Shugaba Buhari Ya Kaddamar Da Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RAHOTANNI

Shugaba Buhari Ya Kaddamar Da Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa

Published

on


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da cewar, a bisa gwamnatin tarayya a bisa kudurinta na yaki da cin hanci da rashawa zata tabbatar da cewar ba ‘a ci galaba akan tab a wajen cin nasara yaki da cin hanci da rashawar ba.
Buhari ya sanar da hakan ne a fadar shugaban kasa a lokacin da yake sanya hannu akan dokar cin hanci da rashawa da sauran laifuffuka mai lamba 6 ta shekakar 2018, inda ya kara da cewar, don tsamo da kasar nan daga matsanciyar siyasa da tattalin arzikin kasa daga matsalar cin hanci da rasawa dole ne dukkan masu ruwa da tsaki da sauran yan Najirea su tabbatar da sun kiyaye yiwa dokar hawan kawara.
Ya shawarci hukumomin gwamnati ta hanyar yin tuntuba da Atoni Janar na kasa don suma subi sahun aiwatar da ayyukan sun a gwamnati ba tare da yin wata almundaha ba, inda ya kara da cewar, yaki da cin hanci da rashawa abune da kowa ya kamata ya sa hannu a ciki don kawo karshen sa a kasar.
Acewar sa, bayanai sun nuna cewar, kudaden da ake kashewa a hukuncin da ake yin a cin hanci da rashawa sun kai yawan naira biliyan 595.4.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!