Connect with us

SIYASA

An Nemi Gawuna Da Ya Yi Takarar Majalisa A Kano Ta Tsakiya

Published

on

Al’umma da dama daga mazabar majalisar dattijai ta Kano ta tsakiya sun nuna goyon bayansu ga fitowar kwamishinan ma’aikatar gona na jihar Kano, Alhaji Dakta Nasir Yusuf Gawuna, sun nuna cewa, shi ya fi cancanta da al’ummar Kano ta tsakiya su mara wa baya dan zama wakilin mazabar a majalisar dattawa ta kasa a zabe mai zuwa da za a gudanar a kasarnan.
Daya daga cikin jama’ar da suke wannan kiran shi ne, manajan darakkta na hukumar “KNARDA”, Farfesa Mahmoud Daneji, kuma daya daga cikin na gaba-gaba da suke fafutukar kiran kwamishinan ya tsaya takarar kujerar majalisar dattawan na kano ta tsakiya a hirar da ya yi da ‘ya jarida.
Ya yi nuni da cewa, tsarin dimokradiyya ta kunshi bangarorin zartarwa da majalisa dana bangaren shari’a kuma sanata bangare ne na majalisa wacce ita take dokoki da tabbatar dasu idan aka kawo da bibiyar ayyuka da ake aiwatarwa a hukumomi da cibiyoyin gwamnatin tarayya.
Dan haka bisa la’akari da cewa wannan bangare yana bukatar jajirtaccen mutum kuma sun san irin jajircewar da Gawuna yake dashi a kan duk abin da yasa a gaba in dai na kawo ci gaba ga al’ummane suke da yakinin inya sami zuwa wannan majalisa ta dattawa bazai zama dan dumama kujera ba, saboda mutum ne mai iya magana a kan karumma da kwarjini duk inda ya sami kansa.
Farfesa Mahmoud Daneji ya ce, Nasiru Gawuna duk abin da ya shafi kawo ci gaba ga Kano ta tsakiya dama jihar baki daya zai jajirce a tabbatar da shi, zai karbi korafi daga jama’a bazai gujesu ba, baya rufe wayarsa duk lokacin da ka kira shi yana amsawa ko bai gani ba daga baya idan ya gani zai kirawoka.
Daneji ya ce, dama Dakta Nasir Yusuf Gawuna dan siyasa ne daga tushe wanda ya yi shugaban karamar hukumar Nasarawa har na shekara takwas dan haka zai dauki bukatun al’umma tun daga kasa zuwa sama.
Farfsa Daneji Gawuna ya ce, shi ne a wannan matsayi na sanatan Kano ta tsakiya zai jajirce a kan kyautata abin da ya shafi jin dadin jama’a na yau da kullum kamar harkar ilimi da nomad a kuma samar da ruwansha da inganta lafiya ta irin ayyukan mazabu da ake basu.
Ya kara da cewa, zai kuma samar da aiki ga matasa a fannoni daban-daban ta la’akari da yadda ake da dinbin matasa a Kano ta tsakiya da basu da ayyukan yi, zai yi kokari wajen samar musu da dama ta dogaro da kai.
Shugaban na hukumar ‘KHARDA’ Farfesa Mahmoud Daneji ya kara bayyana cewa, takarar Nasiru Yusuf Gawuna bata bukatar tallatawa ga al’umma saboda sun san wanene shi wajen kyautatawa kusan duk yan takara da suke neman wannan kujera babu kamarsa dan siyasane mai mu’amala da jama’a komai baya rufe waya daka kirashi zai dauka kullum kuma cikin jama’a yake gidansa da ofishinsa.
Daneji ya yi kira ga al’ummar Kano ta tsakiya su bai wa Gawuna dama cikin yardar Allah za a sami biyan bukata da aka rasa a wakilcin da wasu suka yi musu a baya na majalisar Dattawa da basu sami kulawa ba. Ana da bukatar irinsu Gawuna a kunshin ‘yan majalisar dattawan kasar nan guda 109 domin yin kokarin ya kawo wa yankinsa ci gaba duk abinda za a yi zai tsaya a kai kyam dan kai wa ga nasara da ci gaban al’ummarsa ta Kano ta tsakiya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!