Mamonan Tumatur Sun Yi Kira Ga Gwamnatin Jihar Kano — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASUWANCI

Mamonan Tumatur Sun Yi Kira Ga Gwamnatin Jihar Kano

Published

on


Wani shaharraren manomin tumatur a jihar Kano, mai suna Sani Dalladi Yadakwari sannan kuma shugaban kungiyar masu noma tumatir da sayar da shi tare da sarrafa shi na jihar Kano, bayan haka kuma sakataren kungiyar na kasa .
Ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zanatawa da manema labarai kwanakin baya a ofishin kungiyar dake Kano ciki har da jaridar Leadarship A Yau. Sani Dalladi Yadakwari ya ce, babban tallafin da suke bukata daga gwamnatin jihar Kano a karkashin Abdullahi Umura Ganduje shi ne kayayyakin aikin gona ga masu noma tumatir dake jihar ta Kano. da kuma iri da magungunan feshi masu inganci da sauransu.
Shugaban kungiyar na jihar Kano, babbar matsallin dake addabar daukacin manomin tumatir rashin samun kasuwa da sauransu saboda haka ita gwamanati tana da rawar da za ta taka wajen nemo masu kasuwa daga ciki da wajen kasar nan. A bin farin ciki yanzu ana kara samun masu noman tumatir a jihar Kano dama kasa baki daya idan ka kwatanta da shekarun baya .
Sai dai ya koka game da yadda ake shigo da tumatirin gwangwani daga kasar waje bayan ga shi ana noma tumatir tare da tare da kamfanonin dake suke sarrafa shi, ya ba da misali ga kamafanin sarrrafa tumatir na kamfanin Dangote dake Kano, ya kamata al’umma su zama suna kishin kayayyakin da ake sarrafawa a kasar nan.
Sakataren manoman tumatir din na asa ya yi wa manoman jihar Kano da na kasa baki daya cewa su kara himma akan noma tumatir a wannan shekara domin alamu sun nuna masu noman tumatir za su samu kasuwa mai kyau. Saboda haka shirye shirye sun yi nisa wajen bai wa masu noman tumatir rance.
Ya kuma gode wa gwamnan jihar Kano game da cika masu alkawarin da ya yi masu sakamakon asaran da masu noman tumatir suka tafka a shekarun baya musamman wadanda suka bi ta hanyar kungiya. Yadakwari ya ce, makasudin kafa kungiyar shi ne yadda masu noman tumatir ke tafka asara wasu lokuta shi ne suka ga ya kamata su kafa kungiya domin magana da murya daya da kuma kai kayan da suka noma kamfanonin sarrafa tumatir.
Daga karshe ya yi addu’ar Allah ya bai wa kasar nan damuna mai albarka wadanda suka gamu da asara rayuka da dukiyoyi sakamakon ruwa ko iska a wasu jihohin arewacin kasar nan Allah ya mayar masu da alhairi wandanda suka rasu kuma Allah ya jikansu

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!