujjar ba a kawo rahoton yan sanda ba, hakan ya janyo mutuwar ta an kuma dauki gawar ta an kai ofishin yan sanda dake Sakatariyar Abuja.

A cewarsa a yanzu haka muna jiran rahoton da yan sanda zasu fitar kuma mun rubuta takardar koke mun kai shalkwatar yan sandat ta kasa kuma zamu gabatar da maganar a gabam kotu.

Yaci gaba da cewa, yan sandan sunce sun ga mota mai tsada tá wuce ta wajen shingen kuma basu san ko su waye a ciki ba saí kuma dan sandan yaji ana ihun neman a kawo dauki a cikin motar, inda hakan ya sanya ya bude wuta.

Acewar sa tambaya ta anan Ítaca, “don kawai ka ji ihu a cikin mota na neman taimako kawai sai ka bude wuta? Mai makon ka tsayar da motar don chaje ta, wannan maganar karya ce suna kawai son fakewa ne akan shedancin da suka tabka.

Mai magana da yawun yan sanda  DSP Anjuguri Manzah, ya shedawa jaridar The Nation ta hanyar wayar tafi da gidan ka cewar an fara binciken maranata.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!