Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Fyade: Kotu Ta Yanke Wa Dan Shekara 48 Zaman Gidan Yari Na Shekaru 60

Published

on

Kotun dake hukunta cin zarafin da aka yi a gida ko yin lalata dake yankin Ikeja cikin jahar Legas ta tankewa wani dan shekara 48 mai suna Adelaja Olaide hukuncin zaman idan Yari na tsawon shekaru 60 saboda yiwa wata yar shekara takwas dake aji biyu a makarantar firamare fyade.
Mai shari a Sybil Nwaka, ta dangan ta mutumin a matsayin dabba, Olaide wanda direba ne yana da zama ne a gida mai lamba 17 dake kan titin Itun Oluwo Ketu yankin Ejirin a cikin jahar an yanke masa hukuncin ne akan tuhuma biyu ta huda yarinyar, inda hakan ta sabawa doka ta ranar 27 ga watan Yunin 2015 an kuma yanke masa hukuncin ne sakamakon rahoton duba lafiyar yarinyar da aka yi a asibiti.
A saboda hakan, “na yanke masa hukuncin zaman gidan Yari na shekaru 60 kuma ba tare da wani zabi ko biyan tara ba dan sanda mai gabar da kara Mista Babajide Boye ya shedawa kotun cewar ya aikata lafin ne ta hanyar yaudarar ta da alewa ya kaita gidan sa dake makwabtaka da gidan su yarinyar ya yi mata fyaden.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!