Hukumar Alhazai Ta Fara Horar Da Jami’anta A Bauchi — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RAHOTANNI

Hukumar Alhazai Ta Fara Horar Da Jami’anta A Bauchi

Published

on


Hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Bauchi ta fara bayar da wani horo na musamman ga malaman bita kan aikin hajji, jami’an hukumar na kananan hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki kan aikin hajji, wadanda za su jagoranci ilmantar da maniyyata aikin hajjin bana.
An fara horaswar ne a jiya Juma’ar, inda za a koyar da su yadda za su koyar da kuma yadda za su ilmantar da maniyyata aikin hajjin a dukkanin yankunansu domin samun nasarar gudanar da aikin hajji karbabbiya.
Da yake jawabi a wajen bude bitar, shugaban hukumar jin dadin Alhazai wanda kuma shine Galadiman Bauchi, wanda ya samu wakilcin Limamin Massalacin Gwallaga Imam Ibrahim Idris ya bayyana cewar horaswar tana dana da gagarumar fa’ida domin ilimantar da wadanda za su yi aikin koyar da Alhazai yadda ake gudanar da aikin domin kauce wa shigo da wasu ababen da basu cikin ka’idar gudanar da aikin.
Galadiman Bauchi ya bayyana cewar dukkanin matakan da suka dace su ne hukumar ke bi a kowace shekara domin aiwatar da aikin yadda ya kamata, ya bayyana cewar wanna bitar wani rukuni ne daga cikin aikace-aikacen da hukumar take gudanarwa a duk shekara domin kyautata aikin hajji.
Yana mai kiran wadanda za a basu horon su sanya lura gaya wajen riskar dukkanin ilmomin da ake da niyyar shigar musu domin su samu damar yadawa ga maniyyatan da za su sauke farali a bana.
Da yake tasa jawabin, Kwamishinan ma’aikatar harkokin addinai na jihar Bauchi, Alhaji Ado Sarkin Aska Zigau ya bayyana cewar gwamnatin jihar ta yi cikakken tsari wajen tabbatar da cewar maniyyatan jihar sun samu walwala da kuma jin dadi hadi da samun nasarar gudanar da aikin yadda yake.
Ya ce, gwamnatin jihar hakki ne a kanta ta sanya ido da lura wajen tabbatar da cewar an samar da kariya ga alhazai a dukkanin hidimar aikin tun daga lokacin da suke samun bita, jigilarsu zuwa kasa mai tsarki har ma a kasa mai tsarkin, ya kuma bayyana cewar gwamnatin jihar ta yi tsari na musamman domin ci gaba da dafa wa alhazanta domin kyautata musu Ibadarsu.
Ya hori masu samun horon su sanya hankula domin gane dukkanin ilimin da ake son su samu, ya kuma bayyana cewar hakki ne a kansu su sauke nauyin da aka daura musu na fadakarwa domin samun lada daga Allah madaukakin Sarki.
Daga bisani ne kuma ya bude wannan gagarumin taron bitar.
Da yake tsokaci babban mai tallafa wa gwamnan jihar Bauchi kan aikin hajji, Mal. Tukur Mu’azu ya bayyana cewar aikin hajji daya ne daga cikin rukunai wajiba ga dukkanin baligi mai halin zuwa, don haka ne ya bayyana cewar gwamnatin jihar take dafa da dukkanin karfinta ga wanda ya samu ikon zuwa aikin hajjin.
Ya ce, dukkanin wani jami’in da ya koyar da aikin hajji tsakaninsa da Allah yana da gagarumar lada a wajen Allah madaukaki, don haka ne ya horesu su yi aiki tsakaninsu da Allah.
Wasu daga cikin malaman da suke amsar horon da muka zanta da su, sun bayyana cewar suna samun karin ilimi gaya ba ma kawai don su samu fadakar da alhazai ba, har ma da su kansu suna amfana da ilimin da suke samu, suna masu shaida cewar sun saba tattaunawa duk shekara kan yadda ake tafiyar da aikin hajji a shari’ance domin kauce wa shigo da ababen da babu su a ka’idar aikin.
Taron bitar dai wacce take gudanuwa a cikin dakin taro na babban massalacin Bauchi, inda aka hada malamai, jami’ai hukumar alhazai na kananan hukumomi 20 na jihar Bauchi, malaman da suke jagorantar bita ga alhazai a cibiyoyin bayar da bita ga alhazai a fadin jihar Bauchi, za su shafe kwanaki uku suna amsar wannan horon kamar yadda aka saba duk shekara.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!