Mata Masu Zanga-Zanga Sun Rufe Babbar Hanyar Gwambe Zuwa Yola — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RAHOTANNI

Mata Masu Zanga-Zanga Sun Rufe Babbar Hanyar Gwambe Zuwa Yola

Published

on


A Jiya Juma’a ne Matan karamar hukumar Billiri da ke yankin Gwambe suka rufe babban hanyar Gwambe zuwa Yola a lokacin da suke gudanar da zanga-zangar kin amince da kisan da suke zargin mutanen karamar hukumar Shongom suka yi wa wani matashin garin.
Mazauna garin Billiri sun shaida wa wakilinmu ta wayar tarho inda suke bayyana cewar mata masu zanga-zangar sun rufe babban hanyar ne tun waja-jen karfe 10 na safiya, lamarin da ya janyo cink-oson fashinjoji masu son tafiya zuwa Adamawa, Taraba da jihar Benue.
Masu zanga-zangar sun kuma bayyana bukatar a sake musu matasa 20 da sojoji suka kame a loka-cin da suke kan aikin daidaito da zaman lafiya a yankin.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Gwambe, Mista Tairu Shina Olukolu, ya tabbatar da lamarin ga manema labarai.
Mista Shira Olukolu ya shaida cewar lamarin mutu-war matashin ya faru ne a kauyen Rufai da ke kara-mar hukumar Billiri a sakamakon wani fadar da ya barke a tsakanin al’umman Billiri da Shongom.
Ya ce, lamarin ya fara faru ne tun a daren ranar Alhamis inda daga bisani matan suka tashi da zanga-zanga a ran-ar Juma’a.
Ya ce, rundunarsu tana kan yin duk mai iyuwa wajen daidaita matsalar a wannan yankin da lamarin ke faru a Billiri.
Wakilinmu ya shaida mana cewar wannan al’amarin ya yi matukar haifar da cinkoson motoci a wannan babban hanyar. Har zuwa yammacin jiyan dai matan basu bude wannan babban hanyar ba.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!