‘Yan Kasuwar Azare Sun Samu Tallafin Miliyan 100 Tun Bayan Gobara — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RAHOTANNI

‘Yan Kasuwar Azare Sun Samu Tallafin Miliyan 100 Tun Bayan Gobara

Published

on


Ya zuwa yanzu an samu kimanin Naira miliyan 100 na kudaden tallafi da ake bayarwa domin agaza wa wadanda ibtila’in gobara ta shafa a babbar kasuwar Azare da ke jihar Bauchi, baya ga kudaden, an kuma samu tallafin wasu muhimman kayyakin abinci a matsayin kayyakin tallafi.
An samu wannan adadin kudin ne a sakamakon samun gagarumin tallafin Naira miliyan 50 da kamfanin matatar mai ta kasar Nijeriya NNPC ta hanun Maikanti Baru ta bayar wa ‘yan kasuwan da lamarin ya shafa, tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar wanda ya basu tallafin miliyan 10, gwamnan jihar Gombe, Alhaji Dankwambo Naira miliyan 10, da sauran fannonin da suka samu bayar da tallafin da adadin ya kai miliyan 100.
Mai Martaba Sarkin Katagum Alhaji Umar Faruk II shi ne ya bayyana hakan a lokacin da ya marabci bakwancin mambobin kwamitin dattawa masu bayar da shawara na jihar Bauchi a fadarsa da ke garin Azare.
Sarkin ya bayyana cewa bayan tsurarin kudaden da aka samu; an kuma samu tallafin kayyakin abinci a matsayin gudunmawar rage radadi wa ‘yan kasuwan da suka hada da; buhun shinkafa dubu 3, buhun masara dubu 3, da galan-ganal na manja da mangyada, taliyar sufageti da yawa domin tallafa musu dan rage musu radadin asarar da suka yi; ya shaida cewar tunin kuma aka fara raba musu wadanan kayyakin abincin da aka samu daga masu tallafawan.
Mai Martaba Sarkin Katagum Alhaji Umar Faruk ya kuma shawarci kwamitin da gwamnan jihar Bauchi ya kafa domin bashi shawarori domin samun nasarar tafiyar da aiyukan gwamnati daidai da suke tabbatar da cewar dukkanin shawarwarin da suke bai wa gwamnan mai amfani ce, hade da tabbatar da cewar gwamnan yana amfani da shawarorin domin amfanar al’umman jihar.
Har-ila-yau, Sarkin ya jawo hankalin kwamitin dangane da matsalar shaye-shaye da ta-ki-ci-ta-ki-cinyewa, inda ya nemi su maida hankali hade da jawo hankalin gwamnatin jihar don yin mai iyuwa kan lamarin.
Tun da fari a jawabinsa shugaban kwamitin Dattabai da suke bayar da shawara wa gwamnan jihar Bauchi, Ambasada Jibrin Dada Cinede ya ce sun kasance a fadar ne domin jajanta wa masarautar biyo bayan ibtila’in da ta auku a garin na Gobarar da ya kai ga cinye kasuwar garin karan kaf.
Ya ce, sun kuma yi amfani da damar wajen sanar da sarkin wannan kwamiti nasu da gwamnan ya kafa da irin aikace-aikacen da ke kansu “shi dai gwamna yana son mu taimake shi wajen tafiyar da gwamnatinsa ta zama mai adalci, ta zama mai gaskiya, ta zama mai kula da mutanen da suka zabe shi. Wannan babbar nauyi ne a gare mu, amma ba namu ne na kadai ba, nauyi ne na jihar gaba daya,” In ji shi.
Cinade ya shaida wa Sarkin Katagum kan cewar gwamnatin jihar ta daura musu alhakin lura da yadda jama’an jihar za su ci gajiyar gwamnatin, sai ya bukaci Sarkin da ya kasance daya daga cikin wadanda za su ke shawartar kwamitin domin gudanar da ababen da suka dace don kyautata rayuwar ‘yan jihar.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!